🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
*MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*بسم الله الرحمن الرحيم
9⃣4⃣
Ƙarfe takwas daidai ta gama dukkanin ayyukan ta na gida ta shirya shi tsaf cikin ƙananan kayan kaya riga da wando baƙaƙe gashin fuskar shi ta yi shaving ɗinshi harta da gashin kan saidata rage shi ta gyare mashi,itama sanye take cikin doguwar riga turkish baƙa mai top yellow da igiya a daidai west ɗin tayi rolling gyalen akanta sannan ta yafa babban mayafi a kafaɗar ta tariƙeshi da pin sunyi matuƙar kyau suka sanya shi cikin mota tareda ɗan bayero suka fice daga gidan,
Ƙarfe tara daidai suka isa kai tsaye dakin doctor suka nufa inda yake jiran su,fitowa tayi tabarshi a office ɗin,Fita tayi ta samo ɗanbayaero dake jiranta a motar ta shiga yaja suka tafi,shagon data saba zuwa nan taje ta saida sarƙanta set babban,ta fito suka nufi gym center ɗinsa ɗinshi,ita ƙadai ta shiga ciki kai tsaye sama ta wuce wurin manager shi sun ɗan jima suna magana kafin ya bata keys ɗin office ɗin amjad ta shiga ta soma gyareshi duk da babu wani datti a ciki koina ta gyare har toilet ɗin ta fito ta kulle kofar,
Saida ta maida kets ɗin wurin maganer suka sake ɗan tattaunawa kafin ta fito ta shiga motar suka koma asibiti,koda ta shiga cikin duk saurin datake saita tarar har lokacin basu gama dubashi,saida tayi zaman mintuna goma sha biyar kafin suka fito dashi daga wani ɗakin,ajiyar zuciya ta sauke da karfi a bayyane don ganin ƙafar babu naɗi komai ajiki da alamu gyara ya warke ƙarasawa tayi wurin su tana sakar mashi lallausan murmushi shima yana mayar mata da martani office ɗin doctor suka nufa inda ya yi musu bayanin nasarar da aka samu na gyaran karayar saidai bayn nashi nedai sai hakuri wannan,
tana kallon sanda ya sadda kanshi ƙasa cikin rintse idanu da karfi har jijiyoyin gefen kansa suna tashi da sauri ta sanya hannunta ta ruko hannun shi tana matsawa da ɗan karfi ɗgowa yayi yana dubanta idanun shi har sunyi jajur kamar garwashi girgiza mashi kai tayi cikin dauriya don ita ɗin kiris take jiran ta soma kukan amma ta danme domin samun kwantar mashi da hankali,
Kai ya ɗaga mata yana sakar mata murmushi wanda ta san na ƙarfin haline kawai da jarumta,murmushin itama ta ƙakalo tana lumshe masa manyan idanun ta alamun jin daɗi da godiya,Sun jima a office ɗin doctor yana basu shawarwari akan yadda za'a lura dashi gaba ɗaya zahra ta maida hankali ga sauraron likitan domin tasan zaiyi mata amfani dukkanin bayanin nashi,
yayinda shi kuma Amjad zuciyar shi ta lula dashi chan tunanin rayuwa da lokacin da za'ace duk zasu rabu dashi yasan pretty zata iya zama dashi aduk halin dayake ciki saidai tabbas zaman nasu zai kasance gwara babu dashi tunda ada ma baitaba sanin daraja da daɗin aure ba saida zahra ta shigo rayuwar shi,,tabbas Zahra ƴar halak ce ta nuna mashi itaɗin cikakkiyar mai tarbiyya ce,ya dade yana kwatanta da abunda zai fassara hakurinta amma ya gaza, tabbas yaso ace yana da lafiya,yaso ace ya samu ya faranta mata koda kaɗanne saidai bayajin zai iya barin zuciyar shi tayi nasarar hakan,
dole yayi abunda zai sanyata fita daga rayuwar,domin bayason ya ƙarya alƙawarin dayayi wa pretty zai yi kokarin rabuwa da ita har abada ya cigaba da zama da pretty ɗinshi da abunda yazata haifa aduk irin munin halinta wanda dama ya riga ya saba,Ajiyar zuciya ya sauke a boye ya ɗago idanun shi yana kallon zahra dake riƙe da hannunshi tamkar wacce za'a rabata dashi,ya rasa dalilin daya sanyata shigowa cikin rayuwar shi,tunda yasan ba son shi takeyi ba idan har domin ta nuna mashi ita ɗin mai tarbiyyace tabbas zai rabu da ita don kuwa tariga ta dade da nuna mashi itaɗin tata tarbiyyar daban ce data sauran mutanen dayake mu'amala dasu,matsalar itace zuciyar!,zuciyar shi takamu da ciwon sonta mai tsanani da matuƙar ƙarfi wanda yake ganin tabbas zan iya shiga wani mugun hali idan har ya rabu da ita,
taya zai iya yaƙi da zuciyar shi akan hakan taya zai iya fiddata cikin rayuwar batareda ya bata ranta ba,wanna shine abunda yake damunshi akoyaushe wanda ya gaza samun mafita,
abu ɗaya yasani shine yadda zuciyar shi bata iya hakurin jure rashin ta na tsahon awanni ma balle rabuwa ta har abada,
hawayen dayake rikewa suka zuba mashi tabbas adalci ɗaya zai yiwa Zahra shine na sawwake mata auren shi koda zai kamu da ciwon zuciya ne,wanna ne kawai zai sanya ya wanke dukkanin laifin dayayi mata abaya,,
YOU ARE READING
ZAN RAYU DA KAI
RomanceLabari akan tsantsar soyayya ga Wanda baisan tanayi ba saima niyyar mummuna daya kudira akan ta ,amma hakuri da ladabi hade da karfin soyayya datake masa tun tana karama ya juyar da akalar kudiransa mummuna zuwa ga na alkhairi