🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
*MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*بسم الله الرحمن الرحيم
9⃣3⃣
gaban mudubi ta kaishi ta soma shafa mashi mai ajiki a kunyace tana kauda kai jikinta har yana ɗan rawa yadda takejin tsikar jikinta na tashi bataji hakan bama wurin wanka ko don lokaci hankalin ta a tashe yakene,kaya ta ɗauko marasa nauyi riga marar hannu mai kyau tareda wando three quater sky blue masu matuƙar kyau da boxes da singlet suma kala ɗaya ta sanya mashi idanu ta a rufe har ta gama ta dauko turare ta feshe a jikinshi,duk abunda takeyi yana binta da kallo ne kawai yadda take komai akunyace ya sanyashi shagala sosai da kallon ta musamman inta rufe idanu ita dole bataganin shi hakan ya na sanyashi dariya amma sai ya gimtse yaƙeyin saidai a zuciya don kar ta fahimci kallon ta yakeyi,
Fita tayi ta dauko abunda ta haɗa mashi na karyawa ta soma bashi a baki cikin nutsuwa yana amsa har lokacin ya kasa ɗauke idanun shi a kanta wanda ya rasa dalilin daya tsinci zuciyar shi da son hakan ya kasa gajiya da daina kallon ta duk wani motsi nata burge shi takeyi yadda take komai cikin nutsuwa da kunya wanda ya lura kallon dayake matan tana jin shi ajikinta takan sake takura da sanya haɗe da kunya a duk lokacin da sukayi ido biyu,
Maganin sa ta dauko wanda ko kwance ledar ba'ayi ba tun dawowar su asibiti ta duba kowanne ta bashi ya sha,sa'annan tatura kujerar zuwa parlon ta koma ɗakin ta gyare tass da bed ɗin ta shimfaɗa wani bedsheet ɗin akai ta feshe ɗakin da turaruka masu sanyin kamshi,saida ta duba komai yayi sanna ta koma parlon ta turo shi zuwa ciki har wurin gado ta soma koƙarin dora shi akai,
ba ƙaramar wuya taci ba kafin ta iya dora shi gadon da kƴar gabaɗaya duk tayi gumi yana kallon ta cike da wani irin tausayi da ƙaunar ta mai girma dayake jin tana ƙaruwa cikin zuciyar shi,ta daɗe zaune kafin ta iya yunkurawa ta tashi saboda yadda bayanta da kwankwanson ta ya riƙe mata,tana miƙewa taji marar ta tayi mata nauyi sosai tamkar an cure mata wani irin dutse a wurin,Rintse idanu tayi cikin jin zafi tana cije lips ɗinta tana yamutsa fuska cikin jin zafi kusan seconds biyar kafin ta buɗe su akanshi shima ɗin ita yake kallon saurin sakar mashi murmushi tayi ganin yadda kwalla ta soma taruwa a idanun shi,
da sauri ta wuce wurin ƙaton window dake chan gefe ta yaye labulayyar dake wurin ta saƙale su gefe da gefe ta bude windows ɗin nan take iskar mai daɗi ta soma ƙadawa tana shigowa sauke ajiyar zuciya sukayi dukkansu,tayi matukar mamakin ganin ƙasan wurin yadda yake tamkar wurin shaƙatawa ƙaton swiming pool ne wanda aka zagaye da wasu irin manya da ƙannan lantern na wuta masu kyau ga flowers kaloli daban daban a wurin harda ɗan wani wuri da aka kebe tamkar wurin var shima an ƙawatashi sosai,ga abubuwan wasa nan na manya dana yara kowanne an ajiye shi a inda ya dace da tsarin kwalliyar sa,ba ƙaramin burgeta wajen yayi ba, ajiyar zuciya ta sake yi tana tunanin wani abu kafin ta juyo har lokacin ita yake kallo hawayen yana zubowa daga idanun shi,da sauri ta ƙarasa wurin shi ta riƙo hannunshi tana girgiza mashi kanta a hankali alamun ya daina kukan,lumshe idanun shi yayi yana jin tsananin kunyar ta da abubuwan daya aikata mata wanda yakasa gane kuskuren shi tun farko ya gyara saida lokaci ya kure mashi,
Miƙewa tayi ta ɗauko alqur'an ɗinshi dake ajiye ta dawo ta zauna akan bedside drower ta bude tun daga farkon suratul fatiha ta soma karanta mashi cikin sanyayar daddaɗar muryar ta,ƙasa buɗe idanun shi yayi koda yaji tana karatun saidai ajiyar zuciya daya sake a sihirce muryarta na ratsa kunnuwanshi da jinin jikin shi,yana jin yadda nauyin dake kirjinshi yake raguwa zuciyar shi na sanyaya tun yana sauraron ta har wani dadaɗan bacci ya ɗauke shi wanda rabon shi dayin haka tun ranar daya baro asibiti,
ta jima tana karatun kafin ta miƙe ta rufe mashi bargo tayi tsaye tana kallon shi hawaye na bin fuskar ta tsananin tausayi da wutar soyayyar sa na ƙara ruruwa cikin zuciyar ta"Allah yabaka lafiya mijina"ta faɗa a hankali ta soma bin kowacce gaɓa ta jikin shi tana tofewa da adduoe tun daga kan shi har zuwa tafin ƙafarshi.
YOU ARE READING
ZAN RAYU DA KAI
RomanceLabari akan tsantsar soyayya ga Wanda baisan tanayi ba saima niyyar mummuna daya kudira akan ta ,amma hakuri da ladabi hade da karfin soyayya datake masa tun tana karama ya juyar da akalar kudiransa mummuna zuwa ga na alkhairi