Zan Rayu Da Kai

1K 66 1
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          
loadιng...........✍🏻

                 
        🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
                      

Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
      *MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*

بسم الله الرحمن الرحيم

*fatan alkhairi da kyakyawar addua zuwa gare Ku kuma masoya ina jin dadin adduoe inku ,Allah ya bar kaunar ,one luv🥰*🤝🏻


1⃣7⃣➕1⃣8⃣

Basu bi layi ba wurin shiga saboda Ade sairayin hassana suke duba tickets saboda shima yana dan taba harkar music din saidai duk yadda suka so set din farko basu samu ba saina biyu,,haka suka amshi number s din sit duinsu suka wuce ciki,,

Sosai jikin Zahra ya kara mutuwa tareda yin sanyi matukar irin yadda taga wurin ya cika da wayayyun yan mata kowacce ta kure adaka cikin kannan kaya kusan abunda idanunwanta suke hango mata wurin gabadaya itace bata sanya kananan kaya ba ko masu doguwar riga duka english wears ne,,miyau ta hadiye da kyar zuciyar ta na tsananta bugawa anya kuwa sakonta zai ida isa gareshi kuwa batajin idanunwansa zasuyi sha'awar kallonta,,

Ga wani matsanan cin kishi daya taso ya kullube kokon zuciyarta yadda kowacce ke rawar kai akan son haduwa dashi sai abun yake dukan zuciyarta duk inda suka wuce hirar dayace ta prince Amjad din,,

haka suka karasa suka zauna yar karamar Jakarta ta balle tadauko chewing gum ta worga bakinta kota samu dan kwarin gwiwa,,

Inna lillahi taji yarinyar dake gabanta tana ambata da karfi tana kallonta dago da oily eyes dinta tayi tana dubanta itama hankalinta a dan tashe jin sallatin bana lafiya vane ganin tana kallonta yasanya ta sake kallon jikinta ko wani abunne ya faru bataga wani Abu ba na daga hankali ba dagowa tasakeyi ta kalli yarinyar saitaga wayam babu ita ta waiga hagu da dama bata ganta ba,,

Hmmm ajiyar zuciya ta sauke da karfin tana cire chewing gum din daga bakinta ta jefar tasan shigarta yarinyar nan keyiwa haka,,
Hade bakinta tayi wuri daya idanuwanta na Tara kwalla tace itama kenan Valle shi namiji haihuwar turai dukar da kanta kasa tayi saboda hawayen daya fara zumo mata da sauri ta sanya hannu ta dauke Wanda yayi dai dai da daukewar wutar hall din mai gabatarwa ya fara aikinsa cikeda kwarewa,,

Bayyanarsa ya kasancewa tamkar dauke wutar zuciyarta yayinda salon bugun zuciyarta ya tsanan ta mata cikin salon sauri sauri hakan ya taimaka wa numfashinta  fita da kyar yadda zuciyarta ke aiki tamkar zata faso kirjinta,,

A hanzarce ta sanya duka hannayenta ta danne kirjin nata don batajin akwai abunda zai hana zuciyarta faso wa ba,,
A hankali ta sake dago idanun takalleshi a karo na biyu bakinta dauke da addua har lokacin hannayenta na bisa kirjinta,,

A hanzarce tayi gaggawar dauke idanunta Wanda sukayi ido hudu dashi shima itadin yake kallon,,

Mamaki shigar da tayi yake yi saanan mafi abunda yafi bashi mamaki shine irin yadda ta kame kanta Sam bata nuna murna ko ihu ko jin dadin ganin sa ba kamar yadda gabadaya wurin yanmata da samari suka mike don bayyanar sa,,

Hakance ta kasance a gareta Bayan da sansanyar dandaddar muryar sa ta daki zuciyarta da kunnuwanta nan take tsikar jikinta ta tashi lumshe idanun tayi a hankali tana tuno yadda taganshi sanye yake cikin dakkakiyar shadda baka da fara dinkin zamani akayi mata iyakar rigar cinya wondon kuma kuma pencil ne daga kasa daga sama ya bude yayi matukar kyau musamman daya daura black eye space a fuskar sa ita kanta hular dake kansa yadda ya daurata ta matukar kara fito masa da kyauwun kwantaccen bakin gashin kansa,,

ZAN RAYU DA KAIWhere stories live. Discover now