PAGE 79+80

1.1K 59 11
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          
loadιng...........✍🏻

                 
        🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
                      

Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
      *MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*

بسم الله الرحمن الرحيم

7⃣9⃣➕8⃣0⃣

A hankali take ɓuɗe idanunta dasukayi mata naiyi harta ware su a kan shi lumshe idanu tayi cikin ciwo ta buɗesu a hankali tana sake ƙarema ɗakin kallo karo na biyu idanun ta suka sauka a fuskarshi wacce ta kumbura sosai ƙura masa idanu tayi datake ganin dishi dishi har zuwa lokacin da ta koma ganin daidai wadu hawaye masi ɗumi suka gangaro mata har zuwa kan pillow datake kwance,
abubuwan dasuka faru wurin party take tunowa kukanta na fita a hankali har zuwa sanda aka sanyasu a mota,,

Miƙewa tayi zaune tana  cije lebbanta cikin ciwo don sosai kirjinta yayi mata nauyi da mararta,
a hankali ta sauke ƙafafunta ƙasa ta soma takawa a hankali tamkar wacce take kan tsantsi har ta isa inda yake tsaye tayo a daidai saitin kansa ta gefe kukunta na daɗuwa saida ta cije lips ɗinta ta haɗe su wuri ɗay yaddda kukan bazai fita ba saidai rawar da bakinta keyi da shisshiƙar kukanta data ƙasa riƙe wa,,

Hannunta ta ɗora gefen fuskar sa tana shafawa ahankali cikin tsananin tausayin da ƙaunar shi,sauke hannun tayi ta kamo hannun shi da babu drip a jiki ta ɗago zuwa fuskarta ta shafa hannunshi a fuskarta tanajin wani irin yanayi na tausayi da rauni sumbatar hannun tayi ta rike gam tana masa adduoe a cikin zuciyarta wasu kuma takan topa masa a wuraren daya samu ciwo musamman kanshi,,

Babu jimawa wasu doctors guda biyu suka shigo don suna saka ran zai iya farkawa a wannan lokaci sunyi mamakin ganinta kusa dashi har lokacin tana rsaye gefen shi dukda yadda takejin rashin ƙarfin jiki da ciwon jikin ga hawaye sharkaf a fuskarta harya jiƙa gaban  yar rigar dake jikinta ta asibiti,,

ɗaya daga cikin likitocin ya ƙarasa inda take yayinda ɗayan ya zagaya gefen shi,hakuri ya soma bata akan ta koma kan gadon nata cikin kwantar da hankali akan zasu dubashi ɗa kyar fa iya sakin hannunshi ta koma kan gadonta tana kallo suka janyo wani irin abu tamkar katanga na kwali suka raba tsakanin su dayake da ɗan tazara tsakanin su ya kasance bata iya ganin komai bata hangoshi,,

Kwanciya tayi tana kuka a hankali cikin toshe bakinta "tabbas ta yarda ita ɗin baƙinciki ce ga rayuwar ce, duk wani baƙin ciki nashi dayake ciki ta dalilin shiga rayiwar shine maiyasa zuciyata kikayimun wannan zabin,maiyasa zuciya ta  bakiyi duba da muhallinbdaya dace da tarbar kiba,
Zan fita a rayuwar ka Amjad koda hakan zai kawo karshen numfashi nane domin samun kwanciyar hankalin ka please ka daure ka tashi,ka daure ka tashi ka cigaba da rayuwarka cikin farin ciki please karka fara rafiya ka barni da mummunan ciwon rashinka gwara rashin  soyayyarka ta zamto ajalina nariga ka barin duniya,
don Allah ka daure karka mutu da fushina a zuciyarka hakan zai iya zamowa silar tawa mutuwar",,

Kukane sosai ya kwace mata wanda takasa iya riƙeshi sai kawai ta kifa kanta a saman pillow, daidai lokacin ya soma motsa hannunshi da sauri likiticin suka ƙarasa inda yake saboda karayar cinyar shi ya jima kafin ya soma buɗi idanun shi cikin tsananin zafin ciwo baya gane meyakeyi a ina yake kuma yana dai binsu da kallone kawai da idanun shi dasukayi mashi nauyi sosai saboda ƙunburin da fuskar shi tayi,motsawa yakeson yi amma yakasa ji yake kamar kanshi ne kawai nashi amma jikin tamkar baa jikinshi suke ba dole ya sake rufe idanun shi yana fitarda numfashi a hankali,ganin yadda ya farka ɗin batareda wani kuzari ba yasanyasu kyaleshi,

ZAN RAYU DA KAIWhere stories live. Discover now