Zan Rayu Da Kai

801 38 0
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          
loadιng...........✍🏻

                 
        🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
                      

Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
      *MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*

بسم الله الرحمن الرحيم

*_yar uwa ummie fulani(pure heart)ina tayaki murnar kammala novel din mai suna KE CE  Allah yabaki ladar faɗarkarwar dake ciki yasa mu amfana da abubwan dake ciki_*🤲🏻

5⃣1⃣➕5⃣2⃣

Tayi matukar mamakin ganin  panties din Nasreen  duk jini kwafa tayi ta koma ɗaki ta ɗauko leda ta sanya a hannunta ta a kyamace ta zubasu a leda ta ta fita tawatsar a babban dustbin ɗin dake chan bayan gida ta dawo Har tagama wankesu  ta fito ta shanya bai saukowa ba,

don haka saita cigaba da shirinta cikin sauri ta fito wanda yayi daidai da fitowar shi batareda Nasreen dinba kamar koyaushe haka ya sakar mata jakar a kasa ta ɗauka suka fita wanda fitar su tayi daidai da ficewar motar Nasreen din da alamu faɗan nasu yayi nisa sosai don kuwa tun zuwansu bata taɓa ganin ranar da Nasreen bazata fito yimasa rakiya ba,,

Motar pjaid din suka shiga yauma driver sa yake jansu suna baya kowa da abunda yake yi zahra na aikin tunanin da rashin sukunin zama kusa dashi shikuwa yanata faman latse latsen sa a laptop dinsa har suka isa ya dan ja wasu mintuna kafin ya rufe ya fice ta samu damar dauka itama ta bi bayanshi zuwa ciki,,

Kamar koyaushe hakan ta kasance cikin hidimarsa da ayyuka har suka dawo tana shiga ɗakinta ta wuce toilet tayo alwala ta fito ta kwasu kayan data wanke ta shiga kitchen tuwon shimkafa takeson yi wanda ta tanadi kayan yinsa tun safe shimkafar ta wanke ta daura a wuta hade da ruwan sanwa ta koma kan hade miya kafin ta wuce tayi sallar magrib ta dawo ta cigaba  ,,

Harta kammala bataji duriyar Nasreen ba balle amjad din ta shirya musu akan dining ta dibi nata ta wuce don tadaina zama cin abincin yadda takejin kishi na barazanar buga zuciyarta ,,

Tun wiri ta kulle kofarta tabar keys da tasan karshe tabiyo baasin kayanta wanda ita kuma batada lokacin wannan,
  Allah yataimaketa batayi mata cin mutunciba koda taga babu undies dinta guda biyar wanda zahra ta zubar ko don saboda basu daidaita da ogan bane haka kwanaki sukayita tafiya a wurin zahra babu daɗi babu sauki kullum cikin bauta da hidima ga cin mutuncin Nasreen dukda bata ga fuska ba amma hakan take takata son ranta saboda ganin tasamu dama a wurin Amjad din tunda faɗan nasu bai ɗauki wani lokaci ba suka shirya tana gama period don ba kasaifa take iya fushi da Amjad dinba a gado saida maganar zuwa ce tace sam babu,,
tsakanin sa da zahra saidai gaisuwa kawai shima da gyaɗa kai yake amsa mata sai kuwa bata umarni,,

*after three weeks*

Tashin su daga office wani mahaukacin katon shopping mall suka wuce ta dauka zai barta a mota amma saitaji yace fito haka suka shiga tana biye a bayansa,,

Saidai fa tana zuwa wurin kofar shiga ta kasa wata irin koface wacce ta kasu gida hudu ta glass wurin fita biyu wurin shiga biyu saikin sanya lura sosai gashi zagayawa takeyi saida kawai ka shiga ka tsaya tagama zagayawa zuwa ciki saika sauka,,

Miyau ta haɗiye kwal a makoshi tana kallon kofar yayinda shikuwa ya shige tuni ya barta tana sanya kafa taga tafara zagawa kafin ta rufe saita fito jiki na rawa tun baa ankara ba har mutane suka fara ankarar ana dariya har waɗanda suke ciki abinka da wuri ko ina glass wanda dariyar dasukeyi ce ta sanya hankalin Amjad din dawowa ga tuninin zahra,,

Sosai ransa yayi mugun ɓaci a fusace ya fita ya damko hannunta ya soma janta da karfi zuwa  wurin kofar inda nan take jikinta ya soma rawa tana sallati a zuciyarta har suka zaga ya jenyeta zuwa sama mutane na binta da dariya,,

Saida yakaita inda babu mutane kafin yayi jifa da hannunta yana faɗin kina hauka ne ko kuwa me ko kuwa so kike ki nunawa duniya kedin ure so foolish banda jahilci mai kikeyi vayan kina kallon yadda kowa ya shiga zaki sanya rainin a kaina ki daidaita kwalkwalki ki sanya mata nutsuwa ya fada yana nunnuna kansa ta gefe,
  Sai sauke huci yakeyi tamkar zai daketa,,

Murya na rawa cikin son yin kuka take faɗin kayi hakuri don Allah bazan ƙara ba kanta na kasa ta hade hannunwan ta wuri ɗaya cikin alamun roƙo,,

Tsaki yayi ya juya yabar wurin itama cikin sauri ta mije tabi bayansa tana jin haushin kanta na ɓata ransa dukda yaci ace yayi mata uzuri tunda ita bakuwa ce a wurin,,

A haka suka yi siyayyar tana biye dashi da basket din zuba kaya wanda kusan rabin siyayyar na Nasreen ne sai tsarabar su Ammyn da Suke shirin tafiya chan sallah,,


A gajiye ta shigo gidan tana jefa ƙafa batareda tana kallon gaban taba saboda uban kayan dake hannunta na siyayya dayayi da kyar ta iya hawa sama dasu takai cikin bedroom dinsa ta ajiye tana sauke numfashi wuya ga zufa ta jeƙa mata gashin dake gefen fuskarta da wuyanta da sauri ta koma don kwaso sauran a hanya ta hadu dashi yana kokarin hawa saman saida tajira ya wuce yana waya wanda da alama da Nasreen din yakeyi kafin ta wuce  sauran kayan ta kwaso wanda yawansu yakai na farkon yawa zuwa sama cikin  dakinsa,,

jin yana toilet saita soma gyaran bedroom din ta share shi tas ta fita ta don batasamu damar gyarawa da safen ba kitchen ta nufa ta dora girki ta koma ɗakinta tayi sallah ta koma kan aikin girkin,,

Taliya jelof ta ɗaura saboda itama tanason haɗa kayanta kafin ta kwanta bacci cikin ƙankanin lokaci ta haɗa ta juye musu ta zuba na masu aiki ta fita ta miƙa musu ta dawo ɗakinta saida tayi sallah kafin ta soma haɗa kayanta cikin babbar jaka dukda har lokacin baice ta shirya taji daiji yana waya yana tabbatarwa Ammyn akan zasu zo din,,
Saida tagama haɗawa tas kafin ta kwanta bacci cikeda dokin zuwan tafiyar su da fatan ya barta zuwa ganin iyayen ta,,
Washe gari a ko a office  ba zama yayi ba masu kula da zai barwa komai ya gana dasu ya bar musu amana don jirgin safe zasubi zuwa karfe biyu suka dawo gida ta soma aikin abincin rana tana gamawa yayi daidai da dawowar Nasreen daga aiki sannu tayi mata yayinda ita kumako kallon inda take batayi ba ta haura sama tana sanye da riga da wando waɗanda suka ɗame ta sai wata yaloluwar top data sauka har gwiwa ta baya tabe baki zahra tayi tana fadin nidai sandel,,

Bata jima da hawa sama ba saigata da kaya a hannu tana zuwa ta watsa wa zajra su dake tsaye a dining area tana ajiye plates da spoon sosai abunda Nasreen din tayi ya kawota iya wuya kallo tabi kayan dashi tamkar zata tanka saikuma ta share ta cigaba da abunda takeyi ganin hakan ya sanya Nasreen din jawo wuyan rigar Zahra ta haya tana fadin ke karamar ƴar iska,,

Wani irin juyowa Zahra tayi cikin tsantsar ɓacin rai tana watsa mata mugun kallo wanda ya tsorata Nasreen din amma datake tujara take nema saita dake ta bude baki tanafadin ki tabbatar kin wabke min kayan nan kafin anjim…

Bazanbyi ba nace bazan yiba zahra ta faɗa tana kara bude mata manyan idanunta ta ɗora da faɗin ko kinada yadda zakiyi ne ko kin isa ki sanyane dolena,, tana gama fadar hakan ta fusge hannun Nasreen din daga jikinta ta wuce hartana bangazarta,,

Kusan mutuwar tsaye Nasreen din tayi na wasu daƙiƙu kafin ta saki murmurshi tana girgiza kai ta nufi sama a zuciyarta tana faɗin anzo wurin tabbas zuwa Nigeria zaiyi daidai da rabuwarki da rayuwar mu har abada kai tsaye bedroom din amjad din tanufa tana sakin kuka cikeda kissa,,

*mrs noour ce*🥰



lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻

ZAN RAYU DA KAIWhere stories live. Discover now