🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
*MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*بسم الله الرحمن الرحيم
5⃣9⃣➕6⃣0⃣
Kasa daurewa yayi yace Ammyn my breakfast please ya karashe yana maganar tace Ammyn ta ɗago a fusace tace dama aurena kakeyi ko kuwa ni ɗin ƴar aikin kace ta faɗa cikin ɓacin rai ganin yadda ya nuna halin ko inkula a kan zahra koda ta gaishe shi baiyi maga ya jiki ba wannan abunne ya ƙular da Ammyn dama gashi baiyi sammakon shigowa dubata ba,,
Kusan minti biyu shiru babu wanda ya sake shewa komai yayinda Zahra ta shiga damuwa da tunanin tabbas tasan baici komai tanason miƙewa amma kunya ta hanata dukta rasa nutsuwar ta wata irin doguwar hamma dayayi mai ɗauke da ɗan hawaye a gefe idanun sa ya sanyata mikewa tamkar wacce aka tsikara tayi hanyar kitchen cikin sauri ta sake dumama ruwan shayin dayaji kayan haɗin ta kunna oven ta ɗibi bread yadda zai isheshi ta sanya ciki ta koma ta kwaso kwai guda biyu ta fasa tareda yimasa haɗi ta suya a plate ta haɗo bread ɗin data dumama da kwan ta haɗa tea a mug ta rufe ta ɗauro a babban tray ta nufo parlo kirjinta na bugawa na tsoron karya wulaƙanta ta agaban ammyn ga kunyar ammyn dama datakeji yayinda ammyn ta saki baki tana kallon ikon Allah kafin ta saki murmushi kaɗan tanayiwa Allah godiya cikin ranta dama lokacin nan zaizo da ɗanta zai samu gata da kulawar matarsa tabbas zahra ta cika ƴa mai tarbiyya wacce ta soma ganema ɗanta zama ita dole agareshi,,
agefen sa ta ajiye kan karamin table dage gefe ta janyoshi gabansa sama ta nufa tana gamawa batareda ta tsaya ba shima hartayi tagama ko kallon inda take baiyi ba sai ta ƙasan idanu yake binta da kallo a fakaice,abinci ya soma ci tankar an masa dole yadda yayi kicin kicin da fuska,,
Yana gama ci ya tashi ya fice fuska a haɗe don ya lura yanzu sam daga Afnan har Ammyn basa son farincikinsa sun samu bare wacce Allah ƙaɗai yasan manufar shigar ta rayuwar shi babu wani abu da zahra zatayi ma sa a duniya ta burgeshi koyaji sonta har gobe zuciyarshi ta ƙasa daina tuna masa marin datayi masa a bainar jama'a ga burin shi da ya taso dashi ta sanadin haka ta sanya daddyn ya hanashi waƙa anya kuwa zai iya yafewa zahra wanna laifin mai girma datayi masa,,
Shigar sa sashen su yayi daidai da tashin Nasreen daga barci toilet ya nufa yayo wanka ya fito itama banza tayi dashi don har kokacin bata kulashiba tana fushi ɗakin ta tawuce tayo wanka ta fito ta soma shafe shafenta tana saƙa da warwarar abunda zata yimasa tana gamawaya ata ɗauki key motarta tafito yana kwance kan kujera three sitter ta wuce shi ta fita,,
Lumshe idanu yayi cikin ɓacin rai mai Nasreen takeson maida nine yayiwa kanshi tambayar cikin ransa har ya hakuea sai kuma ya mike afusace yabi bayanta lokacin harta tada mota tayo reverse dinta ya tsaya gaban inda zata wuce doke ta take burki tana watso masa harara ta ciki motar,,
Matsawa yayi wurin motar ya buɗe murfin motar bangaren datake rai abace ya soma faɗin wai Nasreen mai kika ɗaukenine kok…
katse shi tayi tana faɗin abunda zuciyarka tagaya maka shina ɗaukeka har kana da ikon tare min hanya bayan duk irin tarin laifinka kake kokarin dannewa ka nemo nawa akanme wallahi pjaid sam daka ganni nan bana ƙaunar zuwanmu gidan nanhutu saboda nasan takurace kawai da fitina ammyn…Mari ya wanke fuskarta dashi wanda yasanta yin shiru batareda ta shirya bahannu ya nuna mata yana faɗin dont karki ƙara wanna kuskuren wallahi jikinsa na rawa tamkar zai rufeta da duka,,
Ɗagowa tayi dafe da kuncinta tana dubansa cikin tsananin mamaki kafin ta jinjina kai hawaye na zubowa daga idanunta ta dauki black google ɗinta ta sanya tana jan majina ta ba motar wuta cikin murde key ɗin doke ya matsa gefe cikin bigu murfin motar taja aguje tabar gidan tamkar zata rushe katangar gidanAllah yasa ma maigadin yayi hanzarin buɗewa yana tsaye dama,,
YOU ARE READING
ZAN RAYU DA KAI
RomanceLabari akan tsantsar soyayya ga Wanda baisan tanayi ba saima niyyar mummuna daya kudira akan ta ,amma hakuri da ladabi hade da karfin soyayya datake masa tun tana karama ya juyar da akalar kudiransa mummuna zuwa ga na alkhairi