🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
*MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*بسم الله الرحمن الرحيم
4⃣9⃣➕5⃣0⃣
Amsar wayar yayi ya jiya ya fita daga ɗakin cikin tsananin mamakin sanyin Zahra,,
Har ya shiga bedroom dinsu yana tuno yadda fuskarta ta kasance cikin tsantsar annuri da yalwar farinciki hade da tsantsar biyayya ga Ammyn,,kallon gefen da Nasreen din take kwance yayi dayake ta kwanta da wuri wai tagaji a office kuma shes on her period,inama ace hakan ta kasance ne daga pretty dinshi,,inama wannan soyayyar da girma ya kasance pretty dinsa ce lallai dayafi kowa farin ciki a duniya edukda yakanyi mata uzuri duba da yadda ko iyayenta bata cika damuwa da kiransu a ra'ayinta na yanci wato bata takura ba kar a takura mata,,
ajiyar zucoya ya sauke da karfi yana tabe baki hade da dage kafada cikin tunanin maybe zahra tayi hakan ne kawai don kewar iyayenta da kuma kadaici ba lallai itama inta samu dama ta so su kamar haka ba,kayan sa ya cire ya sauya zuwa na bacci ya kwanta da tunanin yadda zasu kaya da Nasreen domin kuwa Ammyn tace dole su dawo gida Nigeria suyi babbar sallah wanda yasan hakan bakaramin artabu zaayi da itaba,,
Ga maganar haihuwa da akoyaushe cikin tambayar shi take lafiyar zahra wanda yasan bawai lafiyar ce cikakkiya take nufiba na juna biyu ne,,
Wanda shi sam ko a mafarki baya fatan hada shimfida da zahra zamanta dashi bawai na tsawon lokaci bane don yarasa maizaiyi mata yaga fushi ko kunci da danasani akan kusantar shi datayi saima yake ganin tamkar jin dadin abubuwan dayake yimata takeyi,karamin tsaki yayi yana gyara kwanciya,,
Duk iya yadda yaso fahimtar da Nasreen din muhimmanci haihuwar da lokaci wanda ba nasu bane akoyaushe ubangiji zai iya yin hukuncinsa akansu wanda zai zamto musu nadanasani amma saita yita kawo masa uzururruka ta akan da sauran lokaci,,
Runtse idanu yayi cikin son ganin bacci ya daukeshi yayinda Zahra yau takejin zuciyarta sakayau bayan sun gama wayar jitakeyi tamkar da mama tayi wayar duk wata damuwa tata saitaji rabin ta ya kau babu bata lokaci bacci yayi gaba da ita,,
Kamar kullum ɗan karamain agogon dakin data saita shi ya shiga fidda sauti wanda ya sanyata juyowa takai hannu ta danna daya daga cikin madannin ya daina fidda kidan,,
"A hankali ta mike cikin yin mika tareda addu'ar tashi daga bacci ta sauke kafarta a hankali zuwa kasa ta nufi toilet wankan tsarki ta farayi ganin alamun tafiyar jinin haila ta kafin tayi wanka ta fito wanda fotowar ta yayi daidai da karfe uku da rabi na kasar cikin sauri ta sanya doguwar rigar data ahe saboda salla ta nufi inda shimfiɗar dardumar ta take ta soma nafilfikun ta cikin nutsuwa da tarin imani da tsoron Allah,,Har saida ta daidaita lokaci kamar yadda ta sama don tunda tazo ƙasar bata taɓa jin kiran sallaba koda sau ɗayane har kuwa a wurin aikin su,,
tana idar da sallah bata wani jimaba ta mike ta cire jallabiyar ta sauya da doguwar riga gown ta atampa tun kayanta na gida bata tsaya yin ko shafa ba ta fito zuwa ga aikin tadashi ta fara cin karo yana sanye da jallabiya fara khal hannunsa dauke da chazbaha a kullum takanyi mamakin inda yake zuwa sallah don ita dai bata taba ganin masallaci ba anan kusa dasu dukawa tayi tana fadin ina kwana cikin siririyar muryarta,,
YOU ARE READING
ZAN RAYU DA KAI
RomanceLabari akan tsantsar soyayya ga Wanda baisan tanayi ba saima niyyar mummuna daya kudira akan ta ,amma hakuri da ladabi hade da karfin soyayya datake masa tun tana karama ya juyar da akalar kudiransa mummuna zuwa ga na alkhairi