page 83+34

1.1K 51 1
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          
loadιng...........✍🏻

                 
        🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
                      

Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
      *MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*

بسم الله الرحمن الرحيم

8⃣3⃣➕8⃣4⃣

Karki damu lokacin kaɗan ne zaki daina jin komai"ya faɗa yana maida hannunshi cikin nata,,

Shiru tayi kusan minti biyar kafin ta ɗago tana kallon shi,shima itaɗin yake kallon,murmushi ta sakar mashi tana sake taunar maganar kafin ta furta amma bubu yadda ta iya ta dole ta faɗa,
ɗofanawa tayi daga gefen gadon ta zauna tana kallonshi tareda riƙo hannunshi sosai tana murzawa  tamkar tana masa tausa ta soma faɗin "amma baby da inada wata shawara inason kayi mun kyakkyawar fahimta a ganina a halin damuke ciki lafiyar ka muke buƙata first abubuwan danake hango mana kenan tun baya ya kamata kaima ka duba please ni inaga yadda gashi zuwa office ya gagareni ga kula dakai wanda shima nasan wani lokacin zaimin wuya em why not nace mu cire cikin nan zuwa…"

Kasa ƙarasa maganar ta tayi saboda yadda ya fuzge hannunsa daga nata yana mata wani irin duba cike da tsantsar mamakin ta, hawayen dasuka daina zuba masa nan take suka dawo runtse idanu yayi yanajin bacin rai cikin zuciyar shi akanta,,

Kamo hannun shi tasakeyi tana faɗin please baby ya kamata ka fahimce ni wane gata da kulawa  kakeson mu bawa yaron mu a wannan yanayin dakake ciki,rayuwar yanzu ya kamata ace komai mutum zaiyi saida plan ɗin da…

Janye hannushi ya sake yi daga nata,yana ɗaga mata hannun sama daidai saitin fuskar ta hannun na rawa sosai alamun tsananin bacin rai wanda ta san tabbas da lafiyar sa ƙalau saita sha mari,
"Mai kunnuwa na suke jiyemin ne daga gareki pretty,ashe har maganar ki ta ɗazu bata kasance har cikin zuciyar kiba u said i will be fine very soon,ta ya zaki dinga magana tamkar ba da amjad ɗin ki kikeyi ba,buɗe idanun sa yayi yana kallonta yadda fuskarta ta nuna babu wani damuwa ko danasanin akan abunda ta faɗa,girgiza kai yayi yana danne fushin sa kafin yace "idan ya kasance shine kawai ɗana a duniya taya kike tunanin zan barki ki aikata hakan bayan bamuda tabbas akan lafiya ta da kuma sake haihuwar ma please Nasreen na roƙeki ki cire tunanin nan a ranƙi don Allah karkiyi abunda zai sanya zuciyata bugawa please,,""
ya karashe yana kuka tareda riƙo hannunta cikin alamun roƙo,yafi kowa sanin wacece Nasreen tabbas a yadda yake kwance lallaɓawa ita tafi dacewa dashi saigashi shine take neman sanya zuciyar shi bugawa,ahaka take ikrarin tana sonshi,,

Sosai zuciyar ta takaraya hawaye ne yasoma silalowa daga idanunta kissing hannunshi tayi tana ɗorawa kan cikin ta " kayi hakuri baby am really sorry bana son in rasaka koda a mafarki ne" ta karashe cikin yin murmushi da son kauda maganar,,

shima kyaleta yayi don bayason maganar komai zai iya faruwa idan har maganar tayi nisa,ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta yace "inason inyi sallah pretty can you help me,"
Waro idanu waje tayo cikin mamaki kafin tace "haba baby wace irin sallah zakayi akwance bakada lafiya kabari ka warke mana kuma ma yaya kakeson inyi mka bayan kasan bawani jin daɗin jikina nakeyo ba please ka hakura atleast ko ƙafar ne tasamu sauƙi saikayi",

"For how long zanyita jiran warkewata bayan mutuwata bazata taɓa jirana ba, kwana na nawa anan batareda sallah ba bazan ita ba pretty saboda ina cikin hankali na a yanzu zan iya yi koda a kwancen ne"ya bata amsa ranshi aɗaj bace,,

ɗage kafaɗa tayi tana faɗin shikenan yarage naka nikam bansan yadda zanyi maka ba wallahi u can wait har lokacin da Nurses zasuzo sai suyi maka"tana gama faɗar haka ta miƙe ta ɗauki jakar ta tana faɗin su mom na jirana zan dawo da daddare idan kana buƙatar wani abu,,

ZAN RAYU DA KAIWhere stories live. Discover now