🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
*MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*بسم الله الرحمن الرحيم
*Nagode sosai da Adduoein ku gareni Allah ya ƙara mana lafiya bakiɗayanmu(ameen)*🤲🏻
_Habiba muhammad tareda Hafsat ina matukar godiya Allah ya bar kauna_🤝🏻🥰6⃣5⃣➕6⃣6⃣
Mikewa yayi ya fice daga parlon zuciyar shi chunkushe babu daɗi babu wanda hankalinsa yakai gareshi sai Ammyn da Zahra wancce jikinta yayi sanyi laƙwas a koyaushe tana ƙarfafa zuciyarta akan mai hakuri shikeda riba komai zai wuce zai zo mata da sauki muddin ta riƙe Addua da hakuri hade da juriya a zaman auren ta amma a yanzu zuciyarta ta fara rauni ta fara sarewa daga saran Amjad zai sota koda da kwayar zarra ne a zuciyar shi,
ƙasa tayi da kanta don jin hayawe na kokarin zubo mata ta soma kokarin hana hakan gudun kar wani yagane halin datake ciki,,abunda batasani ba shine idanun Ammyn tsab suna kanta tunda Amjad ɗin ya fice a ɗakin take nazarin yanayi Zahra tabbas abunda take zargi ya tabbata dole ne kuma tasan yadda zata bullowa amjad akan zaman sada Zahra dole ta ɗauki tsattsaura mataki akansa cikin sigar daya biyo musu dashi don bazata taɓa sake yayi rashin mace kamar Zahra tunda zuciyarshi ta iya yin hakurin zama da Nasreen toh dole ya ajiye duk wani kuɗiri da rashin so agefe ya riƙe zahra dukda batada tabbacin abunda ke cikin zuciyar shi,,
Wunin ranar zahra tayishi cikin farin ciki saida rashin nutsuwar zuciya na tunanin Amjad ɗin nata dukda basa barinta itakaɗai balle tayi nisa cikin tunani su Amal suna maƙale da ita ko baccin rana ma batasamu yiba saida itama tanajin daɗin hakan koba komai tana rage yawan tunanin shi a ranta,,
da yamma ta tattara su duka sukayi kutchen don yin girkin dare ta hana masu aikin kitchen ɗin ko yankan albasa tana tsaye har sukayi suka gama dining ɗin sama Ammy tace a shirya abincin achan don haka komai dazasu buƙata saida ta tabbatar ta ajiye kafin ta wuce sama ɗakin Afnan tayi wanka hade da ɗauro Alwalar,,
Kai tsaye gidan su Aj Amjad ya nufa wanda tun daga kallo ɗaya daAj yayiwa Amjad ɗin yasan akwai matsala,,
sun daɗe suna tattauna yadda zasu bullowa lamarin duk yadda Aj yayi dashi akan ya hakura ya zauna da Zahra ƙi yayi don baya sonta sam cikin zuciyarshi asalima yariga yayiwa Nasreen alƙawarin bazai zauna da Zahra ba dole aƙarshe ya kyaleshin da bashi shawarar ya sake bata dama na ɗan wani lokaci,,ya jima gidan sai bayan dasukayi sallar magrib ya nufo gidan Ammyn saboda kira da Ammyn tayi masa a waya nason ganinshi,koda ya ƙaraso saida yayi sallar isha'i kafin ya shigo gidan shida daddyn,,
Zaune suke gabaɗayansu a dining suna yin dinner kowa na jin daɗin abincin da Zahra ta dafa su afnan sun kasa shiru sai zuba santi da yaba mata sukeyi yayinda Zahra take cin abincin cike da jin nauyin daddyn wanda maibamasan tanayi ba Amjad ɗinma dayake tunani nacinsa a zuciyarsa abinci sam bayajin daɗinsa Ammyn na kule da yanayin shi gashi tunda ya shigo gidan kallon arziki sam bataga yayiwa Zahra ba koda ta gaidashi bai amsa ba har zuwa yanzu bai kalli inda Zahra takeba,,
shiya fara mikewa ya wuce bedroom ɗin Ammyn dayake a sama suke cin abincin saida tabari daddyn ya mike kafin itama ta mike don hankalinta naga kan Amjad tabi bayanshi,,
Kwance yake yana waya da alamu da Nasreen ɗin yakeyi jin ya Ambaci sunan pretty bata jima bada shigowa ya katse kiran tareda kashe wayar gabaɗaya don tun daya fita shida Zahra, Nasreen ɗin ke kiransa bai ɗaga ba gabaɗaya hankalinta ya tashi kishi ya sanyata gaba zuciyarta na hasaso mata abubuwa dayawa marasa kyau zasu iya faruwa hankalinta ya kasa kwanciya sai yanzu daya ɗauki kiran shine ta fashe mai da kuka akan yayi hakuri,
wanda hakan yana ɗaukanshi a rainin hankali ne yanzu gabaɗaya lamarin ta ya fara fita mishi akai sam wurin ƙinyi masa biyayya da rashin mutunci bata jin nauyi amma babu dama ya nuna fushinsa yanzu ta ce baiyi mata adalci ba akoyaushe kanta take kokarin samawa farin ciki bashiba wanna itace sahihiyar soyayyar ta gareshi?
YOU ARE READING
ZAN RAYU DA KAI
RomanceLabari akan tsantsar soyayya ga Wanda baisan tanayi ba saima niyyar mummuna daya kudira akan ta ,amma hakuri da ladabi hade da karfin soyayya datake masa tun tana karama ya juyar da akalar kudiransa mummuna zuwa ga na alkhairi