🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
*MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*بسم الله الرحمن الرحيم
7⃣➕8⃣
Bude idanunwan tayi da sauri tana duban Mama dake tsaye a kanta,,
Da sauri ta mike zaune tana fadin sannu mama cikin in ina hade da tsoro,,Kallon ta Mama ta cigaba dayi cikin nazarin yar tata tana kallon yadda bugun zuciyarta ke fita a hankali ta girgiza kai ta juya ta fice daga dakin,,
zahran ma ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana lumshe idanu badon taso ba ta ajiye wayar Bayan ta danna recoding ta mike tabi Bayan MAMA zuwa kitchen din,,
Sai Bayan magrib ta kammala aikin Bayan shigewar mama ta share kitchen din gabadaya aikin cikin sauri takeyinsa hankalinta naga cigaba da sauraran abunda takeji gani take tamkar wani zai chanja recording din,,
Alwalar tayi da sauri ta shigo dakin tana duban kan gadon Mamar babu wayar a kai duban inda MAMA take zaune bisa sallaya tayi idanunta suka yi raurau tamkar zata kurma ihu amma babu hali dole ta wuce ta cire uniform din ta sauya dana gida zuwa atampa doguwar riga ta tada sallah,,Mama na lura da ita amma saitayi tamkar bata lura ba,so take ta tambayi Mama ina wayar ta kasa har taci abinci tayi sallah isha'i bata samu fuskar tambayar ba saboda yadda Mama taki bata dama Baba na dawowa ta dauki abincinsa ta wuce dakin sa,jiki a sabule Zahra ta mike taje tayi masa sannu da dawowa ta dawo dakin ta kwanta lamo bisa katifar ta tana tunanin rayuwarta abaya,,
"Asalinsu"Asalin mahaifinsu dan jihar katsina su Biyar ne wajen iyayensu biyu mata sai maza uku babban su shine shamsudeen sai mahaifin Zahra sulaiman sai maimuna da Rukayya sai autansu mmahaifinsu ya turasu karatun allo shida Ismail garin Maiduguri sun sami tsahon lokaci anan daga bisani Ismail din malamin ya hada shi da kanin sa Wanda shima malami mazaunin Lagos ne,,
Yayinda shikuma mahaifin Zahra saida ya sauke a garin har girmansa inda ya soma dan dabarun Sana'a dazai rike kansa har lokacin da alamin nasu Allah yayi masa rasuwa saiya dawo gida inda ya soma karantarwar shima Wanda burin mahaifinsu kenan,,
Kusan shekaru biyar da dawowar sa aka hada auren su da yar uwarsa mahaifiyar zahra Jamila wacce tazamo yar uwarsa ce akayi hadin zumunci,,
Da yake halin nasu kusan dayane na rashin yawan magana ga hakuri sai zaman nasu ya dore cikin kwanciyar hankali tamkar auren soyayya,shekaru biyu Bayan aure Allah yabasu haihu da namiji yusuf Bayan shakaru biyar Mama ta haifi Zahra a lokacin kuma Baba ya kara aure da Uwani kunsan abunka ga malamai inda mahaifin uwani wato hinde shiya baiwa Baba auren ta,,
Bayan shekara biyu da auren uwani ta haifi umar Bayan shekara biyu ta sake haihuwar auwal sai lokacin kuma Mama ta sake haihuwar sani Wanda yake shine autan tindaga haihuwarsa daga Mama har Mama uwani babu Wanda yasa ke yin bari ma balle haihuwar,,
Wanda Hakan shine ya zamto silar kiyayyar Mama uwani ga Mama saboda bokaye suna gaya mata Mama ce ta hanata haihuwa yayinda baba yabar koyarwar gabadaya ya koma kasuwa yana saida kayan hatsi saboda daowar sa cikin garin katsinar Bayan ya gina dan gidansa karami ,,
Dakuna hudu ne gidan Mama nada biyu ,sai baba daya sai Mama uwani said an karamin kitchen dake tsakar gidan,ta Bayan dakunan kuma anan akayi bayi guda biyu na wanka dana bahaya,,
YOU ARE READING
ZAN RAYU DA KAI
RomanceLabari akan tsantsar soyayya ga Wanda baisan tanayi ba saima niyyar mummuna daya kudira akan ta ,amma hakuri da ladabi hade da karfin soyayya datake masa tun tana karama ya juyar da akalar kudiransa mummuna zuwa ga na alkhairi