🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
*MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*بسم الله الرحمن الرحيم
9⃣5⃣
"Pretty meye wannan ɗin haka"yayi tambayar zuciyar shi da idanun shi haɗe da muryar shi duk suna rawa yana kafeta da idanun shi dasukayi masa matuƙar nauyi,
Girgiza jiki tayi tana rausayar da kai gefe tareda turo baki gaba tace"pretty ai wanna sunan na amsa shi duk irin ƙauna da soyayya da kulawa danake yimaka amjad shine kake kokarin cin amanata bayan kafi kowa sanin yanzu wacece Nasreen wallahi sam amjad bazan ita wanna zaman ba da lafiyata da ƙuriciyata da kyauwuna wanna zaman na nakasassune irin ka don haka amjad ka sauwake min auren ka tun kafin takaimu da zamab court dakai, shiyasa nayi maka adalcin haka saboda basai na wahaltar dakai ba tunda baƙafa ce dakai ba" ta ƙarashe maganar tana ciro takarda da pen daga jakarta dake makale a hannunta tana miƙa mashi,Tabbas yasan daman lokacin nan yana zuwa sai dai baitaɓa tsammanin cikin kanƙanin lokaci irin haka ba bai taba tsammanin wannna cin mutinci da cin zarafin ba wurin Nasreen koda zata barshi duk iya yadda yake ganin zai iya jure haka ƙasawa yayi domin maganganun ta sun matukar girgiza zuciyar shi da sanya shi cikin wani hali kallon ta yakeyi hawaye nabin idanun shi yace"please pretty kiyi hakuri don koda haihuwa ne kiyi saina sawwake maki tabbas mafanar ki gaskiya ce babu wani mai iya zama dani inba nakasasshiya ƴar uwata ba amma don Allah pretty na roko ke gwiwa ta bisa ƙasa dukda vazan iya hakan ba don Allah pretty ki vari ki gaifa min abunda ke cikin ki koda ranar ne nasan Zahra zata iya min wanna sadaukar wa ta rainar min du…"
Dariya ta sanya haɗe da shewa mai ƙarfi tana tafa hannu cike da cin mutunci ta yatsina baki da hanci tana faɗin " huuh an zo wurin dama abunda nakeson ji daga gareka kenan amjad ai indai Zahra kake tunani, wallahi bazata taɓa iya ƙare rayuwar ta wurin yi maka wanna sadaukar wanba domin abun duniya ne kawai yake zaune da ita duk bayan irin cin mutunci da cin kashi dakayi mata, karka manta inda ta fito amjad, kaine baka da wayo amjad har yau zuciyar ka a rufe take bazaka taba gane mai ƙaunarka da gaskiya ba amma"kyabe baki tayi tana ɗage kafaɗa alamun ba wanna ya dameta ba sanna ta cigaba da faɗin "ba wannan ne matsala ta ba amma idan har hakane why not ka dauki cikin gashinan ka maidashi cikin ta tun kafin ka makaro amjad,idan har kayar da ita ɗin da sadaukar warta gareka"
da sauri ya kalli ledar yana budewa,runtsi idanu yayi zuciyar shi na bugawa wasu zafafan hawaye masu matuƙar radaɗi da zafi suka soma zubowa daga idanun shi ,idanun shi lumshe yana dafe da kirjinshi da hannu ɗaya ya ke faɗin
"Preety mai nayi maki na chanchanci wanna wulaƙancin duk irin soyayyar dana nuna maki karki manta wanna cikin shi kaɗaine mafarin cikina preety bayan duk halin danake ciki kece silar ingizani wurin rashin yiwa iyayena biyayye da shure umarnin su maiyasa zakiyi min haka Nasreen?maiyasa zaki ƙarashe gawar daba taki ba?maiyasa Nasreen vakida tsoron Allah da sowa ɗan uwanki abunda zaki sowa kanki ne? amjad ɗin ke ne fa preety mai yasa …ya ƙarashi yana kuka sosai cikin ƙaraya da rayuwar duniyar gabaɗaya,tsaki tayi tana faɗin"a'a amjad ban kasance haka ba babu yadda zaayi na iya kashe rayuwata a bautar ka kariga kazama marar amfani yanzu domin dukiya bata gaba amjad na aureka ne domin rsantsar kyau da haiba da cikar zatin ɗa namiji da Allah ya yi maka wanda kuma yanzu babu ko ɗaya daga ciki don haka karka soma tinnin zan zauna zaman tara dukiya kamar wacce jakar,don haka saika gaggauta maida ciki gareta indai zaka biyata zatayi domin abunda take zaman kenan,zan tafi Amjad!zan barka!zan fita daga rayuwar ka!a ƙarashe ina maka fatan alkhairi da zaman ka da ita saidai shawara ɗaya zan iya baka shine kayi kokarin daina sakin jiki da ita domin zata iya barinka a lokacin da kake gangarar mutuwa,
domin tun ranar da kayi accident na fano tsantsar soyayyar dakaje ta koƙarin boyemin ta Zahra,na tafi amjad!!!"tana gama faɗar haka ta juya ta fice daga ɗakin ta barshi cikin wani irin mawuyacin hali na ciwon zuciya,
YOU ARE READING
ZAN RAYU DA KAI
RomanceLabari akan tsantsar soyayya ga Wanda baisan tanayi ba saima niyyar mummuna daya kudira akan ta ,amma hakuri da ladabi hade da karfin soyayya datake masa tun tana karama ya juyar da akalar kudiransa mummuna zuwa ga na alkhairi