PAGE 97

1.6K 84 8
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          
loadιng...........✍🏻

                 
        🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
                      

Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
      *MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*

بسم الله الرحمن الرحيم

*Narasa mai ma zance gareku masoya da tarin kulawa da ƙauna hade da adduoe inku gareni,Allah ybar ƙauna,ana mugun tare*😘
_Allah kabaiwa dukkanin ɗaukacin bayinka lafiya,kasa mugama da duniya lafiya(ameen)🤲🏻_

9⃣7⃣

"Wai Zahra maiyasa zaki yi min haka,maiyasa zaki ɗauki mataki a lokacin da kika san hakan zai iya illata rayuwa da zuciya ta   please come vack to me Zahra dont live me alone Zahra"ya faɗa da ƙarfi yana bin motar da kallo tamkar Zahra ce gabanshi,har motar ta ɓacewa ganin shi bai daina surutun ba yana kuka sosai cikin tashin hankalin da bai taɓa shiga irinshi ba,
   da ƙyar ɗan bayero ya iya ɗaga shi daga wurin yana faɗin" sai hakuri yallabai amma doke kayi kuka wanda inaga bai kamata kayi shi a yanzu ba kamata yayi ka tashi kabi bayansu ko ina zasu  duk rintsu kar ka bari a tafi da ita"

Rungume ɗan bayero yayi a jikinshi yana faɗin "nagode ɗan uwa nagode sosai"ya sake shi da gudu ya koma cikin gidan cike da ƙwarin gwiwa wanda ada sam tunanin da dabarar bin bayansu baizo mashi ba,
   

Zahra kuwa kuka ne mai ƙarfi ya kufce  mata lokacin data daina hangoshi, take duk wani ƙarfin gwiwa da jarumtar data sanya wa ranta na kokarin rabuwa dashi taji sun gushe,lokaci ɗaya damuwa da tsananin tausayin shi mai ƙarfi ya lullube zuciyar ta,anya batayi kuskure wurin amincewa da wannan horon gareshi ba,tana gudun kar hakan yazamo masa wata babbar lalurar dazata sake jefa zuciyarta cikin tarwatsewa,
   Har suka isa airport ɗin  bata daina kuka ba,a haka ammyn ta fito da ita tana rungume da ita a jikinta,basu wani jima ba a wurin suka gama komai ga mamakinta daddyn bai biyo suba abunda taji ana ambata ma kamar ba Nigeria zasu tafi ba,
Saida suka zauna kan kujerun sannan ammyn ta shiga lallashin ta tareda ƙarfafa ta akan hakan shine daidai wanda intayi hakuri na lokacin kaɗanne,dole ta rage sautin kukan nata ta koma na zuci wanda ita aganin ta hakan tamkar bawa amjad ɗin dama ne na yakeceta a ranshi kamar yadda ya daɗe yana buri batajin tana da wannan girma da darajar da soyayyar dazai iya biyo bayanta aduk inda take .

Pasport da katin shaidun shi tareda wayoyi da system ɗinsa kawai ya iya ɗauka ya zuba cikin jakar,har ya nufi toilet don yin wanka sai kuma ya fito don tunanin dayayi zai iya missing fligth ɗin dasu ammyn zasubi duk da ba shida tabbacin zai iya samun ticket a cikin fligt ɗin nasu,drower ya nufa ya buɗe ya ɗibi kuɗi masu yawa ya cika a jakar jikin shi na rawa wanda shi kanshi baisan maizayi da kuɗin ba,sida ya cika jakar kafin ya rufe drower ya rayata jakar ya sanya takalmin shi sau ciki ya fice da sauri,a harabar wajen ya cillawa ɗan bayero keys ɗin gidan yana faɗin "ka kula da gidan"

Bai tsaya hawa mota ba don gani yake zai iya ɓata lokaci da gudu ya fice dafa gidan yana faɗin"am coming for u Zahra,babu wani abu dazai sake nasarar shiga tsakanin mu da rayuwar mu"
    Taxi ya tare ya shiga tareda faɗawa driver ya kaishi airpot in hurry please,cikin mintuna goma sha biyar suka isa don gudu sosai ya sanya driver yi fitowa yayi ya miƙa mashi kudin ya a faɗin "keep the change" da gudu ya ƙarasa ciki wanda yayi daidai da jiyo sautin ƙarar tashin jirgin da sauri ya rugu ciki ya isa wurin manyan glass window ɗin dake zagaye da harabar wurin tashin jirgin yana bin jirgin da kallo har ya ɓacewa ganin shi lumshe idanu yayi hawaye masu zafi suna zubo mashi .

ZAN RAYU DA KAIWhere stories live. Discover now