zan rayu da kai

1.1K 67 0
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com


loadιng...........✍🏻


🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*

Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
*MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*

بسم الله الرحمن الرحيم

1⃣1⃣➕1⃣2⃣

Ta sha adduoe sosai wurin jamaa zuwa mahifinta wanda saida yayi hawaye saboda bashi kujerar danayi ,,

walima sosai aka yi a gida bayan sun dawo har katon rago saida baba na lagos ya siya mata,,

Mama uwani ma kam harda kyautar doguwar riga tabani wanda nasha mamaki harna gaza boyewa a lokacin data miko min da kyar na iya bude baki nace nagode ,,

A ranar ne kuma ya samu Baba da maganar cigaba da karatuna na gaba da secondary inda Baba yace sam aa bai amince ba,,

Duk yadda yaso nunawa Baba muhimmanci dake cikin karatun ki yayi akarshe dole ya hakura bayan ya tursasa Baba ya amince da zuwa na lagos nayi azumi da sallah achan tunda baifi sati biyu ba,,

Nayi murna sosai don kuwa tunda yaya yusuf yatafi nake burin zuwa nima koda sau dayane kafin inyi aurren kamar yadda baba ya fada,,

Washe gari tunda na tashi nake aikin shirin tafiya yadda nake zakwadi kaikace saudin zan tafi ni kaina ina mamakin yadda nake matukar farin ciki da tafiyar duk lokacin dana tuna saina saki murmushi ,komai nawa na gama kimtsa shi a ranar har Aisha nayiwa sallama dana shiga gidan da daddare bayan dawowa ta ma cigaba nayi da tsintsintar abubuwan danasan zan bukata Mama dai na kallona har nayi na gama na kulle jaka,,
Zama nayi daga gefen gadon ina fadin wash Allah na nagaji sosai bayana na zame na kwanta babu bata lokaci bacci yayi gaba dani

Tun karfe hudu na dare Mama ta tasheni nayi wanka na shirya don muna sallar asubahi zamu wuce sosai mama tayi min fada akan na tsaya matsayina batason hangi da duarawa kai abunda yafi karfin ka,nayi riko da mutincina domin shine mutincin su harsaida na zubar da hawaye,,

Dukada ta saba yimin fada nasan wanman dabanne hardana wayar Aisha dana amso,nayi kuka sosai dazamu tafi tamkar na tafi kenan kamar banice ki wanna rawar kafar ma jiya,,

Tun ina kallon hanya ina karanta sunan garuruwa da kauyuka harna sare gabadaya zamanmotar ya isheni kafafuna duk sunyi tsami dukda ana tsayawa muyi uziri ko siyan abinci sai goma da rabi muka sauka,,

A matukar gajiye muka isan gidan Wanda duk murna da dokin tafiyar da nakeyi sainaji abun ya fita kai na da gudu yan mantan gidan suka rungume ni suna murna,,

Sai da Anty tayi musu tsawa tana fadin Baku lura da tafiyar data kwaso ne kuke niman kayar da ita kasa,,

Murmushi nayi ina daukar da kaina kasa,har kasa na duka na gaisheta bata amsa ba saima kama hannun na da tayi ta kaini cikin wani daki Wanda da dukkan alamu na yan matan gidan ne toilet ta nuna min da hannun ta tana fadin oya maza 'yata shiga kiyi wanka sai mu gaisa tana fadar haka ta juya takorasu duka da suka biyo bayan mu ta ja min kofar,,ina jiyo su suna rokonta cikin wasa da dariya ita kuwa tace Sam babu Wanda zai Shiga,,

Murmushi tayi tana sauke ajiyar zuciya a lokaci daya mayafin dake jikinta ta cire ta shiga Bayan tayo wanka da ruwa mai zafi sosai alwalar ta dauro ta fito ta shiga rama sallar da batayi ba,,

Koda ta fito kasa cin abincin tayi sai anty ta hada mata tea mai kauri tasha tayi musu saida safe ta wuce ta kwanta babu bata lokaci bacci yayi a won gaba da ita,,

ZAN RAYU DA KAIWhere stories live. Discover now