🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
*MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*بسم الله الرحمن الرحيم
9⃣9⃣
A daren ranan Mahfuz y asamu iyayen shi da maganar auren,dukkansu sunyi murna musamman dayake ɗan gata ne,saidai jin bazawarace ya sanya mom ɗin nashi turjiwa amma dayake komai yakeso shi sukeyi ya sanya dad ɗinshi baiwa mom ɗin baki dole ta amince badan ranta yaso ba,musamman dayake dad ɗin nashi bayarabe ne baiga wata matsala ba don Mahfuz ɗin ya auri bazawara ba .
Bayan sati ɗaya iyayenshi sukaje neman aure inda babu bata lokaci aka sanya biki wata ɗaya ba tare da iyayen sun san zaman tsiyar da sukeyi ba valle abata damar yin istibra'i ba,cikin girma da mutunci aka rabu irin na ƴan boko.
Ranar wurin Mahfuz Nasreen ta kwana suka durji juna sosai na ban kwana,domin tanason ta fara gayra akan lokaci wanda mom ɗinta tabata shawara a matsayinta na wacce zata auri saurayi,
Shiri sosai ya kankama tsakanin gidajen na ƴan boko da ƙarya ga giyar juɗin gwamnati dake shawo jinin su musamman mahfuz da har lokacin mahaifin shi yake mataimakin gwamnan na lagos saidai dukda muƙamin sa mahaifin Nasreen yafi shi kuɗi sosai,
Tun saura sati ɗaya biki Nasreen ta dawo daga paris inda akayi mata surgery na breast wanda akayi nasara sunyi mata girma da cika yadda takeso nan suka dasa parties kala kala waɗanda duk taron abokansa ne marasa kamun kai yayinda kwakwata koda wasa baisanar ma Aj ba valle Amjad ɗin dasuke tunanin yananan zaune babu lafiya,
gyara kam tasha shi sosai suka kasha kuɗi musamman da Nasreen ɗin tasan halin mahfuz ɗin nabin mata saidai kuma tabi zuciyarta data yarda da mahfuz ɗin akan ya daina tun haɗuwar shi da ita kuma dayyi aure shikenan,anyi kuma sa'a bai ƙara neman wata yarinya ba tunda aka sanya ranar bikin suhar zuwa yau da aka ɗaura aurensu wanda ya tara shahararrun masu faɗa aji da muƙamai komai an gudanar cikin girma da wayewa an kai amarya gidan surukarta aka buɗar kai inda mom ɗin mahfuz ba ƙaramin girgiza tayi da ganin Nasreen ba a matsayin matar mahfuz wanda ko kusa bata taɓa tsammani ba bai kuma gaya mata ba har aka gama,Shiyasa ko yaushe tayi masa zancen su Aj saiya banzatar da maganar,ashe da dalili,ba ƙaramin bata ranta abun yayi ba wanda taci alwashin sai sun gane kurensu kuwa,
Amarya da ango antare an zuba soyayya tamkar ba'a taba sanin juna ba saboda mugun gyaran datasha ciki da waje,kwana uku dayin aure suka lula ƙasar waje don barje amarci wato honeymoon,
Tunda Amjad ya fita da Zahra suka nufi cikin gare babban hotel yai musu lodging ɗakin bavban tamkar flat,a ranar kuwa taga mai ake kira soyayya tun tana kunya da tsoro har ta saki jiki suka barje soyayyar su,kwanan su biyu ana vasu koda leƙa waje saidai masallaci suna leƙe da juna,a kwana na ukku ne suka wuce ƙasar makka inda tayi tayi ya barta suyi sallama dasu afnan amma yaƙi ƙimemem akan sa haɗu a Nigeria dole ta hakura,
Ba ƙaramin daɗin garin takeji ba musamman yadda yake nuna mata wata irin zazzafar soyayya ibadar ma tare sukeyi,satin su biyu suka wuce holland domin akwai abubuwan dayake son gudanawar tsarabar da suka loda kuma suka biya kai tsaye aka wice dasu Nigeria,Babu yadda batayi ba akan su suka gidan su amma yaƙi ƙememe wanda ta san dalilin baya na bayason tuno rayuwar shi da Nasreen ne tunda bai samu damar chanza komai na gidan ba,
YOU ARE READING
ZAN RAYU DA KAI
RomanceLabari akan tsantsar soyayya ga Wanda baisan tanayi ba saima niyyar mummuna daya kudira akan ta ,amma hakuri da ladabi hade da karfin soyayya datake masa tun tana karama ya juyar da akalar kudiransa mummuna zuwa ga na alkhairi