Zan Rayu Da Kai

999 51 1
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          
loadιng...........✍🏻

                 
        🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
                      

Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
      *MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*

بسم الله الرحمن الرحيم

2⃣7⃣➕2⃣8⃣

Ko kuwa shima yana kaunar ta tamkar yadda take kaunar shi har dashi yazo neman auren ta da kanshi cikin kankanin lokaci,,juyi ta sake yi ba tareda ta bude idanuwanta a hankali ta kira suna Aisha wacce ke zaune gefe ta zuba mata idanu cike da tausayawa irin halin da kawar tata take ciki,,

Wallahi friend koda wannan auren da wata manufa yayi ko kuwa ince miki daukar fansa toh tabbas ina bai tabbatar miki wallahi zan zauna zan yi hakuri zan jure duk wani damuwa da bacin rai da zan shiga,,

Domin banajin akwai abunda zai yi mun a duniya komai muninsa soyayyar da kaunar sa ta ragu cikin zuciya ta burina a duniya shine in rayu da shi in kuwa har ya aure ni wallahi zan rayu da shi har karshen rayuwa koda kuwa hakan yan nufin zai jefani a wani hali,,ganinsa yafi komai sanya rayuwa ta cikin farin ciki,,

""Zan rayu da kai,,""
"" zan rayu da kai ""
Zan rayu da kai""har karshen rayuwa ta ta karashe maganar cikin sanyi da fitar da wasu zafafan hawaye zuciyarta na zafi yadda ta kamo da ciwon sonsa yana chan tareda matarsa ba tareda yasan da hakan ba,,

Share hawayen Aisha tayi cike da tausayin kawar tata ta ruko hannuwanta  duka tana kallonta bakinta ya Gaza furtawa Zahra komai,,

Bude idanuwan ta tayi wadanda suka chanza kala sukayi jajur saboda damuwa kallon Aishan tayi cikin ido a hankali ta soma fadin mai yasa baba zai ki amincewa be?
Meye aibu ko laifin shi,,?
Wallahi ina son shi haka,,zan aure shi koda kuwa hakan na nufin karshen tawa rayuwar……

Da sauri Aisha ta sanya hannu ta akan labban Zahra tana girgiza mata kai murya cike da tausayawa ta hadiye nata kukan ta soma fadin please ki daina fadin haka don Allah kina addua Zahra nima ina tayaki insha Allah adduar mu zata zamo karbabbiya saidai banason kina yiwa kanki mugun fata insha Allah zaku rayu da juna cikin farin ciki da kauna hade da soyayya mai ban mamaki har karshen rayuwarku,,nayi miki alkawari ninkawa fiyeda da akoyaushe zan tayaki rokon ubangiji ya cika miki burinki in har alhairi ne gareki domin bazan so idanuwanki su rufe akan soyayya ba Wanda vazai zamto alkhairi gareki ba,,

Komarda kanta tayi ta kwantar akan pillow hawayen har lokacin yana zubowa daga idanunta murmushi yake tayi tace bazaki gane bane Aisha shidin tabbas Alkhairi ne a koyaushe ina ji ajikina shidin alkhairi ne,,
Akoyaushe nayi tsayuwar dare akan rokon zabin ubangiji soyayyar sa mai karfi ke sake lullubemin dukkan magudanar jini da zuciyarta ,,

★★★★★★★★★

Tare suka tashi baccin safen daya koma suka nufi toilet tana makale dashi sukayi wanka tare suka fito shirin ma kusan tare sukayi shi don ita ta gyare masa gashin kansa yayinda shi kuma yayi mata shafa kananan kaya ya sanya riga da wando milk color marasa nauyi itama kwalliya tayi sosai cikin doguwar Riga gown light blue wacce ta kamata daga sama zuwa kugu ta nude anyi mata kwalliya sosai a jikinta tamkar wacce zata je party hula ta sanya a kanta wacce take tamkar set din kayan ta bazo gashin dokin ta zuwa bayanta sosai sun yi matukar kyau suka nufi bangaren Ammyn hannun su sagale dana juna cike da so da kauna,,

Tunda suka shiga ta kimtse fuskar take shan kanshi koda Afnan din ta gaidata a dan dakile ta amsa saida ta zauna kan kujera saanan ta gaida Ammy ba tareda wani girmamawa ba ita kuwa cike da kulawa da so ta amsa tamkar batajin zafin abunda tayi ba,,

ZAN RAYU DA KAIWhere stories live. Discover now