Zan Rayu Da Kai

1K 53 0
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          
loadιng...........✍🏻

                 
        🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
                      

Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
      *MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*

بسم الله الرحمن الرحيم

4⃣1⃣➕4⃣2⃣

Shikuwa har ga Allah Sam ya ma mance da batun Zahra da suke tare sai ma system dinsa daya maida hankali akan ta yake aikinsa hankali kwance yayinda Nasreen kusan rabin jikinta ke leke da nashi dukda ba dadin zaman taji ba yadda shidin ya dan rankwafa kansa kasa kadan,amma haka ta hakura dukdon ta nunawa zahra miji natane ,,ta dauki magazine ta fuske tana dubawa cikeda dagawa,,

Ita Sam ma Zahra bata lura da abunda Nasreen din ke nufiba hasalima taga ganin jirgin ya daidaita kowa ya fara harkar gabansa itama saita dauko alqu'ran dinta ta soma karantawa ko zata samu nutsuwa cikin zuciyarta,,

Haka suka kasance tun koda ma'aikaciyar ta tambayeta abunda take bukata bata iya bada amsa ba sai ruwa kawai data iya ambata ta cigaba da karatun ta,,
   Ta dade tanayi har bacci taji ya soma daukarta nan ta ajiye AlQurani ta dan zame tareda rufe fuskarta da mayafin ta babu dadewa bacci mai nauyi ya dauketa saboda rashin yin ishasshe jiya,,

Ta jima sosai tana bacci kafin ta tashi cikin sallati da addua hamma tayi tana duban agogon dake daure a hannun ta awowi hudu ta dauka tana bacci  karamin tsaki tayi ta saci kallonsa a wayance Wanda yayi dai dai da juyowar sa gareta tabe baki yayi ya juya tareda kwantar da kansa a kafadar Nasreen wacce itama bacci yayi takeyi,,

Koda maaikatan suka dawo da kansa ya fada musu abunda zasu kawo tana ta kokarin hada turancin ta wuri daya da tunanin abunda zatace taga kawo mata hamdala tayi tana dubansa ganin hankalinsa baya gareta ya sanyata bude yar farar robar friedrice ce ba wata maiyawa ba sai tarin uban ganye da aka zuba a sama da naman kaza a gefe,,
Sosai ta zage taci abincin saboda yunwar datakeji,,

Dayake lokacin ba daya bane da namu sai dare sosai suka sauka wannan karon ma biye take dasu da yarjakarta a hannu su kuwa suna manne da juna tun fitiwar ta sanyi ya addabeta sosai ko numfashi ta fitar sai taga hazon sanyin ya fita a haka suka karasa inda aka gama checking kowa ya turo jakar kayansa tana ture da nata kamar yadda taga anayi hakan ta sanya natsuwa itama tayi yayinda shikuma yake ture da nasu har suka fita harabar airport din,,

Motoci biyu ne suka zo daukar su yadda suka taho hakan sukayi ta Shiga mota daban zuwa gidan sosai ta saki baki da hanci take kallon garin yadda ko ina yake da haske ga mutane suna hidimar su hankali kwance tamkar ba dare ba Allah mai iko ta fada Wai yau itace a wannan kasa,,

Mamaki ta Shiga yi tana jinjina kyau da tsarin haduwar gidan koda dare  ne jinjina kai tayi Bayan ta fito daga motar lallai dole Nasreen kiyi dagawa wannan rayuwa haka tamkar mutum ba zai mutuba ta fada cikin zuciyarta,,

Maaikatan gidan suka dauko musu jakun kunan su sai gaidasu sukeyi cikin tsantsar ladabi yayinda ita dai sai daga kai kawai takeyi duba da yadda sudin ko amsawa basayi a haka suka Shiga cikin gidan da hannu tayi wa Wanda ya dauko mata kaya nuni da inda zaikai,,
Itama bin Bayan shi tayi domin tagajii sosai,,

Saida tayi da gaske kafin ta iya kunna ruwan jacuzzi dake bayin ta samu tayi wanka ta dauro alwalar ta fito,,

Kayanta ta maida ta soma rama sallalin dabasu samu yiba,,

ZAN RAYU DA KAIWhere stories live. Discover now