🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
*MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*بسم الله الرحمن الرحيم
8⃣9⃣➕9⃣0⃣
Sau uku tana gwada kiran amma yaƙi shiga amsa ɗaya take samu shine a ƙashe wayar take, ƙaramin tsaki tayi ta ajiye wayar gefe ta tada motar ta ƙai tsaye wurin wani shaƙatawa ta nufa, babban wurine wanda ya haɗu iya haɗuwa an ƙawata sosai da duk abubuwan nishaɗantarwa da shakatawa,parker motar ta tayi a harabar parking ta sanya eye glasses a idanunta ta fito da wayoyi da handbag ɗinta rike a hannu,chan ciki ta shiga bayan wurin,wurine mai girman gaske tamkar ba'a cikin gari yake ba tafkeken ruwane wanda baka iya gano ta inda yake shiga da fita ga ta wurin ga shuke shuke ko'ina matuƙar kyau sanyi da iska na kaɗawa sannu a hankali,mutanen dake wurin sai hidimar su sukeyi hankali kwance yawancin wurin zakaga mace da namiji ne ko kuma kungiyar friends na mata da maza, ita kaɗaice take zaune a sit batareda kowa ba,tana kallon yadda yan mata da samari suke soyewa a wurin hankalin su kwance gaba ɗaya kuma sai taji ta takura nitsuwar datake son samu saitaji ta gaza samun hakan saima bacin rai da baƙin ciki da suka mamaye zuciyar ta harta zubda hawaye,
"shikenan ita haka zata ƙare rayuwar ta cikin baƙin ciki da damuwa da wannan abunda da ya faru ga mijinta"
Runtse idanu tayi tana gyara zama tabbas ita kanta tasan bazata iya zama da amjad a yanzu ba dukda tsananin son datake mashi batajin zata iya riƙe kanta batareda sake saduwa ba har abada,tun a yanzu ma gabaɗaya ta takura ta shiga wani hali taya zata iya zama dashi batason ɓata jininsa danawa shiyasanya ta yabke hukuncin zubda cikin ta samawa kanta damar yimasa duk abunda tasan zai sanya ya saketa"Wayar ta ta ɗauka ta soma latse latsen ta aciki tanayi tana ƙurbar juice dukkanin shafukan sada zumunta Mahfuz sai da tabi ta tura masa da sako na hy sanna ta kashe wayar gaba ɗaya ta ajiyeta ta maida hankalin ta kan kallon ruwan dake wurin,anan ta wuni har yamma sosai sannan ta miƙe ta tafi bawai don zaman ya isheta ba saidan gundira da tayi da zaman ita kaɗai,,
gaba ɗayan Wunin nasu ya kasance cikin shiru da tunani a kokarin shi na ganin ya kiyaye alƙawarin daya ɗauka naƙin sakin jiki da ita baya iya koda amsa mata da eh ko a'a ne saidai idanu kawai yakan zuba mata idan hankalinta baya gareshi da sun haɗa idanu zai rufe nashi idanun yayinda da ita kuma hakan yasanya ta sanyaya tareda kame kanta daga gareshin saboda gudun kar hakan ya bata ranshi,duk wani abu data sabayi mashi na kulawa bata fasa ba saidai daɗi akai, ƴar sakewar da shakuwar data soma shiga tsakanin su duk ya kawar ta hanya ƙin kulata saidai har cikin zuciyar shi yana jin wata irin girma da darajarta sosai fiye da yadda kwakwalwar ke tunani komai tayi burge shi takeyi yanayin yadda take komai cikin sanyi da amvaton Allah baya gajiya da kallonta a fakaice don kuwa baya taɓa bari su haɗa ido kofa ganshi yana kallon ta sai dawowar Aj ɗakin ne da yamma ya sanyashi yin magana ita kuma ta kuma gefe chan kan kujera tana karatun alqur'anin ta cikin zuciya,,
A kwanaki huɗu da sukayi wata irin soyayyar sirri ce ta kulla tsakanin Mahfuz da Nasreen duk wata damuwa da kewar mijinta dake damunta Maflhfuz ya kawar mata tun safe inra fita zasu haɗu wuraren yawo da shaƙatawa iri iri achan zasu wuni, ko asibitin tare suke zuwa wanda hakan ba ƙaramin tada hankalin Amjad yakeyi ba don yafi kowa sanin waye mahfuz dukda zuciyar shi na ƙarfafa shi akan bazai ci amanar shiba,haka in sungama zaman asibitin tare suke tafiya ban ɗinma sai sun gama zaga gari yayi mata siyayya sanna zai kaita hotel ɗin dasuke,haka da dare ma aikinsu kenancharts vasa gajiya zantuƙa iri iri kowanne yana daɗa rura wutar sha'awar sa ga ɗan uwan shi duk da babu wanda ya iya fitowa ya faɗi abunda ke zuciyar shi,Nasreen kam dalilin cikin jikinta ne datake jira har lokacin bata samu cirewa ba haka shima ya barine saita gama sakin jikinta dashi tagama buƙatuwa da ɗa namiji sannan zaibtunkareta gabaɗaya yasan bazata taɓa ƙin bashi haɗin kai ba,,
YOU ARE READING
ZAN RAYU DA KAI
RomanceLabari akan tsantsar soyayya ga Wanda baisan tanayi ba saima niyyar mummuna daya kudira akan ta ,amma hakuri da ladabi hade da karfin soyayya datake masa tun tana karama ya juyar da akalar kudiransa mummuna zuwa ga na alkhairi