© *_HAKKIN MALLAKAR_* ® *_Maryam Abdul_* _______________________ *_INDA RAI

3K 116 1
                                    

© *_HAKKIN MALLAKAR_*

® *_Maryam Abdul_*

_______________________

*_INDA RAI....._*
              *_ASHE DA RABO......_*


        *DAGA MARUBUCIYAR*
____________________

1. *HADUWATA DAKE*
2. *ABDULMAJID*
3. *A DALILIN PRE-WEEDING PICS*
4. *ZURI'A D'AYA*
5. *MEYE LAIFINTA?*

Wattpad me on @MaryamAbdul559





*Dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah madaukakin sarki, Wanda mulki da buwaya suke nasa ne, tsira da aminci su tabbata ga masoyinsa d'an gatansa masoyin mu Annabi Muhammad S.A.W tare da sahabbansa masu shiryarwa da mafifitan iyalan gidansa, tabiai zuwa tabi'uttabi'una zuwa shuwagaban Musulunci ameen..*

_Wannan labarin Mai suna a sama kirkirarren labari ne Mai cike da darussan rayuwa, idan yaci karo da halinki/ka to arashi ne a yafeni_🤗

*Masoya masu bibiyar labaraina ban manta da novel din da na alkawaranta muku ba na _A KARKARARMU_ kasancewar say true life story dole sai na samu dukkan abinda nake bukata kafin nace zan rubuta shi, domin kowa yasan rubutu ba haka kawai akeyinsa Kara zube ba, dole saida bincike da kuma nazari, Amma inshaa Allah yana nan tafe..*









{ 1 }


"Daddy wannan, no Daddy wancen" wata kyakkyawar k'amar yarinyar dake tsalle-tsalle cikin katon mall din ke fad'a tana nunawa Dadyn nata abinda takeso ya dauko mata inta nuna wannan sai ya dakko sai tace aa wancen ne..

Kallon sa yakai gun wata kyakkyawar farar matashiyar mata dake gefe ta zuba musu ido tana kallon shiriritar 'ya da ubanta, tasa hannenta ta tallabe matashin cikinta daya fito yayi dass ya Kara mata kyawu...

Langab'ar da Kai yayi tare da kallonta ya nuna mata yarinyar da baki alamar tasa baki, murmushi kawai ta saki tare da masa alama da ido cewar kunfi kusa...

Hararar zamu had'u ne ya watsa mata tare da yin kwafa ya maida idonsa kan yarinyar dake nuna masa wata k'atuwar teddy tana fadin "yawwa Daddy wannan" tana sakin murmushi alaman tana son teddy sossai, sauko mata da teddy yayi tare da dukawa daidai tsayinta ya sunkuya ya m'ika mata sannan ya kama hannunta cikin marairaicewa yace "angle dady is tired and mommy too let go home pls!"

Hannayenta ta zagane a wuyarsa ta rungumesa "yes daddy am tired too let go" tace tare sungumar teddy ta, shima Mik'ewa yay tare da basket din da ta cika da tarkacen chocolates, biscuits, sweets da sauran tarkacen ta..

Murmushi matar ta saki ganin yadda yadda yadda tallabo kwandon yabi bayan yarinyar kawai wani guard dinta a fili tace "SALAMAH! Rigima amma maganinka kenan   kaida ke biye mata" tabi bayansu itama da nata tarkacen data d'iba, biya sukayi aka zuba musu a leda sannan yaran shagon suka bisu dasu mota.....

Tafe suke tana zuba musu surutu masa kan gado baban na biye mata yayin da mamar ke musu kallon sha'awa tana musu fatar d'orewar wannan soyayyar da shakuwar dake tsakaninsu...

Daidai wani eatery wadda a kallo kawai zaka tabbatar eh ba karya ya had'u yayi park domin sudan yi lunch tunda Salamah ta cinye musu lokaci....

Akan idon ta suka shigo wadda a kalla Fara aikinta gurin wannan shine ganinta na 3 ko 4 da tayi musu a wurin, kuma tun farkon ganinta dasu ta kulla wani buri a ranta game dasu...

Cikin kwarkwasa da kissa irin na gogaggun 'yan bariki ta isa Inda suke zaune tana wani kashe ido tare da tambayawar su me suke bukata..

Matar ce kawai ta lura da ita shikam duka attention nasa nakan 'yarsa dake gayamai me takeson ci, Kai tsaye ba tare daya kalleta ba ya gaya mata abinda zata kawo musu, ba tare da b'ata lokaci ba kuwa ta dawo tare da wata Waiter suna dauke da manyan trays suka ije musu tare da fadin "sir have ur lunch"

"Thanks" yace still ba tare daya kalleta ba duk da kuwa kafesa da mayun idanuwanta da tayi..

Itadai matar duk tana hankalce da take taken wanan Waiter din wacce da gani ba tambaya rikakkiyar 'yar duniya ce, murr tasha sossai ganin yadda ta tsaya musu akai kamar an dasa ta..

Kallon sa yakai ga matar tasa ganin tak'icin komai ta kuma had'e gabas da yamma yai mata alaman yadai da ido, d'auke ido tayi Wanda sai lokacin ya kula da Waiter dake tsaye a gurin ya gane dalilin fushin matarsa...

"U can go" kawai yace mata, tare da dauke kansa, cikin jin kunyar kanta taja jiki tare da matsa can take samu wuri ta zauna saidai duka motsinsu nakan idonta, itakam matar duk dadin abincin gurin da takeji yau kam tsakura kawai tayi shima Dan kar mijin ya tuhumeta ne....

Tana ganin sun mike zasu wuce gurin biyan kudin, cikin sauri tasha gabansu tare da cewa su bata kudin zata Kai, shima cikin k'osawa da shisshiginta ya mika mata kudin tare da sungumar 'yarsa yayi gaba, kallon banza matar ta watsa mata tare da take masa baya...

Murmushi Mai cike da ma'anoni waiter ta saki tare da fadin "easy u don't know me oo" tare da ciza lips dinta...

"Daddy nifa kar mu k'ara zuwa wannan eatery gaskiya" matar ta fad'a bayan motar tasu ta lula kan titi, murmushi ya saki ganin kishi k'arara fuskar matar tasa...

"Shikenan princess yadda kike so" tare da kashe mata ido, murmushi ta saki tanayin kasa da idonta...

"Laa Daddy ni angle mommy Princess to kaifa?" Salamah dake back site tace, kama baki yayi momy na kunshe dariyar da taco mata, san yama manta, da Salamah idonta biyu....

Kallonta yayi ta madubi tana kiff da ido tana jiran amsar sa "Ni Daddy Mana"

"No Daddy prince dai" tace tana dariya suma dariyar sukayi suna mamakin wayau da surutu irin na Salamah.....





*Sabon salo, koda wane salo mukazo wannan karon?? Ni daku mubi a sannu mu gane🤩**




*_Maryam Abdul_*

inda rai ashe da rabo....Where stories live. Discover now