© *_HAKKIN MALLAKAR_*
® *_Maryam Abdul_*
_______________________
*_INDA RAI....._*
*_ASHE DA RABO..._*Wattpad me on @MaryamAbdul559
{ 27 }
Anyi shagalin biki sossai inda yaro yaci sunan Abbansu Hammad, Muhammad Sani zasu kirasa da Adeel, amaryar jego Ummitar da jaririnta Kai harma angonta sun barar da wanka a ranar na mutunci, su Salamah tun ranar da sukazo suke Mata tsokanar Wai dawowa gida wanka daga haihuwa irin na 'yan kebbi tayi a jahar wasu, dake itama da bakinta tace yo ai Koda kasa ta Bari indai zata haihu Dole ta dawo gida ta cika sunnar jaharta, hadda cewa yanzun ma kara mike kafa zatayi Dan sai tayi wata uku kafin ta koma, suko sukace sai su zuga Baban baby ya auro 'yar budurwarsa ya angance abinsa ita Kuma taita zaman jego, haka dai suke tayiwa juna tsiya hadda cewa take nasu lokacin na zuwa kamar gobe ne zataga yadda zasuyi ai, Dan duk aurar dasu zatayi ba zata Bari su koma ba saidai su hakura da karatun su sake jonawa a tare da ita tunda itama yanzu zata Fara, dake Bata jona ba tayi aure Kausar ce dai tace sai karatu.....
"Sis meke damunki?" Feenah fad'a tana tsareta da idanu, murmushi ta saki Wanda iya fatar baki ne kawai "me kika gani sis, nikam ba komai"
"Hmm sis nice fa nasanki sossai saidai in kina ganin bai dace in sani bane to is ok" tana gama fad'a ta yunkura domin tashi daga gadon" saurin rik'e Mata hannu tayi tare da mik'ewa tsaye tana fuskantar ta.
"Ba haka bane sis, kawai dai kwanakin ne Ina yawan mafarki da Mamana, sis inason in ganta ko sau d'aya ne a rayuwa I want see her, pls understand wlh badan na rasa komai ba, I really appreciate yours effort, kunyi min komai, kawai inaso na ganta ne even once in my life" sai hawaye sharr, kamar dama jira take...
"Subhanallah! sis pls stop it, I understand ur mood, inshallah zaku had'u, da Mama very soon, karka karaya kece fa Salamah Mai k'arfafa min a kowanne lokaci inshallah *inda Rai da Rabo* zaku had'u da Mama da Dady dama duka familynki gaba d'aya, komai ya kusa zuwa k'arshe da izinin Allah" sossai ta mayar Mata da hugging d'in ta da tayi, Wanda takejin kamar Yana rage Mata wasu abubuwa ne da takeji a rayuwar ta, lallai sadaukar wa abune Mai girman gaske ba Wanda zai fahimta sai Wanda yayi ta....
**********
"Ya Muhammad so soon zaka koma gaskiya kad'an jira Mana ayi kasan fa bamu wani Samu ishasshen lokaci a tare dakai ba, ka Kuma k'anwarka Nan itama tana son yayanta kusa da ita koba haka ba sis?" Murmushin yaken Nan dai data mayar a fuskarta shine take ci gaba dayi, Allah ya sani tana k'onuwa matuk'a idan tagansu a irin wannan yanayin saidai ba yadda zatayi kuma Bata isa ta Hana zuciyarta jin daci ba, tana rokon Allah ya yaye Mata Dan tabbas ta Riga tayi abinda ya dace a nata tunanin....
"Eh yayanah bamu samu ishasshen lokaci ba, why not ka Bari har bayan bikin Ya Saif please?" A hankali ya sauke kwayar idaniyarsa a kanta kallon tsaf yayi Mata cikin abinda baifi seconds ba, kafin ya mayar kan Feenah, mamalacin murmushin gefen baki ya saki, Wanda ya k'ara tunzura zuciyarta har takejin kamar da gayya yayi shi, da ba Dan tsoron darsa shakku a zukatan su ba da tabbas tabar wajen Dan gudun kada jarumtarta ta gaza..
"Waiku so suke ya fasa tafiya bayan har ya fito? Lallai bakusan aikin Yaya bane shiyasa ma mukam ai har mun saba" cewar Kausar,
"Jinsu nake kawai ai Bros ai tafiyarsa da dawowarsa kamar hab'o ne ba mamaki ya dawo auren Mai gida Saif" cewar Sadiq
"Wai tafiyar ce dai Muhammad? Kuko lafia kukayi kirko kirko haka kamar sojoji" sai lokacin ya Samu bakin magana...
"Da safen na Samu Kira daga oga urgent kinga sun tasa Ni gaba Wai karna tafi, ban sani ba ko in na rasa aikin zasu samar min da wani ne oho" dariya sukayi har Abba dake fitowa ganin yadda yake maganar da gaskiyarsa...
"Captain Muhammad M Sani, har an fito, takaddamar me ake anan?" Gaisuwa 'yan matan suka kwasa gurin abban dake basu gaisa ba...
"Abba ai bafa wani abun bane" yace cikin yanayinsa na rashin son magana tare da duban Sadiq "maza muje ku sauke ni ko?"
"Mami Ni zan wuce, sisters sai gani na gaba may be na dawo before ku koma watakil Kuma sai na kawo ziyara ta musamman malesia" murmushi kwance a kan fuskarsa ya kalleta ta gefen ido kallon da ya k'ara narkar Mata da zuciya Wanda ita kad'ai tasan ma'anarsa..
Jiki a sanyaye ta hau saman bayan sun gama masa fatan sauka lafia, wunin ranar a hakan ta wuni wata sukuku da ita, tun kafin a tuhumeta dalilin ta gaya musu zazzabi take ji, hakan yasa kowa yin shiru tare da Mata fatan samun sauki, washe gari Saif yazo d'aukar su, domin bikin shi nata matsowa saboda shirye-shirye..
Kafin su wuce Mami ta kirata d'akin ta.
"Salamah kinga rayuwa kala- kala a k'ananun shekarun ki, saidai Allah cikin ikonsa ya sadaki da iyayen riko na gari, ko baki fad'a ba, yanayin ki kad'ai ya tabbatar min da Yaya da Aunty sun r'ike ki dakyau, saidai duk da hakan gurbin uwa daban ne Salamah na sani, kina buk'atar Umm Ruman a wannan gabar kina buk'atar wacce zaki gayawa damuwarki, kina buk'atar uwa a matsayin ki na wacce batasan dad'in ta ba.
Ina Miki albishir komai yazo karshe inshallah, ada Banda dalilin zuwa gareta saboda baki tare Dani, nasan zataji dad'i innaje Amma zatafi farinciki inta ganki, nasa an bincika min Salamah mamanki Bata maiduguri yanzu, Bata ma k'asar Nan, ta auri Dan uwanta ya tafi da ita k'asar da yake aiki, Amma an bani tabbacin cikin shekarar Nan zasu dawo, kakanninki nanan da sauran 'yan uwan mahaifiyarki, Amma Ni Naga kamar gara a Bari su dawo d'in sai muje gaba d'aya munyi maganar da Yaya Koda zuwa Kun koma ne suka dawo inshallah zakuzo aje gaba d'aya ki k'ara hakuri kinji, shima dangin mahaifinki zamuje inshallah Amma abi komai a sannu" murmushi da dariya takeyi a tare da taji anji inda zata Samu mamanta, badan suga dokinta ba aida sun gaya Mata wace k'asa ce taje ta sameta, jinta take kamar ta taka kan jariri saboda farinciki, fad'awa jikin mami tare da rungume ta..
"Nagode sossai Mami, kece Mamata ta biyu, Momy haihuwata kawai tayi, Amma kune kuka reneni keda mom bazan manta wannan ba har abada Ina k'aunarku sossai"
"Shitt! Waya gaya Miki idan uwa tayi ma 'yarta Abu tana godia? Farinciki kawai nakeso kiyi, ki zama cikin aminci Salamah kinji?"
Da Kai ta amsa ta tare da k'ara k'ank'a meta.....
"Naso keda Muhammad ki kasance ma'aurata, Amma ko yanzu ina farinciki keda Nafisah duk daya ne a gareni, nidai fatana kuyi farinciki, Allah ya Baku farinciki a duk inda zaku tsinci kanku a rayuwa"
"Ameen" ta fad'a a sanyaye, Mami ta Mata fami a ranta, ko sunan Muhammad taji sai zuciyarta ta doka, Allah ne kad'ai yasan iya adadin sonda take masa, wani abun ne ya girmi wani......
A tare da Kausar suka wuce kasancewar suna cikin hutu, tunda sukaje basu zauna ba, kullum sai sun fita siye-siyen kayan bikin, shirye-shirye suke na gaske, sossai ta saki jikinta tare da danne damuwarta, takanji wani lokacin suna waya da Kausar ko Feenah, ko sau d'aya bai tab'a kiranta ba, saidai Bata nuna musu Dan kar su d'auka da matsala ne, hasalima Bata tsayawa in suna wayar, Akbil shine Wanda ta tsayar wa zuciyarta ta gudurta suna komawa zata bashi dama ya turo iyayensa, gara tayi auren kawai ta nisan ta dashi watakil zata manta dashi da soyayyar sa, hakan tasa a ranta shiyasa take kulasa sossai suna Kuma waya akai akai, duk da yayi mamakin canjawarta bai fad'a ba dai tunda shikam gaba ta kaishi hakurinsa bai Fadi a banza ba....
Pls
#Vote#
#Share#
#Comment#*_Maryam Abdul_*
YOU ARE READING
inda rai ashe da rabo....
Ficción GeneralIt's all about magic, sacrifice, pity, and true love