© *_HAKKIN MALLAKAR_*
® *_Maryam Abdul_*
_______________________
*_INDA RAI....._*
*_ASHE DA RABO..._*Wattpad me on @MaryamAbdul559
{ 6 }
"Ya Hammad"
"Uhm" kawai ya amsata ba tare daya d'ago ba Yana ci gaba da danne danne a k'aramin system d'in da babansa ya siyamai domin yin karatu, k'ara matsawa tai har gabansa ganin hankalinsa baya kanta...
"Mommy koh, Dana dameta akan cikinta ba, ba shine ba tace wai zasuje asibiti ita da dadynah, sukai cikin se abasu baby, to muma in mukayi aure cikina yayi kato ai zamuje asibiti mu amso baby koh?" Cikin mamaki ya d'ago Dara daran kwayoyin idanunsa ya zuba mata, duk da shima lokacin duk baifi 12 ba Amma Yana mamakin yawan surutu da wayon Salamah, Sam bata shayi ko tsoronsa komai yazo mata fadar abinta take Kai tsaye....
"Ko baka Sona ne ba zaka aureni ba" ta sake fad'a ganin yadda ya tsareta da idanu ba tare da yace komai ba, oh Allah ya fad'a a ransa...
"little cute, ai kinsan dai ba yanzu zakiyi aure ba ko?" Kai ta gyada masa alaman eh sannan tace..
"Amma in na zama doctor zaka aureni ai koh?"
Murmushin yanayin maganarta ya sakashi, Allah yama so shi sauran yaran basa gurin aida sai taja masa raini "inshallah bani da mata sai Salamah ta, yayi miki koh?"
"Eh yayi Ya Hammad"
"Oya! To maza jeki gun su Ummitar wasa ki barni nayi karatu"
"Ya Hammad in gayama Ummitar me kace?" Da kai yai mata alaman aa hakan yasa ta fice tana Dan tsalle Dan ta fahimci yau baijin firar....
*********
"Harun pls na rok'eka ka tsaya ka gayamin menayi maka? Ko me nake maka ka zabi ka hukuntani ta wadannan hanyoyin? Karka manta munyi wa juna alkawarin ba zamu ringa boyewa junan mu ba idan munyiwa juna laifi zamu zauna mu magance abin a tsakanin mu..
Pls ka tausaya min ka gayamin laifin da nai maka ka Dena cin abincina, ka dena zaman gida tare damu ka bamu lokacin ka, Harun har 'yarka yanzu ta fara complain akan Dadyn ta baya zama gida ya Dena kulata, Harun Dan Allah kar laifina ya shafeta, na rok'eka, yarinya ce ita Amma mai wayo sossai, Dan Allah ka zauna mu magance koma meye matsalar a tsakanin mu, karka manta Harun, banda kowa a wannan garin bayan Kai sai Salamah da wannan cikin, duk fad'in Sokoto da zagayenta ku kad'ai ne zan Kira nawa, sai abokan arzikin kirki da nake da, Dan Allah Harun karka juyan baya"
Sossai maganganunta suka dakesa kuma ta matuk'ar bashi tausayi, to Amma ko zata kashesa bazai ce ga laifi d'aya da tayi masa ba, hasalima in laifin ne shine yayi mata, saidai a yadda yakejin Sofie a ransa yanzu tabbas komai ya shirya hakura dashi ciki harda ita kanta kak har d'iyan da yake matuk'ar k'auna....
"Ina sauri yanzu, inna dawo mayi maganar" iya ansar da ya bata kenan, ya fice daga d'akin ya barta zaune tana zubar da hawayen tausayin kanta da kanta, lallai al'amarin aure dole sai ankai zuciya nesa, da yin hakuri sossai...
Yanzu towa zata tunkara wa zata shawarta akan wannan matsalar, mamarta aa Mama tayi nisa xan tayar mata da hankali ne kawai, yayyina fa? Suma duk tashin hankalin ne tunda gari yayi nisa, to yan uwansa fa? Kamar nakai k'aransa ne to ai...
"Maman Sadiq" itace ta fad'a a fili, dak'yar ta iya tashi saboda yadda cikin ya tsufa ya k'ara nauyi, hijab kawai ta saka ta ture gidan, shara ta sameta tanayi yanayin ta kad'ai ta kalla bayan sun gaisa tasan ba lafia kodai haihuwa ce ko wata damuwar wacce tun ba yau ba take ganinta tare da ita....
"Maman Salamah mu shiga ciki koh" ba musu ta bita, duk abinda ya kamata ta gaya mata domin ta bata shawara shi ta gaya mata game da zamansu na yanzu da mijin nata Wanda ya canja salo...
Jim tayi na d'an lokaci "Maman Salamah, wannan al'amarin Yana buk'atar Addu'a sossai, sannan kema kiyi tunani ko kinyi masa wani laifi ne kamar yadda kika bukaci sani daga garesa, kiyi hakuri ki k'ara zaman aure tabbas zamane na hakuri sossai, ki jira shi ya dawo kamar yadda fadan ki koma tuntub'arsa da zancen, pls ki rage damuwar nan kodon lafiyarki Dana jaririnki, inshaa Allah komai zai daidaita kinji" hakanan taita Bata shawarwari tana janta da fira cikin hikima da azanci har tayi nasarar raba da wasu daga cikin damuwarta....
Nan gidan ta wuni har su Salamah suka dawo anan sukaci abinci su duka da yake batayi ba ita tana gidan, ba ita tabar gidan ba sai bayan la'asar bayan yaran sun wuce islamiyya...
Saida tayi kokari ta samu abinda ta dafa masa duk da Bata da tabbacin zaici, yau ma sai bayan isha ya shigo tana kuwa zaune falo, tana jiransa dan kar ma yazo ya shige dakinsa ba tare daya nemeta ba kamar yadda ya saba yanzu....
Kallo-kallo suka shiga yiwa juna, kafin ta mik'e dak'yar ta isa gunsa tana masa sannu da zuwa tare da mik'a hannu domin amsar jakar tasa, janye jakarsa yayi tare da fad'in "thanks" can cikin mak'oshi yana wani cin magani...
Ba tare data nuna jin haushi ba tace "ga abinci can a dinning is ready" yatsina fuska yayi kafin yace "am full" sossai abun ya soketa Amma ta dake tace "to naje na had'a maka ruwan wanka?"
Shima cikin basarwa yace aa zaiyi da kansa, tana kallo ya wuce ta gabanta, anan taci gaba da zama shiru- shiru bai fito ba, damarta ma Salamah tayi bacci tuni, to an wuni jiganiya sai bacci, tashi tayi ta bishi Dan gaskiya yau dole ne suyita ta k'are tasan matsayinta garesa...
A mike ta samesa Yana waya k'asa k'asa yana ta nishadinsa Yana ganinta ya yanke wayar tare da dinke fuskar kamar bashi dai ba Harun dinnan nata Mai matuk'ar k'aunarta...
"Wai nikam Umm Ruman ba zaki barni na huta bane ba kam" yace cikin daga murya, idanu ta zuba masa kafin ta samu k'arasawa bakin gadon....
Kan guiwuwinta ta zube, tare da d'ora hannayenta bakin gadon "Dan Allah Harun na rokeka karka min haka, karka manta soyayya da yadda da aminci sukasa na baro iyayena 'yan uwana, dangina nayi nisa dasu na biyoka nan bayan ka amshi amanata a hannunsu pls karka juyamin baya a daidai lokacin da nafi buk'atar ka fiye da kowane lokacin Dan Allah Harun, ka gayamin menayi maka...."
Jiyai kamar yaje ya rungumeta ya bata hakuri ya manta da wata Sofie da tazo daga sama take neman tarwatsa masa rayuwa, Amma kash sihiri gaskiyar mai shi, sossai yakejin zafi da rad'ad'in sonta a ransa yake gudun bacin ranta fiye da nasa...
"Ke nifa ba abinda kikamin, ke bari ma kiji nifa aurema zanyi Dan da sati biyu...""
"Au..au..aure Haaa..haaa...haaaruuun!! Wayyo Allah na! Wayyo cikinah" nan take ta zube gurin warwas kamar gawa Amma ma yasa Bata cikin ta fad'i ba hannunta kafe Wanda take nunasa dashi.....
Kicin kid'ima da tashin hankalin da baisan ya iya ba ya wulluto daga gadon, sai gabanta ya gansa Yana jijjigata tare kwalla mata kira, cike da rud'ewa, ganin tabbas ba nunfashi tattare da ita ya sakashi sunkutar ta, cike da rud'ewa ya fice Yana kuka shima wiwi kamar mace, Yana ci gaba da Kiran sunanta .............
*_Maryam Abdul_*
YOU ARE READING
inda rai ashe da rabo....
Narrativa generaleIt's all about magic, sacrifice, pity, and true love