© *_HAKKIN MALLAKAR_* ® *_Maryam Abdul_* _______________________ *_INDA RAI

465 30 0
                                    

© *_HAKKIN MALLAKAR_*

® *_Maryam Abdul_*

_______________________

*_INDA RAI....._*
              *_ASHE DA RABO..._*

Wattpad me on @MaryamAbdul559

{ 26 }



*RAYUWA BATASAN INDA AJALINTA YAKE BA, ABU DA KAWAI MUKA SANI KUMA MUKA YARDA DASHI SHINE, A KO INA AJALINKA/KI YAKE SAI MUN ISKO SHI KODAI KAKAI KANKA KO A KAIKA DAYAN BIYU NE, ALLAH YASA MU CIKA DA IMANI, ALLAH YASA MU GAMA DA DUNIYA LAFIA AMEEN🤲🏼*






"Salamah ce fa" zuciyarsa ke gaya masa, yatsu biyu ya saka a goshinsa Yana shafawa kamar Mai liliya gurin da yaji ciwo, jijiyoyin kansa a mimmik'e alaman ransa a matuk'ar bace yake, sossai yake tausar fushinsa zuciyarsa na k'ara jaddada masa wa yake tare da ita....

"Am sorry! Am out of my control" cikin sanyin muryar da kana jiyo rauninsa a ciki yayi maganar tabbas itace, itace weak point d'insa, Mami kad'ai ce yai iya d'aga ma kafa sai ita Kuma....

Cikin rawar muryar da kanaji kiris take jira ta fashe da kuka duk jirkinta mazari yake, ba abinda take maimaitawa a ranta bayan innalillahi wa'innah ilairrajiun lahaula wala kuwwati illah, wannan shine ka koshi ga kuma kwanan yunwa, yau fa itace tare da Ya Hammad d'inta da suka sadaukar da tsawon lokutan su na jiran wannan ranar, suka rufe zukatansu kuf ba tare da baiwa kowa dama ba, gafa dama ta kasancewar su tare saidai k'addara ta Riga fata, *Feenah ce* wacce kullum take sadaukar da farincikinta saboda ita tayi farinciki, take sadaukar da lokutanta saboda ita, for d first time da takejin zatayi Mata sadaukar wa, Dole ne, tabbas Dole ta danne dole ta hak'ura da Hammad Dan farincikin Feenah kawai, sun Mata komai ita ahalinta ba zataso Koda zuciyarta ta zargeta da rashin sanin halacci ba, tabbas ita 'yar halak ce Kuma tasan halacci.....

"Am sorry ya Hammad ba Dole ne duk abinda mukeso mu sameshi ba, nasan wacece Nafisah ban tashi tare da ita ba, inshallah ko Momy mahaifiyarta Bata fini sanin Feenah ba, Feenah mutum ce cikakkiya, tasha sadaukar min da farinciki, lokuta, dama uwa uba muna shearing happiness and tears a tare, da tasan alakarmu Koda wasa ba zata tab'a maka kallon so ba, Bata masaniya Nima kuma bansan meyasa banga yama Koda itace ba, Tasha gayamin zurfin cikina wataran zai iya zamomin illah, nasan komai game da ita, Bata tab'a so ba sai a kanka, kuma sonka take bada wasa ba, alkawari nane ka taimakeni na cikawa Feenah wannan alkawarin duk da cewa na kasa cika naka pls ka yafemin Yayana, help me out" kneeli down tayi a gabansa tare da hade duka hannayenta alamar begging...

"Pls have a site" yace da sauri tare da saurin kawar da idonsa akan fuskarta, zama tayi kamar yadda ya buk'ata....

Itakam haka tata k'addarar take daga wannan sai wannan tun kuruciyarta har girma, a shekara 22 da take da inshallah 6 dannan na k'arshe ne kawai zata Kira tasan wani Abu dad'in rayuwa a tare da kawunsa, tunawa yayi da maganar mamanta _Hammad ka kula da Salamah da sauran kannenta, Dan Allah ka tsaya Mata iya iyawarka_

"Nafisah kike so naso ko? Kuma ita kikeso na aura?" Da sauri ta amsa masa dakai..

"Kin tabbatar hakan zai sakaki farinciki Koh?" Nan ma da sauri ta amsa masa, tana Mai k'ak'alo murmushin da ko iya lebben bai gama wadatarwa ba.

"Shikenan na amince Salamah, duk abinda kikeso a rayuwa a shirye nake Dana yi Miki shi, ma'ana hadda bayar da rayuwa da kanta domin ke kawai, karki manta domin ke kawai kuma *inda Rai ba'a core tsammanin samun rabo*

*Inda Rai da Rabo* ya Hammad" cikin hantsari tabar gurin ba tare data sake waigawa ba, shi kuma bin resting chair din kawai yayi Yana tunanin yadda rayuwa ke safe da sauye sauye kowacce Rana da nata sabon al'amarin take zuwa "hazbiyallahu wa ni'imal wakheel" ya furta a fili...


********

"Twiny ina kika shige ga babyn ya bud'e ido inata nemanki kizo ki d'auke sa foton da kike ce, kinga ni ko ya bud'e ido" k'awata fuskarta tayi da murmushi saboda gudun zargi....

"Kai so cute Fee inason yara sossai...."

"Gashi kuma kina tsoron kula iyayen yaran ba, am just wonder yadda kikeson yara Amma bakyason kula samari bare har azo maganar aure...wait meya sameki a ido, kuka kikayi?"

"Kai twin rigima, irin wannan ranar farincikin niko Mai zai sakani kuka, kawai fa naje can ne shan fresh air Abu ya fad'an a ido" cikin fuskar tausayi ta matsota tana k'okarin duba idon.....

"Opp! Nafa fitar dashi ma, muje kawai gurin su Ummitar ki turon photon nayi status"

A tare suka jera kamar dai kullum uwa 'yan biyu Feenah na fad'in "ai Ina tare da ita tun dazun tana gayamin kuruciyarku Ashe dai kema kin tab'a rashin ji, kin Kuma takurawa my crush d'ina, ur a d best d'in shi anya ma ba sonki yake ba?" Dam k'irjinta ya buga, saurin basar wa tayi tare da tabe baki..

"Hmm! Lallai ma bakisan waye ya Hammad ba, kema da kika dauka ai kinada aiki a gabanki zakiyi fama da zuciya" murmushi ta saki

"Whatever inason kayana a duk yadda yake"

"Kinji zaki iya ne so ga fili ga Mai doki" cikin k'ok'arin batar da hankalin Nafisah akan maganar ta, ta farko ne ya sakata biye Mata Amma ita kad'ai tasan me take feeling inside...

"Niko Ummitar tace shegen surutun tsiya ne dake da jan magana, Amma yanzu duk babu why? Kin koma wata marason magana Kuma a yanzu"

"Sis! Yanayi ne dake sassauya mutum" Nan fa suka shiga suka Samu Kausar da Ummitar aka dasa wata firar ranar sunkai pass 1basuyi bacci ba sai tuna baya ake abin dariya ayi, na kuka a yi alhini, na takaici da shirme da shirita shima a dara ( kuruciya kenan Mai Dadi da hausa😁)

Mom da Abba da Nuriyya, Saif, Nuren ne suka koma Abuja anan aka bar Salamah da Feenah akan sai sunzo suna daga Nan sai su koma tare su Fara Shirin zuwa birni domin Fara bikin Ya Saif......

A tsawon satinnan duk wata hanya da zata kad'aita ta da ya Hammad ta toshe ta shima Kuma daya fahimceta sai ya nisan cetan kamar yadda yaga tana buri, saidai abun iya sune ya shafa Dan in Ana a taro sossai take sake jikinta ayi fira kamar ma ba komai, Feenah Kam sossai take k'okarin shisshige masa, ita ke kaimai abincin safe, rana, dare har fira zuwa masa take Wanda ya yanjo hankalin yan gidan akai, ba laifi shima yana sake Mata kamar ma bashi d'in ba a yadda takejin labarin sa(yarinya alfarma kike ci)

Lokacin da Mami ta tare shi da maganar Salamah Dan ita kaidai ce tasan meye a zuciyarsa game da ita ce Mata yayi "Mami nisan mu ya saka zuciyar Salamah ta zama ba tawa ba na hakura da ita, Nafeesa zan aura" duk da zuciyarta na gaya Mata wani Abun ba daidai bane a wani gurin hakan bai hanata yi musu fatan alkhairi ba, Dan tasan son d'anta kema Salamah ya wuce ya sallamasa da sauki haka, saidai koma meye tana fatar hakan ya kasance mafi alkhairi a garesu, da Nafisah da Salamah duk 'ya'yanta ne Kuma tana sonsu gaba d'ayansu.....

A wannan tsakanin iya jarumta da dauriya Salamah ta nuna shi, ita kad'ai ke konuwarta a zuciyarta taking yadda kowa yasan me take ciki, da safe zuwa marece zaka ganta faran faran anata wasa da nishadi a tare sai zuwa dare ne lokacin da kowa yace tunanin shine lokacin hutunsa lokacin ne take kulle kanta a toilet ta saki shawa tayi kukanta Mai isarta, Dan shi kad'ai ne ke rage Mata nauyin da zuciyarta tayi, Bata tab'a jin rashin uwa sai zame Mata barazana ba kamar wannan lokacin inama ta ganta ta kwanta a k'afafunta ta gaya Mata damuwarta Koda ba zata samar Mata mafita ta shafa kanta kawai ta gaya Mata komai zaiyi dai-dai...

Daren yakan kare ne da kuka da tsayuwar dare tana gayama Allah damuwarta tana rokon ya had'a fuskarta da mahaifiyarta Koda sau d'aya ne a rayuwa......





*Lafia uwar jiki babu Mai fushi dake, kudai k'ara hakuri lafiyar Nan dai tamin karanci pls ku sani a addu'o'inku koda sau d'aya ne nagode*👏🏼





Pls

#vote#
#share#
#comment#



*_Maryam Abdul_*

inda rai ashe da rabo....Where stories live. Discover now