© *_HAKKIN MALLAKAR_*
® *_Maryam Abdul_*
_______________________
*_INDA RAI....._*
*_ASHE DA RABO..._*Wattpad me on @MaryamAbdul559
{ 37 }
__Jikinsu ya Gama yin sanyi dajin labarin abubuwan da suka faru, tabbas sunga rayuwa, Kuma sun jarabtu su dukansu ba Wanda bai tab'u ba, k'addarorinsu nada girma da fad'i sun kwace musu wani Abu sun Basu wani abun, sunyi kuka aciki haka zalika sun dara duk a cikin, idan akwai Wanda k'addarar sa tafi zafi a cikin su baifi Harun ba, k'addarar sa ta kwace masa komai nasa, adalcin da zaice k'addara ta masa shine dawo masa da yaransa, su duka cikin aminci....
"Kiyafemin Ummu Ruman!! Alhakinki bazai......"
"Aa Abban Salamah, k'addarar mu ce a hakan, bamu isa muyi jayajja da ita ba" tayi saurin katse sa, ba zatace ga ainihin abinda takeji game da Harun ba a yanzu, Abu d'aya ta sani tausayinsa ya lullub'eta, k'addarar sa ta tab'a ta fiye da tunani..
"Mamanah ban kasance uban da zakiyi alfahari dashi ba agare...,"
"Aa Dady ba wani uba daya Kai ka duk fad'in duniyar Nan, duk da ban samu soyayyar ka a lokacin zaman mu ba, ina hango k'auna ta a tare dakai, komai da ya faru ya faru ne a dalilin k'addarar mu, bamu isa mu canja ba, saidai zamu iya fahimta mu Kuma yafe, Kaine uban da yafi kowanne uba aduk fad'in duniya" murmushi sossai ya bayyana akan fuskarsa, duk yasan ta fad'a ne kawai domin ta sanya shi farinciki yaji shima uba ne, Kuma tabbas yaji, Dan yamutsa fuska yayi tare da dukan kansa da hannayensa ya kalli Abdul...
"Wane irin shashashan uba ne zai manta jaririn yaron sa? Nikam da nine a matsayin ka Little bazan iya yafewa ba" tasowa yay tare da zuwa gabansa da duka hannayensa biyu ya rungume sa, yanajin wani yanayi na daban, a tare suka sauke ajiyar zuciya "Baba!" Ya fad'a cikin kunnensa....
A sanyaye kwalla na cika masa ido ya jinjina masa Kai, yanajin yadda sassa daban daban na zuciyarsa ke bud'ewa suna karb'ar sabon yanayin Ashe Yana da sauran jindad'i bayan ya dawo hayyacinsa kamar haka....
"Naso ace dakai na bud'e ido na rayu dakai, k'addara ta Hana wannan damar" kallon Aliyu yay, murmushi aliyun ya sakar Masa shima ya mayar Masa da martani...
"Abu ya hanani rashinka Baba! Ya maye duka gurabun da ka Bari, saidai still naka nanan wanda ka cike a yanzu" dariya ya saki..
"Wayau ko lil?" Dariya sukayi a tare...
"K'aunar ku agaremu daban ce Alhaji Sani, Maryam bansan me zance ba, ban kasance Dan uwa/mak'oci na gari agareku ba, kunyimin abunda ko jini d'aya muke daku iyakar abunda zakuyi kenan nagode, nagode sossai, Dan Allah kuyafemin ban aikata muku.."
"Aa Harun ko Kaine a matsayin mu zaka yi mana, kanada kirki Harun k'addara ce! kaddarace tazo da hakan, ban rik'e ka a raina Harun, Allah ya yafemu Baki d'aya" Abban su ya Hammad ya fad'a....
Mami ya kalla, murmushi tayi "Baban Salamah komai na tafe ne bisa k'addarar sa, Duka yaranmu ne su abinda ya Kamata ne mukayi, bakada buk'atar godiya" Yama kasa cewa komai tabbas girma sai Dan girma....
Cikin jin nauyi Gwaggo tace "kuyi hak'ura d'iyata Rumana, muna Nan muna ta zuciya da Haruna bamu duba ke da yara Ashe abubuwan sun rinc'abe fiye da misali, ki yafe Mana 'yarga Dan Allah.." cikin sauri tace
"Dan Allah Inna ki Dena fatar haka, Nima ai da nawa kuskuren, ya Kamata nazo na sanar daku kafin na wuce, kuna hakkin ku sani, Amma jin haushin abinda ya faru zuciya ta debeni nayi tafiyata, ku yafeni Nima"
YOU ARE READING
inda rai ashe da rabo....
General FictionIt's all about magic, sacrifice, pity, and true love