© *_HAKKIN MALLAKAR_*
® *_Maryam Abdul_*
_______________________
*_INDA RAI....._*
*_ASHE DA RABO..._*Wattpad me on @MaryamAbdul559
{ 43 }
"Muna fad'a ne? Nayi laifi ne my love?" Ya sake fad'a mata cikin kunnenta da muryar da bata tab'a sanin yanada ita, mamakin da 'yar kunya yanayin nasu ya sakata, Ashe haka yake take ta tambayar kanta....
Muryar mc taji Yana tambayar Ina tsuntsayen soyayyar ne suka buya kodai hadda amaryar ta b'ata ne, saboda sune kawai Basu bayyana ba.....
"Ya Hammad mana!" Tace cike da shagwab'a, murmushi Mai sauti ya saki "oya muje" hannunsa ta kamo yana biye da ita suka bayyana a filin Nan fa aka hau tafi da shewa, tare da ci gaba da gudanar da taron cikin tsari da wayewa, haka taron ya watse mashaa Allah, kowa cike ka ganu cike da farinciki, gwanin sha'awa...
Abu ne fa na masu shi, cikin k'ank'anin lokaci aka gama komai na shirye shiryen tafiyarsu kasashen guda uku, tuni flight dinsu, ya zama ready, tafiyace ta matasa kawai, ba iyaye a ciki Dan sunce sudai sun gama Mai wuyar a barsu su huta, Sossai mutanen Hammad suka karramashi domin sukutun suka bashi jirgi a yakaisu duk inda sukeso tare da bashi a month a matsayin nasu gudummuwar kasancewar sa jajirtacce Mai gaskiya da Kuma sanin makamar aiki, hakan ba k'aramin dad'i yai Masa ba, Dan sun karramashi ta yadda bai tsammata ba...
Haka aka zab'i mutum biyu biyu daga kowanne b'angaren inka cire su Yaya saif, Nuriyya, Minal, Ummitar, Abdul dasu Afiya su masu permanent sit ne tare da angaye da amaren..
Har airport d'in Abuja da zasu tashi iyayen su sukayi musu rakiya cike da fatan zuwa da dawowa lafia, tare fatan alkhairi, hakan jirgin nasu ya lula tare da keta hazo kowanne Zuciyarsa d'auke da mabanbantan emotions..
Wonder should never end, a tayar jirgi ta gaba na hango members of marraha home of peace, cike da mamaki nake tambayar su meyasa basu shiga cikin jirgin ba, bud'ar bakin ta baban Nana sai cewa tai "Dan muga gari gari ma ya gammu sannan mu shaki iska yadda mukeso" dariyar kawai nai Dan nasan wannan shawarar kishiyas ne da Billy in ma akai wasa baza'abar umm annur a baya ba, heart u all marraha u peoples mean a lot to me....
Ban Gama mamaki ba saiga matan kirki a fiffiken jirgin sun mak'ale, indo uwar Billy sai kokuwa da zanenta da iska ke kwasa take, asiya matar Dr kam ta rik'e fiffiken Gam uwar ranta, er balki Kam tayi tsuru sai sakin ido take, oh! Sorry aunt sumee, kekam da alama 'yar gari ce irin wannan bajewar kamar kin samu kujerar falonki? Lol.
Can Kuma saiga duniyar makaranta a d'ayan tayar jirgin ta baya, wato dai mutanen Salamah yan gani kasheninta Nafisa da aysher sun mak'ale tayar irin bafa za'a barmu a baya ba tare da sauran masu goyon bayan tafiyar, cike da mamaki nake kallon my sweet sis jannart lamido tare da cewa hadda ke sis? Washe Baki tai "naki wasa ne aunt kin ma ga cute mubee gefe na" abun azimun ne nace tare da daga musu hannu nadai San akwai kura....hhhhhhhhh love you all my true fans...
Journey mercies d brides nd grooms ✈️
************
India suka Fara yiwa tsinke a gidan su Zakiyya na k'asar suka sauka dake babban gida ne ba matsala kowa a wadace angaye fa suna zuba ido suka an ware musu dak'una suda amaren su sai sukaga sab'anin haka, Dan kuwa tun can su Mami sun jaddada ma su Nuriyya dake ma hadda aunt tome k'anwar umm Ruman, kar a yadda abar su keb'ewa da angwayen na minti goma, aiko shi akayi akabar angwaye da buhuhuwan takaici, Nuren sai Taki yaketa zubawa sadiq na mishi dariya, Hammad dai gefe yaja tare da Jan girmansa sai Jan Akbil fira yake kamar ma ba abinda ke damunsa, Amma Kam da za'a tona zuciyarsa ji yake kamar ya kurma ihu...
Sun Sha mamakin event d'in ta friends d'in na Zak's suka tsara, ya matuk'ar burgesu Dan hatta kayan da suka saka sune suka d'auki nauyi, kwalliyar had'addun sari da sukasha design mashaa Allah, necklace har da kafa kamar wasu India haka suka fito, mazajen kuma fakistan masu bujen wandon Nan har da rawunansu irin dai na India su Hammad cikin buje... lol
Gaskiya taron ya k'ayatar Dan kuwa sun baje musu hajar al'adar India rawa Kam ba wacce ba'ayi ba yo dama India ga rawa ga Waka aiko dai sun gajije Dan kowanne su sanda ya taka tasa rawar hadda masu buje.....
Kwanansu 3 suka d'aga zuwa malesia, Nan ma a gidan Dady suka sauka still dai Bata canja Zane ba Dan kuwa d'aki d'aya aka warema angayen kamar India dai Nuren dai har ya sallama tunda ya fahimci akwai k'eta a lamarin abinda ya fad'awa Nuriyya taita mishi dariya...
Event d'in da aka had'a musu malesia event ne na Musamman domin kuwa k'aton hall d'in makarantar aka k'awata sossai, Drama suka had'a musu da k'ananun yara yadda likitoci ke wahala akan karatun su da yadda suke saving life cikin asibitoci sunyi akan case din tiyata da Kuma na emergency yaran ba k'aramin k'okari sukai ba duk da kana gani kasan sun horu kafin zuwar ranar Amma duk da haka sun trying sossai Dan ba Wanda ya wuce ten years a ciki saidai kasa da haka, gasu sanye cikin suit da lab coat har da glasses gwanin birgewa 'yan matan hadda mini hijab d'insa...
Tsabar farinciki ciki Salamah hadda hawayen ta, yaran sun matuk'ar burgeta tare da tsaya Mata a rai, ta Kuma ji dad'i sossai yadda makarantar ta karramasu haka, Hammad Kam ji yake kamar yay hugging d'inta a gurin lokacin da taje tana speak d'in godiya da yabawa yaran yadda take fitarta turancinta fluency, gift suka bawa yaran Wanda sukazo dashi domin taron itada Akbil da akayi dominsu.....
Bayan sun Gama nasu ne Suma b'angaren law suka fito sukayi nasu inda yaran suka fatata a kotu a matsayin su na barristers, hohoho zanso kuga farincikin feenah a wannan lokacin itama dai mutuniyar hadda kukanta, itama tayi godia da Basu gifts kafin suma school d'in ta kirasu ta gabatar musu da gift d'inta garesu tare da musu fatan zaman lfia Mai d'orewa...
Daga Nan Kuwait suka lula, acan kam ba'a cewa komai, Dan larabawan sunyi musu karamci iya karamci, a ranar Suma su Mami, Ummi, da Hajia Inna suka d'ira a Kuwait da sauran mutum biyu a dangin mom, domin idan an Gama event su sada Feenah da nata d'akin miji.....
Event kam anyi yakai uku hadda su Shan black tea, Suma ukun an tak'aita ne tun da su Mami sunce ba Zama sukazo ba, haka suka d'unkula Feenah zuwa katafaren gidanta Mai Kama da k'aramar Villa, bayan k'ara d'anka amanarta gurin surukan nata masu karamci da suke saka ran 'yarsu ba zata wulakanta a hannun su ba, sun kuwa tabbatar musu zasuyi iya k'okarin su gurin rik'e ta da Amana....
Yau ko ake daru Dan kuwa Feenah da Salamah k'ank'ame juna sukai tamau suna rurar kuka da duka gaskiyar su, ba Wanda basu saka hawaye ba a gurin domin kuwa yadda ma suke kukan abin tausayi ne Mai cike da kewar juna da zasuyi, dama sabo shi akewa kuka....
Dak'yar Mami ta banbaro Salamah jikin Feenah Ummi kuwa da su Gwaggo ajidde ciki sukayi da Feenah suna da d'a lallashinta, hakan wasu daga cikin yan uwan Akbil Suma suka zagayeta suna Bata Baki cikin harshen turanci tunda bajin larabci take ba sossai Suma Kuma basajin hausa Sam, akwai Zama kenan kafin a saba, wannan ya bawa su Ummi damar zamewa ba tare da ta sani ba saida kawai ta shafi taga ba kowa nata a gun, Nan fa sabon kuka ya k'aru, har zuciyarta ta Fara gaya Mata tayi kuskuren auren nesa inda Bata da kowa, da sauri Tai saurin kawar da mummunan tunanin b'angaren na zuciyarta ta Karb'i na Wanda ke gayamata ubangiji na tare da ita ko'ina.....
Salamah Kam har suka shiga jirgi Bata Dena kukan ba idanuwanta sunji suntun, tare da jin jajir tsabar kuka tun ana rarrashinta har an zuba Mata idanu, Nuriyya ke fad'in a barta ta koka shak'uwar su Bata wasa bace....
Hammad har cikin tsokarsa yakejin kukan nata, kasancewar su Ummi a tare dasu ne kad'ai yai mishi katanga da zuwa ya rungumeta ya rarrasheta yadda ya tabbatar dole zata Dena kukan.........
*Hakurin Nan dai da kuka Saba my friends inshaa Allah, mun kusa dama kunsan aski in yazo gaban goshi yafi zafi* 😅
Pls
#Vote#
#Share#
#comment#*_Maryam Abdul_*
YOU ARE READING
inda rai ashe da rabo....
General FictionIt's all about magic, sacrifice, pity, and true love