© *_HAKKIN MALLAKAR_*
® *_Maryam Abdul_*
_______________________
*_INDA RAI....._*
*_ASHE DA RABO..._*Wattpad me on @MaryamAbdul559
{ 21 }
"Yanzu Bala hakan zaku zuba ido tsawon shekarun ba amo ba labari Haruna? Yanzu fissbillahi shikenan muda shi Kuma, idan shi ya manta hakki da girman zumunci muma sai mu biye masa har rayuwa ta k'are, shikenan nasa zumuncin damu ya yanke, kunfa je makaranta babu jahili cikin mu musan hukunci da girman laifin datse zumunci, kar ku duba maganganunsa ki biye masa muje kodon yara kada a datse musu zumuncin dangin ubansu, Ni jiki yayi nauyi Amma ku Dan Allah kuje ku binciko Mana shi Dan Allah" tsohuwar take fad'a cike da jimami wacce tsufa yaci k'arfin ta ga alamun ciwo Kuma...
"Gwaggo wallahi Nima abun na damuna sossai Kuma ba k'in zuwa ne mukayi ba nida yan uwana, a da kam min dau zafi kamar yadda yace bamu bashi mun barshi a hakan, Dan idan muka nace da bibiyar sa, zai iya d'auka ko don akan wani Abu dake a hannun sa ne, Amma daga baya muka sake shawara ganin yadda shekaru suka ja bashi ba iyalinsa musamman ma ita Rumana yadda take da son ganin had'in kanmu, shiyasa naje cikin garin Amma abin takaici na Samu labarin ya bar unguwar gaba d'aya Kuma ba Wanda yasan inda ya koma, bayan na Samu labarin rabuwar da yayi da Rumana abin ba dad'i Wai fa tun farkon aurensa da amaryar sa, Amma bamu da labari, hankali ya matuk'ar tashi to fa shine sanda na dawo da zancen Kuma keko jikinki ya tashi ya rikice kinji dalilin da yasa bamu tattauna zancen ba" salati tsohuwar ta shiga yi tare da tafa hannaye fuskarta d'auke da tashin hankali...
"Yanzu abunda ya faru kenan, to kun gani ko ai kunga illar watsar da zumunci, yanzu duka hallaci da k'auna da yarinyar nan ta nunawa Haruna ya iya rabuwa da ita, Amma gaskiya bai kyauta Mana ba, to yanzu Bala kana nufin ba'asan takamammen ina Harunan yake ba yanzu kenan?"
"Wlh gwaggo haka ne"
"Oh ni Tsaibi, yanzu da Yaya da innarku suna da rayuwa ina tabbacin ba zasu tab'a Bari irin wannan abun ya faru ba, Bala mu duka mu dage da Addu'a akan al'amarin Haruna tunda Allah ya kaddaro masa auren irin wancen matar ba abinda ba zata iya ba, duk nasan rashin kulawa irin ta Haruna dabi'un kahirrai sun shigeshi Amma abin yayi yawa, mu dage da Addu'a da yardar Allah Haruna da kansa zai dawo"
"Inshallah gwaggo zamu ci gaba da Addu'a allah ya dawo Mana dashi lafia tare da iyallansa! Ni yaran ma bansan ya akayi dasu ba, ko suna tare dashi ne Amma naji sunce lallai macen tana nan Dan da ita sukabar unguwar kila k'aramin nacan tare da ita Rumana, lallai Dole muyi shiri nida Harisu da Dahiru muje can Mai dugurin mu basu hakurin abunda ya faru mu kuma sanar dasu rashin saninmu akan al'amarin tare da dubo yaron da yardar Allah...."
"Hakan da zakuyi shine daidai, Allah ya baku ladar da ke ciki yayi muku albarka gaba daya, baiwar Allah Salamatu ta nacan bamusan wace irin rayuwa take yi ba da matar ubanta!"
"Allah dai ya bayyana muna su Gwaggo"
"Ameen kaidai D'an ga ameen ameen".....
*******
Cikin sati d'aya duk wani shirye-shiryen da ya kamata Safiyya tayi shi duk wani gida da fili da duk wata k'addara da Harun ya mallaka mota da sauransu duk ta sayar ta kammala kud'in ta zuba a account, kaso Mai yawa ta d'ibarwa Zaharadden a cewarta ya samu na r'ike kansa idan ya koma gida tunda haka ya zab'a, k'in karba yayi yace shi namiji ne zai tashi ya nema na kansa da k'arfinsa, zai Fara Mata mitar tasa a cewar ta, ta dakatar dashi tare da nuna mishi hanya tace ya gaida Umma....
Harun dai kamar rakumi da akala haka Sofie ta kwasheshi sai kano bayan ta Kama musu gida Wanda zasu zauna, kullum Yana gida kamar macce to aikinsa na sokoto ya baro, ita kuma gogar ganin kud'ad'en a hannunta Nan fa ta had'u da manyan Mata yan duniya irinta suka sakata a layi ta fara fita kasashen k'etare ta fara business ka'in da na'in, yau tana waccen kasar gobe tana wannan shiko hotihon Yana nan gida sai ya ganta kawai, rayuwar sa gata Nan dai za'ace shidai kawai Yana raye a matsayin mutum ne Amma baida alkibla baisan me duniya take ciki ba, ganin shirun zaiyi masa yawa ne yasa Sofie Kama masa shago a kantin kware ya ta zuba kaya yake zaunawa Amma fa duk wani cinikin kudin na hannunta itace boss d'in....
Tauraruwarta sai haskaka take, maza manyan mutane kuwa ta ko'ina Hari suke kawo mata Dan su basu ma d'auka tana da aure ba, badan soyayyar da take ma Harun ba aida tuni ta barshi ta bi wani hamshakin Dan ta K'ara suna...
Kwanaki sai tafiya suke suna zama satittika, suko suna juyewa zuwa watanni, rayuwar Harun dai na Nan a yadda take ba wani canji ko ci gaba, a hakan ne wata Rana hanyarsa ta dawowa daga kasuwa ya had'u da mummunan hatsarin mota Wanda yayi sandiyyar karyewarsa a k'afafunsa da hannaye gaba d'aya, saida ya share wata biyar a asibiti kafin a mayar dashi gida komai sai anyi masa, Sofie dama kacokam ta d'auki Mai kula dashi Dan tace Sam ba aikinta bane aikin wahalar kula dashi iyakarta taje ta dubo shi in tana k'asar....
Daga karshe dai ganin ya zame mata lalura Kuma baida wani amfani a gareta haka ta tursasa shi akan Dole ya saketa tunda baida amfanin da zai yi Mata yanzu, idan Kuma yak'i tafiyar ta zatayi bazai k'ara ganin ta ba har abada, haka a cikin halin ciwo yanaji Yana gani Yana kuka ta tilastasa ya Bata saki ta tsallake ta barshi a garin da baida uwa bale uba, baisan kowa ba baida kowa ga halin ciwo, bayan ta kwashe komai daya mallaka iya gidan da suke haya ta barshi Wanda hayar ta kusa k'arewa dama, inda Allah ya soshi wanda ta nema Mai Dan kula dashi Yana tsananin tausayi Mai sossai ya kuma fahimci wasu daga cikin halayyar da yake ciki shida matarsa a zaman da yayi dasu, duk da shima baida shi Dan babun ce ma ta Sanya shi amsar aikin kula dashi, Kuma tace ta sallamai Amma bazai iya tafiyar yabar wannan rayuwar cikin k'angi ba, hakan yasa ya yanke shawarar ci gaba da zama Yana kula dashi domin Allah, hadda abinci ta hanyarsa Harun ke samu yaci, duk da har yanzu kukansa da maganar bai wuce Sofie ta dawo gareshi ba Dan tsananin soyayyar da yake Mata, Sam baiga laifinta ba saima laifin kansa yake gani daya had'u da ciwo har ya zamo Mara amfani a gareta( tsafi gaskiyar Mai shi, Allah kayi Mana tsari da miyagun mutane da aljannu ka karemu daga abinda muke tsoro da gudun faruwarsa a kayin mu, Allah ka iya Mana da iyawarka).
Mutuniyar Taku kuwa, tana barin garin kano Abuja tayi wa tsinke gurin hamshakin alhajin da suka tab'a had'uwa a k'asar Spain ya lak'e Mata yake Mata naki ko wace Rana, soyayyar Harun ta hanata kulasa, yanzu da dama ta samu Kai tsaye takai kanta da kanta suka jone, suke cin duniyar su da tsinke, ta manta da kowa da komai, duniyar kawai ta saka a gaba( duniya dai ta tafi bagaruwa iya jima, kada kayi murna Dan duniya ta aureka Dan kuwa saida ta saki wani Kafin ta aureka bi sannu dai)..
Komai Yana da lokaci komai ka gani a duniya Yana da iyaka, a yau ne mutumin da ya sayi gidan Harun na farko( Wanda suka zauna da Ummu Ruman) yasa akayi rusau tare da tone kasan domin kafa masana'anta a Nan ne Kuma suka tone duka layukan da Sofie ta binne a cikin gidan(nasan baku manta ba)....
Sossai ake samun ci gaba a jikin Harun Dan kuwa Sani mutumin da ke kula dashi, gurin masu gyaran kariya a gargariyance ya koma da Harun, cikin ikon Allah aka samu dacewa har yake iya takawa da sanda Amma kuma hannayensa ba laifi Yana iyayin wasu ababen sannu sannu......
Kwance yake Amma kamar Wanda ke a farke yakejin kansa, abubuwa da dama ke shigowa kansa jinsa yake kamar bashi ba, Yana feeling empty life, so Yake ya tuna wanene shi amma ya kasa....
Juye-yuje kawai yake Yana banka kafufunsa da yakejinsu wasu irin gangar jikinsa, cikin hakan ne k'afarsa ta fad'a k'ark'ashin gado da yake dama a kasa yake kwance kan tabarma, wata tukunya ya banko ta laka tuss kakeji ta fashe, tuni wani hayaki ya Fara fita bak'k'irin acikinta, zumbur ya mike zaune tare da dafe kansa gaba d'aya da hannayensa dake barazanar rabewa gida biyu, jin yake d'akin na juya masa gaba d'aya, ba abinda take maimaitawa sai innalillahi wa'innah ilairrajiun..
Sani dake wajen d'akin Yana wanke masa kayan ne ya jiyosa, da sauri ya shigo d'akin tare da fad'in..
"Lafiya dai Yayana?" Da yake haka yake kiransa, ido ya zuba masa Yana kallonsa tare da bin d'akin da kallo kamar wani bako haka ya koma bin jikinsa da kallo cikin tashin hankali ya maida kallon sa ga sani dake kallon sa, shima a mamakance, cikin sanyi murya kamar Mai tsoron magana yace...
"Umm Ruman, Salamah, Abdul ina suke? Ina ne nan d'in?"
Sani dabai gane Mai Yake nufi ba da kuma ina ya dosa, kallon kawai yake binsa dashi, ganin Wanda yake tambaya ya mayar dashi Wawa yasa shi daga masa murya a tsawace yace...
"Nace ina Mamata da 'yayana suke....!"
*_Maryam Abdul_*
YOU ARE READING
inda rai ashe da rabo....
General FictionIt's all about magic, sacrifice, pity, and true love