© *_HAKKIN MALLAKAR_*
® *_Maryam Abdul_*
_______________________
*_INDA RAI....._*
*_ASHE DA RABO..._*Wattpad me on @MaryamAbdul559
{ 48 }
••• _*EVERYTHING HAPPEN FOR A REASON, BEHIND EVERY REASON THERE'S LESSON, LESSON THAT BREAK U OR STRONG U, BASE ON UR DECISION, IT'S UR CHOICE BEEN BROKEN OR STRONG UR SELF_* •••
Bayan sun fito daga theater room ne, Dr Abdul yace ma Salamah taje gida ta samu hutu, cos har yanzu Bata cikin yanayin ta daya santa dashi, tare da cewa ta tsumayesu anjima zasu zo da madam d'insa, batasan lokacin da murmushi yazo Mata ba, had'uwa biyun da sukayi da Ramlar Abdul taji ta Mata matuk'a, life style d'inta na matuk'ar burgeta, mace ce wacce take da confident a rayuwa...
Zuwan ta gida ba wani hutun da tayi, saima Shirin tarbar bak'in datai tayi, tare da taimakon Zaliha Mai kula Mata dasu Iman da sauran aikin gida da take tayata, ba kwana take ba, dake 'yar cikin KD ce, zuwa takeyi in buk'atar zuwan ta taso, tsaf tayi musu kalolin girke girke, da abubuwan Sha, natural dama gidanta ba'a shan package drinks, tsaf ta shirya ita da yaranta da Mai gidanta suna jiran zuwan bak'in su....
Bayan la'asar suka shigo Journal Ramlah tare da Dr Abdulmajid, aunty Zee da twins wad'anda ta k'ara Haifa bayan zainab d'in sukazo dasu, yaran da sukaci sunan Dadi Auwal da Abbansu Nihal Yusuf suna kiransu adeel da abid.....
Cikin madaukakin farinciki suka rungume Juna cike da jindad'in had'uwar tasu, direct dinning dire su, Nan sukaci sukasha, sunata raha da tsokanar juna, barin ma Dr Abdul Mai yawan son wasa, bayan sun kammala ne, suka dawo cikin falon tuni iman da Islaha suka ja aunty Zee da su adeel zuwa d'akin wasan su duk da dai zainab d'in ta girme musu haka ta shige cikinsu, Anil na hannunta dama gwanar son yara ce...
Gyaran murya Dr Abdul yayi alaman zaiyi magana Mai muhimmanci "Dr Salamah, yallab'ai ya gayamin duk abubuwan da suka gudana da alakar da ke tsakanin ku da patient d'in mu Safiyya" yace tare da duban Hammad d'in, murmushi kawai Hammad yayi ba tare daya ce komai ba, itama murmushin tayi kafin yaci gaba......
"Salamah jinki nake kamar k'anwa a gurina, kamar Nihal kamar meenal da Husna nakejinki" harara Ramlah ta dalla masa "oh sorry to kamar Madam Ramlah" dariya sukayi a tare....
"Rayuwa tana tafiya ne akan sanadi, kowanne sanadi yakan zo da dalilin sa, kodai ya zamo dalilin karya ka ko kuma ya zamo dalilin karfafa ka yadai dangana da yadda mutum ya d'auki rayuwar sa, kin ganni Nan na tashi ne kawai da mahaifiya ta ba tare da babana ba, a sanadin kakata mahaifiyar babana dalilin ta kuwa nak'in auren iyayena kawai Dan Mami na ta kasance ba 'yar masu dashi ba, to Ni Kinga my granny ce ta samar min cikas a rayuwa, Amma hakan bai zamo silar da banci nasara a rayuwa ba illah kawai karfafa min datai, Kinga Ramlah gata Nan" ya nuna ta.....
"Itama duk labarin mu iri d'aya ne, mamarta Tasha wuya a hannun kakarta itama mahaifiyar Babanta, k'arshe itama ta tashi cikin k'uncin rayuwa duk da haka Bata k'araya ba, k'arfafa itama akayi, kema the same thing matar uba Kuma kema ta k'arfafa ki, tunda gaki a matakin da tace bazakije ba..."
"Duka mun yafe ma kakannin namu Kuma Mami da Abba sunci gaba da auren su bayan dogon lokaci(duba littafin abdulmajid) munci gaba da mu'amala dasu kamar komai bai faru, still kinga mune masu nasara, so pls Salamah forgive and forget duk da nasan is not easily to forget buh try as much as u can....."
Murmushi tayi bayan ta Gama jin bayanan sa "in nace maka I already forgive her tun kafin yanzu ba lallai ku yadda ba, na yafe Mata, mantawa ne kamar yadda kace na kasayi but inshaa Allah, zanyi k'okari naga komai ya wuce, and nice zanci gaba da kula da ita harta samu lafiya inshaa Allah"
"Haka nasan adilar matata Allah ya Baki ikon kula da ita"
"Dad'in abin dai Nima da tawa adilar a kusa" cewar Dr Abdul Nan dai suka mayar da abin wasa, basu sukabar gidan ba sai bayan magrib bayan sun Sha firar su day labaran tuna baya da suka bawa juna na game da rayuwarsu, tare da yiwa juna al'kawarin ziyartar juna time to time tunda duk su Duka ma'aikata ne, tsaraba sossai ta hadawa su amatu dasu Abdul tare da gayama Dr Abdul ya kawo matasu weekend....
*************
Tsawon sati Sofie ta kwashe a asibitin ba tare da tasan Wanda ke kanta ba, dak'yar suka shawo Kan ta, ta farfad'o, lokacin da ta farko nurses kawai anan Nan wata nurse ta gayamata iya abunda ta sani game da ita da yarda Dr Salamah ke bata kulawa, jin sunan Salamah kawai da tayi Nan da Nan jikinta yayi sanyi duk da a ranta tana fatar ace Salamah ce wannan Salamar Mai kula da ita, ta samu ta rokesu gafara kota samu sassauci a rayuwar ta......
Lokacin da Salamah ta shiga wajenta, Sam Bata ganeta ba, saboda gaba d'aya ta canja ta Zama cikakkiyar mace Mai ji da kyau, Isa arziki, da muk'ami, saida nurse ta tabbatar Mata itace Dr Salamah,
"Sannu aunty Sofie, ya kike jin yanayin jikinki yanzu?" Muryar Salamah ta d'oki kunnuwanta...
"Salamah ce, wlh itace, Salamah Ashe zan k'ara ganinki a rayuwa"
Murmushi tayi tare da Zama kujerar da aka tanada domin Dr, dama tuni ta mayar da ita special room ita kad'aice a ciki " *inda Rai ai ba'a cire RABO* aunty Sofie....
Kuka Sofie ta fashe dashi, Kuka ne Mai cike da nadamar rayuwa, kuka ne dake nuna tsantsan kaskancin Mai yinsa, kafin ta Fara cewa " kin gani ko Salamah, Kinga yadda rayuwa ta mayar Dani? Kina kallo amanarku Bata bani bashi ba? Tun ranar da nai sanadin mahaifinki ya koreki Salamah a tunani na, rayuwar ki na lalata duk iya k'okarin da Deeni yayi Dan na gane gaskiya banji ba, Ashe dai Mai rabon Shan duka ko Ana kwab'arsa saiya Shashi, haka na tattara Harun da duk wani Abu daya mallaka a rayuwa mukayi k'aura zuwa Kano" Nan ta shiga Bata labarin zaman su kanon da yadda ya samu accident ya karairaye da yadda ta tursasa shi ya sake ta bayan ta kwashe komai nasa, tabi Alhajinta Abuja.....
"Ashe wuk'a ce na dab'awa kaina ban sani ba, ashe alhakin Harun da ahalinsa ne zai fita kaina, da kaina nakai kaina makasata, Allaji Maddu mugun mutum ne Wanda ya gogu ya kware a mugunta, ya dama Ni ya shanye a duniyanci da wayewa, haka yai ta yimin iza Mai kantu ruwa, har saida ya rabani da duk wata k'addara ta Harun Dana gudo da ita, da sunan ya bud'e min share a kamfaninsa ya Karb'e takardun Harun ya nemawa yaransa aiki dasu, da zummar zamuyi 50 50 nida yaron, saida ya tabbatar ya Gama kwace komai nawa ya kwashe ni mukayi kasar Dubai da sunan shakatawa, kwanan 2 acan ya sulale ya baroni k'asar da bansan kowa ba, a ranar aka koreni daga hotel d'in da muka sauka, dama Ashe iya kwanakin biyu ya Kama, ashe allaji Maddu cikakken Dan damfara ne ban sani ba, haka na tagayyara na wulakanta a cikin Dubai, nayi Allah ya isa yafi cikin buhu nayi kuka har saida nakai babin da bana fitar da hawaye, saida na samu wata d'aya cikin Dubai a wulak'ance ina kwana a titi abinda zanci ma yafi k'arfina, daga lokacin ne na Fara gane ashe duniya haka take tafi bagaruwa iya jima"
*Big Sorry my people👏🏾 Maryam abdul dince uzurikanta suka fita yawa, Amma inshaa munzo gargara, Allah yasa mudace duniya da lahira😊*
Pls
#Vote#
#Share#
#Comment#*_Maryam Abdul_*
YOU ARE READING
inda rai ashe da rabo....
General FictionIt's all about magic, sacrifice, pity, and true love