© *_HAKKIN MALLAKAR_* ® *_Maryam Abdul_* _______________________ *_INDA RAI

599 36 0
                                    

© *_HAKKIN MALLAKAR_*

® *_Maryam Abdul_*

_______________________

*_INDA RAI....._*
              *_ASHE DA RABO......_*



        *DAGA MARUBUCIYAR*
____________________

1. *HADUWATA DAKE*
2. *ABDULMAJID*
3. *A DALILIN PRE-WEEDING PICS*
4. *ZURI'A D'AYA*
5. *MEYE LAIFINTA?*


Wattpad me on @MaryamAbdul559




*Afuwan! Afuwan!! Afuwan!!! Da babbar murya my fans, abubuwa ne sukamin yawa sannan ciwo shima ya saka nashi kwaban🤦🏽‍♀💉, fatar zakumin azuri, kuci gaba da hakuri Dani, abubuwa ne sun canja ba kamar daba, aci gaba da hakuri dai👏🏼*





{ 5 }







Kamar kura da mayen k'arfe, haka yakejin zuciyarsa na azalzalarsa akan sai ya bi Hamdala restaurant, gurin yafi k'arfin wata 2 bai bi kota kan titin unguwar ba, saboda kawai tsare girman alkawarin da yayi wa matarsa, saidai yau a yanda yakejin zuciyarsa idan baije gurin ba ko mutuwa zai iyayi watakil....

" 'yar uwa! Yadai na ganki yau wata iriya kodai nak'udar tsaye kikeyi, nama dai kula 'yan kwanakin nan ganinan dai wata sululu dake kodai akwai damuwa ne?" Murmushin yake ta saki tare da tallabe cikinta da yayo kasa alaman ya kusa zuwa duniya....

"Aunty Wlh nima bansan meke damuna ba, amma a yan kwanakin nan ina yawan mugayen mafarkai, game da Salamah ga yawan fad'uwar gaba da nakeyi ba dalili lokaci lokaci" jinjina kai Maman su Ya Hammad tayi itakam batasan fassarar mafarki ba, Amma tasan wannan baxai wuce sharrin shed'anu ba..

"Karki damu auntyn su, Inshaa Allah ba abinda zai faru kedai ki dage da Addu'a kawai, ki kuma mik'a al'amuranki gurin Allah, kinji ki kuma ci gaba da nema mata tsari daga sharrin shed'anu da mutane ma, Allah yana ji yana kuma gani kuma Yana tare damu inshallah"....

Sossai maganganun suka kwantar mata da hankali, nan sukaci gaba da firar su kamar kullum, dake yaran duk suna makarantar boko har Salamah an shiga kg ya rage kawai Kausar da shekarunta basu Kai ba......

Tunda ya Parker motarsa akan idonta, nan take murna da farinciki suka lullub'eta ta tabbata komarta ta Kama kifin...

Cikin takun nan nasa na matashi Mai ji da kyau da yan canjinsa, ya shigo d'akin, itama cikin kissa da karairaiya ta isa gun da yake zaune, tana tauna chewing gum irin na rik'akk'un 'yan bariki, a mamakin ce maimakon ta bashi haushi kamar kullum sai yaji zuciyarsa na ingizasa akan ya k'are mata kallon, cikin dak'ik'u k'alilan ya kalleta tsaf, ba laifi tana da kyau da zubi irin na mata, saidai koda wasa wutsiyar rakumi ai ta riga tayi nesa da k'asa, tsantsan cikar halitta da kyawu Yana gun Umm Ruman dinsa, jinin shuwa...

Wani miskilin murmushi ta sakar masa tare da kanne ido d'aya tana wasa da harshenta, wadda hakan ba k'aramin tasiri yayi gareshi ba, duk da k'okarin dannewa da basarwa da yake, ya kasa dauke idonsa akanta..

"Yallab'ai me za'a kawo maka?" Kalmar da ta ankarar dashi kenan ya samu ya fitar da kwayar idaniyarsa daga nata, da yakejin kamar tana zuba mashi dafi ne....

"Ur wish ma'an" kalmar da ya iya furtawa kenan, wacce a zahiri shi baima San meyace ba, wani irin juyi tayi shima cike da salon Jan hankali, ta wuce zuwa kawo masa abinda ta tanada musamman domin shi....

Binta yayi galala baki sake, harta bacewa ganinsa, da yatsa biyu ya daki gaban goshinsa tare da fad'in "what wrong me?"

Ba tare da b'ata lokaci ba, ta dawo da babban tire cike da k'ananun flasks da mug, gabansa ta dire tana Mai tsaresa da mayun idanunta, tare da ci gaba da jifarsa da wannan murmushin nata na cuta....

Wasa- wasa tayi ta zolayarsa da ha'intarsa har saida yaci abincin da ta kawo masa fiye da yadda ya zata, agogo ya duba cikin sauri ya mik'e ganin yadda  ya b'ata lokaci yasan princess d'insa na can nata duba agogo, Dan ya matuk'ar b'ata lokaci ba haka ya Saba mata ba....

"Nawa ne bill d'in?" Ya fad'a yana ci gaba da duba agogonsa..

"It free sir"

"As how?"

"As u see" ta mayar masa, cikin dakewa tana ci gaba da murmushi,

"Ok thanks! Till we meet again" kawai ya fad'a tare da wucewa cikin sauri..

Da murmushi ta rakasa tare da seta hannunta a bayansa tayi alaman harbi "shoot! Hahahaha, d deal is off".....

Motsi-motsi idanuwanta nakan agogo tana kallo to 3 o'clock Amma har yanzu Harun bai dawowa tome ya tsaresa? Bugun zuciyarta ne keta karuwa a kowane k'aruwar dak'ik'a na agogon...

"Mommy! Wai Daddy har yanju bai dawo ba?" Salamah ta jefeta da tambayar wacce ke tsakurar abincin da ke gabanta Dan dai kawai mamar ta tilasta ta cinsa....

"Yana hanya mana, kedai ciki abinci ayi wanka kina gani time d'in tahfiz ya kusa....

Sallamarsa ce ta katse ta, da sauri ta ture filet din gabanta ta ruga gurinsa, d'agata yayi sama Yana amsa gaisuwarta.....

Kallon juna sukayi shida matar tasa tare da sakar wa juna murmushi, tana k'okarin tashi, saurin aje Salamah yayi tare da zuwa gareta ya taimaka mata, jakar ta amsa ta shige ciki Yana biye da ita,

"charming prince,  wanka zaka Fara ko lunch?"

"Ba zakiyi korafin abinda ya rike maki niba princess" yace bayan ya dawo ta bayanta ya rungumota.....

"Nasan zaka gayamin ne innayi hakuri" murmushi ya saki  yasan bazai tab'a samun mace kamar Umm Ruman ba, shiyasa yake gudun bacin ranta, saidai tilas yau zaiyi mata k'arya Dan yasan da wuya ta fahimceshi idan yace zai gaya mata gaskiya....

"Kinsan Abdul ai na office din mu?" Da kai ta amsa masa....

"Hmmm! Shine fa ya sakamin rigimar wai Ni kad'ai ne banje naga amaryarsa ba, dole na bisa kuma suka tilastani cin abincin su, kinga dole nai kara naci, shiyasa am full now"

Ido tad'an zuba mishi abinka ga mara gaskiya sai yaga kamar tuhumarsa take koma ta ganosa tunda bai Saba mata k'aryar ba...

"Ayyah! Fatar suna lfy dai ko" ta katsesa..
"Lfy qlau suke"

"Good! Barin had'a maka ruwan wanka" saurin janyota yayi ya zaunar a gefen gado...

"Relax here baby! Zanyi da kaina, Allah yayi maki albarka"

"Ameen habib albi" ta amsa tana bin bayansa da kallo, tana me fatan su rayu a haka har abada....

Shower ya sakarwa kansa kawai, Yana jin ba dad'i a ransa akan abinda yayi wa matarsa, yayin da gefen zuciyarsa ke tariyo masa wancen yarinyar ta restaurant, yanayinta, maganarta, tafiyarta, Kai everything about her....

"To hell! What happen to me?"


















*_Maryam Abdul_*

inda rai ashe da rabo....Where stories live. Discover now