© *_HAKKIN MALLAKAR_*
® *_Maryam Abdul_*
_______________________
*_INDA RAI....._*
*_ASHE DA RABO..._*Wattpad me on @MaryamAbdul559
{ 38 }
*Astagfirullah! Astagfirullah!! Astagfirullah!!! Lana wa lakum min kulli zanbih hatta tugfar'* 🤲🏼
__Sauri sauri tayi shirinta cikin Arabian gown black, tayi rolling vein d'inta, cikin side bag ta wayoyinta da sauran tarkacen ta, saida ta biya ta gayawa mom ta dawo zasu Kuma fita da Hammad sannan ta cimmusu...
A motar da yazo da ita ta samesu suna hirarsu Feenah ce driver seat alaman ita zata ja, shiko Yana gefenta baya ta shiga tana jin Feenar na fad'in inta gaji da driving ita zata karb'a tunda sune sukasan garin...
Shiru tayi Mata Dan batajin zata iya wani gangancin da yafi wannan da tayi a yanzun yadda su shigo mota d'aya a tare su uku, busy tai keeping kanta ta hanyar chat duk Dan kar ma taji firarsu ta toshe kunnuwanta da earpiece...
"Beb Wai bakya ji nane?" Feenah ta fad'a tare da tab'o ta da hannu, earpiece day'a ya zare tare da cewa..
"Magana kikeyi?"
"Aa ihu nakeyi, kajimun yarinya tun dazu Ina Miki magana kinmin banza kamar bake agun" cikin jin haushi take maganar, murmushi tai "sorry Mom! me kike cewa ne?" tace tare da Kama kunnenta d'aya, dariya ce ta sub'uce Mata, duk tsawon lokacin Nan da take nacin tsokanar ta akan ta rik'a ce Mata mom batayi ba sai yau, tunda batada gaskiya....
"Kima barshi na tuna nice boss d'in ai" da Kai kawai ta amsata tare da mayar da earpiece d'inta...
Hammad dake kallon su, sossai yake girmama shak'uwar dake a tsakanin su, tabbas yanzu ya gane me Salamah ke nufi data dage akan Feenah, shak'uwar su me girma ce....
"Ya Muhammad mu Fara zuwa Park ne?" Feenah ta katse Masa tunani, murmushi ya sakar Mata tare da ansawa...
"Yanda kikace lovely yau ranar takice" duk yadda taso ta danne kasawa tai, karaf idanunansu suka tsarke guri d'aya, a tare suka ji wani shock ya ziyarcesu....
Basarwa yayi ta hanyar dage Mata gira sama alamar tambaya, ita Kam da sauri ta d'auke idanuwanta k'irjinta na dukawa da gudu, lumshe idanuwanta tai tare da furta "hazbiyallahu wani'imal wakeel"
Har suka shiga cikin park d'in a tsawwale take ta kasa sake duban inda yake bare idanunsu su sake had'uwa, ga idanunsa da takeji a jikinta a duk wani motsin ta, sossai tayi Dana sanin biyosu dama ta fake a wani abun daya fiye Mata alkhairi, ita tsoron ta ma kar Feenah ta fahimci wani abu musamman kallon Nan yayi yawa...
Feenah Kam tana ankare da duk motsinsu tana girmama k'aunar da sukewa juna, duk da yadda Salamah ke danne wa, indai kasan asalin soyayya da masoya, daga yanayin da suka shiga kad'ai ya isa kasan tsumammiyar k'auna ce ke aiki a gurin, kullum k'ara godewa Allah take d'aya sa batayi kuskuren da zata kasa yafewa kanta ba tsawon rayuwarta, sulalewa tayi gefe tasha firar ta da Akbil da shakuwar su ta k'ara girma fiye da da, wacce take da tabbacin zata zama k'auna Mai girma *Inda da Rai da Rabo*
******
Sossai suka zaga garin dashi duk wani muhimmin guri sun jajje dashi, garin ya Masa kyau sossai da yanayin sa, dama a rayuwar sa yanason tafiye tafiye guraren daban daban a sassan duniya, shiyasa ya zabi pilots duk da cewa makarantar sojoji yayi kuma yayi courses na army d'in kawai dai abinne ya fita ransa daga baya...
Duk yadda Feenah taso ta amshi driving fau Tak'i ta fake a ciwon da ya dad'e da sauka, mamakin yadda a kullum taga Hammad da sabon yanayin da zata tsinci kanta a ciki, ta amince ta kuma yadda na feenah ne, zuciyarta Bata Mata adalci akan Hammad, ta rasa Ina zata saka kanta da rayuwar kwanakin Nan uku daya musu sun Mata fami matuk'ar fami, ga Akbil a gefe d'aya sai take ganin dokin son da yake Mata kafin a bashi ita babu a yanzu sai suyi 2days ba tare da sunyi waya ba, inta Kira kuma yace Yana busy, ta Fara tsorata da lamarinsa, tana tsoron ta wulakanta a k'asar da ba tasu ba, yanzun ma daya Kamata su samu kusanci da cikakkiyar k'auna Babu, musamman yanzu daya koma k'asar su, tana tsoron kar yace zai Rama abinda ta Masa ne fa, duk da a kullum gaya Mata yake abubuwa ne kawai suka mishi yawa, Amma matsayin a ransa na Nan daram bazai canju ba...
Feenah ta kawai sukayi maganar da ita ganin sunada kusanci, tace kar ta damu zata gano koma meye kawai dai ta kwantar da hankalin ta, ga Hammad tun da ya koma ba ranar da zata fito ba tare daya kirata, gaisawa kawai sukeyi ya kashe, hakan ba k'aramin k'ara zumar mata da zuciya yake ba, tana jimamin al'amarin, abunka da abinda zuciya keso har timing lokacin yake kiranta tai duk inda take da lokacin ya kusa zata kame gefe ta nutsu kamar Mai shirin sallah......
*Zanci gaba da Novel d'innan ne kawai saboda katse novel ba halina bane, Amma Naga Sam bai karbu ba gunku fans😏😏*
PLS
#Vote#
#Share#
#Comment#*_Maryam Abdul_*
![](https://img.wattpad.com/cover/198182184-288-k792859.jpg)
YOU ARE READING
inda rai ashe da rabo....
General FictionIt's all about magic, sacrifice, pity, and true love