© *_HAKKIN MALLAKAR_*
® *_Maryam Abdul_*
_______________________
*_INDA RAI....._*
*_ASHE DA RABO..._*Wattpad me on @MaryamAbdul559
{ 20 }
Ba abinda ke tashi cikin falon sai shesshekar kukan Salamah da Feenah suna ruk'unk'ume da juna kamar wasu tagwaye, Mom kukan take, zuciyarta ta karye matuk'a lallai duniya tana cike da azzalumai da baragurbin mutane, rashin imani da tsoron Allah ya mamaye zukatan wasu mutane Sam basa tunanin lahira da kwanciyar kabari duniyar kawai suke hange, wannan itako da wane irin suna zata kirata Dan ta wuce azzaluma ma, daga ji ba tambaya akwai aikin sihiri a tare da baban Salamah Dan acting d'insa ya nuna hakan lallai Yana buk'atar Addu'a sossai, daga duk wani Mai k'aunarsa...
Abba da Ya Saif kansu labarin wannan innocent and silly girl ya girgiza su itako wannan matar wace iri ce a rayuwa, wane irin uba ne baban Salamah, Abba ke jinjina al'amarin a ransa....
"Cry no more DotA!"
Momy kuwa d'ago su tayi tare da zaunar dasu gefenta tana rarrashinsu dama tasan Feenah da matuk'ar tausayi da Kuma raunin zuciya ba abin mamaki a ciki Dan tayi wannan kukan, sanda suka samu nutsuwa sannan Dady ya Fara magana...
"Salamah inaso daga yau kisa a ranki tamkar kina tare da iyayenki, inshallah nida Hajia zamu rik'eki da kyau tamkar Nafeesa, ki d'auki 'ya'yan mu a matsayin 'yan uwanki na jini, Suma inada tabbacin zasu rik'eki a matsayin tasu, maganar karatunki Kuma nayi Miki alkawarin d'aukar nauyin kowanne irin karatu kikeso kiyi a duniya ko wacce kasa kike ra'ayi zan kaiki da duk wasu lalurorinki na rayuwa na d'auka kamar yadda nace Miki ki d'auke mu a matsayin iyaye haka nake nufi ke 'yata ce, ina fatan Allah ya bani ikon cikawa" gun mom ya juya "Hajia nafi kowa sanin wacece ke, nasani zaki rik'e Salamah da Amana tamkar Nuriyya da Nafeesa, Allah ya baki ikon riketa da kyau" ameen ta fad'a a sanyaye....
Haka ma Saif da Feenah duk saida Dady ya damka musu amanar Salamah, sannan ya tabbatar mata zaiyi iya k'okarin sa na binciko Mata mahaifiyarta duk da yasan al'amarin da wahala kasan tuwar babu komai dazai iya sadar dasu cikin sauki, sannan ya tabbatar Mata zai mayar da ita da kansa hannun mahaifinta in lokacin hakan yayi....
Cikin kukan farinciki take zuba musu godiya bayan ta gama godewa Mai kyauta Mai biyan buk'ata garara misali Wanda bai da misali ubangijin talikkai...
*******
Within 2 to 3 weeks duk wani shirye-shiryen da ya kamata domin d'agawar su zuwa malesia Abba yayi Kama daga amso original copies na credentials d'in da yi mata passport da Visa, can ma malesia tuni yayi musu cuku-cukun makarantar da zataci gaba dama ita Feenah tuni an riga anyi nata inda zata karanci law ita Kuma Medicine kamar yadda take buri tun farko...
Haka suka tattara suka lula cikin sararin samaniya zuwa k'asar malesia, for d 1st time in her life yau gata a jirgi (safe mercy sweeto Salamah) lol.
Duk yadda Take tunanin familyn Alhaji Aliyu Mai Dala sun wuce Nan, mutanen kirki ne to d extend kowanne cikin su Yana k'okarin ganin ya sakata farinciki ne tare da son mantar da ita rayuwar ta, ta baya hadda Nuriyya da Nuren da suka isko a can a takaice dai familyn is sweet and loving family...
Sossai ta sake dasu itama takejin su kamar tana tare da iyayenta da 'yan uwanta na jini ne, musamman Feenah da sukayi wani irin sabo da shakuwar gaske Kai in ba kasani bane zaka iya cewa twins ne masu mabanbantan kamanni Dan kuwa hadda sutura iri d'aya suke sakawa different color, tabbas ta samu yanci da cikakkiyar nutsuwa a tare da wannan familyn da batasan dame zata saka musu face ta bisu da Addu'ar tabbatuwar farinciki a cikin su, tare da fatan musu dace a can lahira, Dan sunyi Mata abin tasan iya shi ne Koda iyayen da suka kawota duniya ne zasuyi....
Burinta na farko ya cika ta samu damar Fara karatun ta na medicine Wanda take rokon Allah ya Bata ikon kammalawa lafia, sai burinta na gaba da batasan yaushe zai cika duk da ta sani ita butulu bace mom ta maye Mata gurbin uwa sossai Amma tanaso sossai koda sau d'aya ne s rayuwar ta ta had'u da mahaifiyarta tana son k'ara ganin mahaifinta tana son tasan halin da yake ciki duk da kullum Yana cikin Addu'ar ki ta kamar yadda ta sab'a kuma mom tace ta dage sossai dayi masa Addu'a, ko zata sake had'uwa da Aunty Maryam? ya Hammad d'inta? Ummitar da Kausar? Fauziya fa? Dangin mahaifinta dana mahaifiyarta? Duk lokacin da take irin wannan tunanin takan ce *inda Rai da Rabo* inshaa Allah zamu gana wata Rana daku gaba d'aya, yanzu kam kacokam ta tattara duk hankalin ta akan karatun ta ne Dan shine take gani babban gatan da bayin Allah Nan sukayi Mata bataso ta basu kunya, tanaso suyi alfahari da ita suji basu yi Westin money akanta ba....they want make them proud of her...
*****
"Alhaji so nake mubar garinnan ya isheni" kamar wani soko yace "to Safiyya ina kikeso mu koma?" Yatsina fuska tayi tare da juya ido alaman tunani "kano nakeso mu koma, sokoto ta isheni"
Cike da bin umurninta "to shikenan sai ayi yadda kikeso ai, ki tsara Mana yadda tafiyar zata kasance Tau" Zaharadden dake shigowa gidan yaji abinda yayar tasa ke fad'a ya tsaya, idasa shigowa yayi fuskarsa cike da tausayin mutumin nan tsawon lokaci yake lallaba da bibiyar yayarsa akan ta sassautawa bawan Allah Nan danshi da gaske har ransa tausayin sa yake gashinan dai kamar jariri sai yadda tayi dashi Amma mirsisi batajin say Dan ta riga tayi nisan ciwo saidai addua kawai.....
"Yawwa Deeni yanzu kuwa nake da niyyan kiranka sai gaka kazo, dama so nake ka samo Mana masu siyan gida da filaye Dan zamuyi kaura zuwa kano Dan kasan ance na zaune baiga gari ba" galala yayi Yana kallon ta tare da cewa "Tau" yadda ta d'aure fuska tamau kar ma yaga damar ta..
"Saika Fara shiri kaima Dan tare zamu koma dakai" cike da takaici yace "Hajia aini gida zan koma Umma tana da buk'ata ta zuwa yanzu" cikin nuna rashin damuwa tace "Tau yadda kakeso, nidai kayi abinda na gaya maka"
*Kuyi hakuri masoyana nasan kunyi ta zuba ido shiru shiru kuke ji kamar an tura bawa garinsu, wlh ba Jan Rai bane yanayi ne kawai yaxo da hakan Dan Allah ku Kara hakuri dani Nima abin na raina Dan zamma iya cewa na fiku damuwa, Fara novel na dakatar ba dabi'a ta bace inshallah tunda na Fara zan iyar indai da Rai da lafia, mudai kara hakuri mu duka, nagode #one love# so d'aya.....*
*_Maryam Abdul_*
YOU ARE READING
inda rai ashe da rabo....
General FictionIt's all about magic, sacrifice, pity, and true love