© *_HAKKIN MALLAKAR_*
® *_Maryam Abdul_*
_______________________
*_INDA RAI....._*
*_ASHE DA RABO......_**DAGA MARUBUCIYAR*
____________________1. *HADUWATA DAKE*
2. *ABDULMAJID*
3. *A DALILIN PRE-WEEDING PICS*
4. *ZURI'A D'AYA*
5. *MEYE LAIFINTA?*Wattpad me on @MaryamAbdul559
{ 4 }
"Sobina sannu da zuwa kinsha hanya, tun jiya nake tsumayen isowarki nan Dan sakon zuwanki ya riskeni tun watan jiya" cikin yarensu na igala yake maganar da Sofie wacce ke zuba murmushi jindad'i tare da k'ara yadda da bokan nata, falo ne na musamman wadda yaji kayan jindad'i da more rayuwa wad'anda ke gwamutse da kayan bokanci ko wanne sako da lungu na kusurwarsa, shi kansa ogan nasu zaune yake hakimce akan fatar Zaki...
Wani irin allon k'arfe ya jawo tare dayin wasu surkulle kala-kala da yaren da shi kadai ya San shi, ya d'auki lokaci yana yi, itadai Jamila k'awar Sofie kamar tv haka ta mayar dashi, zuwa can ya d'ago allon ya nuna mata, cikin mamaki da zabura Jamila tace nuna abinda ya fito cikin allon....
Wanda ba komai bane face foton falon gidan Harun suna zaune shida matarsa da 'yarsa cikin kyakkyawan yanayi da kowane iyali ke buk'atar kasancewa....
Murmushin nata na mugunta kawai takeyi, yayinda shima ya saki wata iriyar kafurar dariya wacce sanda falon ya amsa...
"Ya kike so ayi ne? A haukatar da matar ne? ko a rabasu ne? Koko a mayar da ita bora ce sai yadda kikayi da ita? Wanne kikeso?"
"Gigi go gi" tace tare da d'ora tafin hannun daman ta a hagu ta sunkuyar da kanta a kansu alamar sujjada ne ko meye oho...
"Da girman kujerar tsafinka mara dusashewa(wa'iyazu billah, Allah kad'ai ne Mai wannan mukamin ba Dan adam ba, Allah ya kiyashe mu fad'awa shirka komai k'ankantar ta)
"Nadai fara shiga gidan tukunna, nafiso na zauna da ita koda na wata d'aya ne, na gasa mata aya a hannu, ladar hararan da tamin, sannan ta k'ara gaba naci duniyata da tsinke! Shikam tun yanzu nakeso ya dawo k'ark'ashin ikona" cikin kwanciyar hankali da murmushin kasaita take zare zancenta hankali kwance...
Wasu layu guda uku ya bata yace ta binne d'aya a mak'abarta, d'aya a k'ofar kasuwar garin, d'aya a gidansa bayan aure, sannan ya bata wasu kulle-kulle magani yace ta ciyar dashi dasu daga lokacin da ya fara zuwa restaurant d'in da take aiki, amsa tayi tana k'ara kod'asa da jinjina masa, tare da aje masa damin kud'i....
Jamila ya kalla datai zuru-zuru da ita tana kallon abinda ke wakana kamar a mafarki, lallai Sofie ta haura duk wani hasashenta a kanta...
"Kema ungu wannan ki ringa shafawa kawai idan Zaki fita duk Wanda kikeso da kun had'a idanu to an wuce wurin" kwallin ta karba hannu na rawa zata d'akko kud'i a Jakarta yace aa wannan a kyauta ya bata tunda k'awar Sofie ce, su tsumayi wani karon.....
"Assalamu alaikum mommy na dawo" murmushi ta saki tare da ware mata hannayenta alaman taje gareta, Aiko da gudun ta, isa gareta tare da cire hijab d'in islamiyyar daya kasance ya kusa Kai mata k'asa...
"Oyoyo da angle din dadynta yan islamiyya, fatar ansha karatu sossai ba?"
Aiko an tab'o mata abinda takeso nan fa zuba ta tashi "eh mommy bari ma kiji karatun, malamin mu cewa yayi fa wai lah yadhular jannatu nammamun!"
"Iyye yarinyar Daddy, to me yake nufi ne?" K'ara sakin baki tayi tana dariyar jindad'i "wai Mai annamimanci bai shiga aljannah, mommy waye annamimi?"
"Rungume 'yarta sossai tayi tana Mai jin sanyi a ranta "Salamah annamimi shine munafuki, Mai had'a wancen da wancen fad'a, Mai cewa wane yace ko yayi ba tare da yayi ba kuma koda yayi d'in idan ba Mai kyau bane bai kamata a fad'a ba kin gane?"
"Mommy kamar yaya cike nufi?"
"Yawwa 'yar maranta, kinga yanzu kamar Ummitar tayi ma mamanta laifi kuma maman bata sani ba kuma bataso ta sani sai kije ki fad'a ma mamanta bayan kinsan za'a doketa, kuma kila ma bada gangan tayi ba, ko kuma Kausar tace wani game da Ummitar ko Sadiq ko Hammad dinki" ta k'arasa tana murmushi itama murmushin ta saki jin an Kira mata ya Hammad dinta...
"To shikenan sai kije ki gaya musu kice ai kausar tace kaza da kaza kuma kinsan fad'in hakan zai iyasa suyi fad'a ko kuma su Bata kashi, kinga kinyi mata munafinci kenan" ware ido waje tayi tare da kware baki ta kama bakin da hannunta kamar wata babba...
"Yes dota, kinga idan kinayin haka ki dena ba kyau" girgiza mata Kai tayi alaman toh..
"Yawwa gud gal na, zonan a cire uniform muje kici abinci...."
"Mommy, saida fa ya Hammad ya bani abinci yanjun nan da muka dawo"
"Au nafa manta kina da ya Hammad dinki, Mai kula dake"
"Eh mana! Kinga chocolate ma ya bani kuma fa har k'ofar falon Nan ya rakoni kuma ya hana su Ummitar su biyoni wai kar muyi wasa da yawa na manta kayatuna" kallon yarinyar take cike da sha'awar wannan shakuwa dake tsakanin ta da d'an makociyar tata kuma aminiyarta, yayarta, har tana ji a ranta *inda rai da rabo* wata kil wata rana wata k'akkafar alaka zata iya k'ulluwa a tsakanin su, muddin suka wuce a haka har girmansu.....
*_Maryam Abdul_*
YOU ARE READING
inda rai ashe da rabo....
General FictionIt's all about magic, sacrifice, pity, and true love