© *_HAKKIN MALLAKAR_*
® *_Maryam Abdul_*
_______________________
*_INDA RAI....._*
*_ASHE DA RABO..._*Wattpad me on @MaryamAbdul559
{ 25 }
*_RAYUWA KULLUM CIKIN GUDU TAKE, KULLUM CIKIN TAFIYA DA SAUYE SAUYE TAKE, YAU FARINCIKI GOBE BAKINCIKI, YAU SAMU GOBE RASHI, YA LAFIA GOBE CIWO, YAU MUNA A RAYE GOBE MUN MUTU!! MUTUWA!!! WLH TANA KAN KOWA KO NA SHIRYA? KA SHIRYA? SUN SHIRYA? KO DUKA BAMU SHIRYA BA, WLH BA D'AYA DAGA CIKINMU DA ZATA BARI, MU KASANCE CIKIN SHIRI KULLUM MU KASANCE KAMAR BAKI KO MATAFIYA A CIKIN DUNIYA MU GYARA, WLH MU GYARA TSAKANIN MU DA MAHALICCIN MU, DOMIN MU HAD'U DASHI CIKIN AMINCI, ALLAH KAYI MANA DACEWA DA RAHAMAR KA, KASA RANAR MUTUWAR MU TA KASANCE RANAR FARINCIKI A GAREMU YA ALLAH🤲🏼🤲🏼😢_*
"No not Salamah, u will not suppose be here!"
"Nice dai da gaske ya Hammad, Ashe *Inda Rai da Rabo* ba'a cire tsammani banyi tunanin zan k'ara ganinku ba, Ya Hammad Ina Mami da Abba, Ina Ya Sadiq, Ina Ummitar da Kausar, Alhamdulillah" kamar Wanda ya Samu tv haka ya zuba Mata ido yana kallon yadda take maganar gata dai ta girma Amma kallon lokutan baya yake Mata, sai rayuwar ke dawo masa fresh kamar yanzu abubuwan ke faruwa....
"Easy guys, don't tell me dama Gwaggo Maryam ce Aunty Maryam d'inda kike magana" Nuren ya fad'a cike da mamaki...
"Wonder should never end" cewar Ya saif shima da mamakin ya gama cikashi....
"At all dai d world is small, abun yazo Mana da sauki" cewar Feenah.....
"Nima rasa mezance nikam, towai Taya ma hakan ta faru, ya akai ma kuka had'u?"
"Hmm! It long story mu shiga cikin tukunna zakaji komai"
Dunguma sukayi gaba d'aya, fuskar kowanne ka kalla d'auke da farinciki musamman muhammad ga Wanda ya sanshi ya ganshi Dole yasan Yana cikin farinciki kobai fad'a bama, saida sukaje k'ofar falon ya dakatar da Salamah yace sauran su shiga tare dashi Dole ne yaba Mami surprise....
"Mami" ya kirata cikin yanayin sa, na miskilanci...
Sanin baya Mata Kiran banza yasa tace" yadai Muhammad daka banni da murnar ganin yaran Nan nawa kad'ai ma ya isheni....
Mom da sai lokacin ta kula ba Salamah bud'e baki tayi "aa Ina baby......." Saurin toshe Mata baki Feenah tai tana Mata alaman tayi shiru da hannu, sakin baki tayi cikin mamakin meyasa to.....
"Mami Mana zo muje kiga wani Abu minti biyu kacal" ya k'ara fad'a cikin sigar son taje d'in..
"Please Gwaggo" duka yaran suka had'a baki, kallon tuhuma Mami da mom suka musu su Kuma suna kunshe dariyar su,
"Oya muje d'in na ga meye wannan" suna isa k'ofar ya Kama handle d'in ya bud'e tare da fad'ar "surprise!"
Zaro ido aunty Maryam tayi, tare da sakin baki, kafin ta Fara mutsikka ido Dan tama kasa yadda da wacce take gani a gabanta tana Mata murmushi kamar Mai koyon magana ko tsoron tayi magana ta bace mata tace....
"Salamah!"
Da gudu tazo ta rungume ta, tare da sakin kukan da ita kanta ba zatace ga ainihin na meye ba, itama rungume tan tayi sossai tana bubbuga Mata baya...
"Ina ka sameta Muhammad?" Mom tace....
Bud'e hannaye yayi alaman bashi bane murmushi kwance akan fuskarsa "tare sukazo"
"Dasu Aunty Aisha?"
Dakai ya amsa Mata "Allahu Akbar! Mu shiga ciki"
Fad'in irin farincikin da suka shiga guntun feji na bazai d'auka ba, hadda Ummitar Mai jego sai gata ta manta jego hadda tsallenta, bare Kausar Kuma, saida suka nutsu tukun aka zauna kafin a koma maida zance.....
"Lallai ikon Allah yawa gareshi yanzu dama tsawon lokacin Nan 'yata na tare daku ba tare Dana sani ba, lallai munyi sake da zumunci shiyasa har irin hakan ta faru danmu fad'a ka mu gane, Aunty kunyi matuk'ar k'ok'ari keda Yaya saidai nake Allah ya saka muku da mafificin alkhairinsa...
"Salamah munyi nemanki garin Sokoto da zaginta ba, nayi jiran kiranki shiru, munje gidanku akace Kun tashi Kuma ba Wanda yasan inda kuka koma, naso Koda Kai Safiyya Allah dai ya tsine Mata, ta zama guba a cikin al'umma, Allah ya kawo karshen Azzaluma da masu zalinci irinta" ameen duk suka amsa...
Haka suka wuni cikin farinciki har Abba da ya Sadiq suka dawo Suma aka Dora dasu, yan matan ne suka shiga kitchen ranar suka samar musu abinci, Dan zungur suka wuni Ana maida labari, Allah kad'ai ke tayar dasu.....
Muhammad ji yake kamar an gafarta masa a wannan ranar fuskar sa k'awace da murmushi wanda aka kwana biyu ba'a gani, Mami Kam bakin ta kamar gonar auduga gata ga Salamah, kullum damuwar ta bai wuce son sanin halin da take ciki ba, takejin kamar Bata r'ike amanar da umm Ruman ta damka Mata bane, sai yau ta samu yanci taji ta kamar an sauke Mata wani nauyi babba a kanta lallai *inda Rai Ashe da Rabo* gashi yau ta gana da Salamah tana fatan ta gana da Umm Ruman watarana kamar haka ta Kuma danka Mata 'yarta da hannunta.....
*******
"Salamah har yanzun na kasa yadda kece, gani nake Dana yadda na bar gidan Nan bazan sake ganin ki"...
Murmushi ta saki tana Mai wasa da yan yatsun ta "Ya Hammad Ni kaina na kasa yadda Wai mune muka sake had'uwa bayan tsawon shekarun Nan buh Dole mu yadda tun da gamu a tare a zahiri" shiru ya ratsa na tsawon mintuna, jin shirun yayi yawa ne, yasa ta d'agowa karaf idanunansu suka sarke da juna, saurin kautar da idaniyarta tayi tana sauke numfashi kamar wacce tasha gudu, tana tsoron kada ya jiyo yadda zuciyarta ke bugawa da sauri sauri kamar tana Shirin fitowa....
"Kalleni Salamah!" Yace a sanyaye, cike da mutuwar jiki ta d'aga ta kalleshi....
"Ina soyayyata? Ina alkawari nah?" A matuk'ar razane hadda wani zabura ta kalleshi, shikenan abinda take gujewa tun dazun ya faru, meyasa ranar Nan tazo Mata a hakan, meyasa duka kalaman da tayi tattali da tanadi domin wannan ranar ba zasu fad'u ba?
"Sadaukarwa!!" Sashen da ke k'arfafata na zuciyarta ya fad'a, tabbas Dan Halak Dole yasan anyi Mai halacci...
"Soyayya ta nake magana Salamah!" Ya sake fad'a jin shirun da tayi....
"Soyayya ya Hammad soyayyar ka sadaukarwa ce ga Feenah, soyayyar ka Naga Feenah, Feenah tana matuk'ar k'aunar ka, na gani a idonta, naji daga bakinta, don Allah, don Allah na rok'eka, ka mayar da soyayya ta ga Nafeesah wlh tana matuk'ar k'aunar ka"
"How dare you!!?" Ya fad'a a matuk'ar tsawacen da ya saka 'ya'yan hanjinta kadawa.....
*Wacce Nima tsawar ce ta saka wayar subucemin a hannu🥴😜😍*
#vote#
#share#
#comment#Pls
*_Maryam Abdul_*
![](https://img.wattpad.com/cover/198182184-288-k792859.jpg)
YOU ARE READING
inda rai ashe da rabo....
Ficción GeneralIt's all about magic, sacrifice, pity, and true love