© *_HAKKIN MALLAKAR_* ® *_Maryam Abdul_* _______________________ *_INDA RAI

423 26 0
                                    

© *_HAKKIN MALLAKAR_*

® *_Maryam Abdul_*

_______________________

*_INDA RAI....._*
              *_ASHE DA RABO..._*

Wattpad me on @MaryamAbdul559




{ 41 }




Taro yai taro gurin d'aurin auren ya cika mak'il ba masoka tsinke, motoci ne iya ganin idanka birjik sun cika layin, daga can gefe na hango muku zaratan angayen hud'u, cikin fararen shaddodi k'al sun Sha malun malun, tare da dakakkun huluno Na Maid sai ky'alli suke, Akbil sossai kayan suka d'auke shi sai wani irin kyau na musamman ga madaukakin murmushi a fuskarsa....

A can na hango muku gogan naku Hammad, friends saidai muce mashaa Allah Dan kuwa yayi madaukakin kyau a cikin Fara k'al d'in wankansa daga kafa har zuwa Kai, fuskarsa a sake cike da annuri, murmushi yak'i barin bakinsa, hannu kawai yake da 'yan uwa da abokan arziki dake ta tayasu murna...

Gefe Akbil yaja shi tare da rad'a Masa a kunne "zan fa Kira wifey ka, Ina seeking excuse kasan yanzu ta canja Zane" dariya yai tare da dukan kafad'ar sa, tuni sukayi sabo ba kad'an ba, tun zuwansa malesia suka jone "ur Free" yace Yana jin wani feeling a ransa so special Wai a yau shine ya mallaki Salamah? Salamah ta zama tasa har abada, mallakinsa ce? Yama kasa yadda da hakan sai yakejin kamar za'a iya tayar dashi ace mafarki yake, Koda mafarkine ya tabbatar yau d'in babban Rana ce a tarihin rayuwarsa ya cika burinsa " *Inda Rai Ashe da Rabo* " ya fad'a a fili yana Mai yin cikakkiyar godia da hamdala ga sarkin talikkai daya nuna Masa wannan madaukakiyar Rana a cikin ranakun rayuwarsa....

********

Kwance take lahu  duk inda lakkar jikinta take a sanyaye takejin ta, hatta yatsanta nauyi yake Mata, ga zuciyarta data kasa tantance a wane mizani take, tunda taji an dawo daga sokoto d'aurin auren Nuren daga bakin Meenal matar ya Saif jikinta ya k'arasa mutuwa gaba d'aya, shiyasa ta kasa ma zama d'akin da suke ta sulalo ta dawo d'akin Hajja daba kowa bare a dameta....

"Hasbiyallahu wani'imal wakeel" kawai take ta maimaita a bakinta, ring wayarta dake yashe a gefe ta Fara, dak'yar ta zura hannu ta janyo ta, wani irin duka k'irjinta yai ganin future H ke kiranta, a darare ta daga Kiran, daga b'angaren yace..

"Congratulations Salamah, yanzun nan aka Gama d'aura Mana aure,  wish you a very happy bless full marriage life!" Kitt ya kashe Kiran ba tare daya jira amsarta ba, dariya ya kwashe da ita, harararsa Hammad yayi "kudai kaida matarka kun sakomin Mata a gaba, daga yau dai barazanar ku ta k'are a kanta, kwaje can ku k'arata" dariya ya sakeyi, Yana mamakin yadda k'arfi da yaji yaji hausa Akan dagewar Feenah, lallai komai nada sanadi a rayuwa.....

Taji Dad'in da bai jira amsarta ba Dan da tabbas data bud'i Baki asirinta ya Gama tonuwa domin kuwa kukane zai kasance amsar....

A wannan gabar Bata isa ta Hana hawaye kwaranya daga idaniyarta ba, duk da zubar su bazai canja ta rasa Ya Hammad ba, Rashi na har abada, Amma zata bawa zuciyarta yancin samun sassauci ko Yaya ne, sannu a hankali ta shiga rera kayanta Bamai rareashinta bare ban Baki, tana Mai yiwa kanta alk'awarin shine na k'arshe da zata koka saboda rasa Ya Hammad, tare da d'aukar damarar karb'ar Akbil da duka zuciya da ruhinta, ba zata Bari soyayyar Hammad ta rusa rayuwar Akbil ba ta kowanne b'angaren bai cancanci hakan ba....

"Salamah! Salamah kina ciki kuwa?" Ta jiyo muryar Feenah daga falon Inna tana kwalla Mata Kira, saurin tashi tai daga bed d'in tana gyara doguwar rigar shaddar da ke jikinta, tare da d'aure Kanta da d'an kwalin, toilet tayi saurin shigewa tana jiyo Feenar na k'okarin shigowa d'akin...

Bakin gado Feenah ta zauna ganin wayarta da veil d'in ta a saman gadon ga Kuma motsin ruwa tana ji a toilet itama da irin shigarta sak, color kawai ta banbanta su....

Wanke fuskarta tai tare da murza powder da ta shiga da ita, tsaf ta fito kamar ba ita ke kwance a gurin tana kuka ba, kallanta Feenah tai ganin idanta dad'an kumburi kad'an ya tabbatar Mata kuka tai, basarwa Tai tare da fad'in "kukanki ya k'are daga yau inshaa Allahu" a ranta...

"Nad'an shiga bayi ne Koda kike kirana" tace da Feenah tare k'okarin Zama gefenta, saurin mik'ewa Feenah tayi ta Kama hannunta bayan ta d'ora Mata veil d'inta akai "zo muje kiga wani Abu"

"Wani Abu Kuma meye?" Tace tana yamutsa fuska "kedai zo muje kawai" tace tana Jan hannunta suka fice ta k'ofar baya saboda yawan mutanen ke cikin gidan, main falon gidan ta shiga da ita tare da turata ta yanjo k'ofar "angonki ke nemanki" ta fad'a tana Mata dariya....

Bayansa kawai take hangowa, ras ras, gabanta ya yanke ya fad'i "Ya Hammad!" Ta fad'a a hankali kamar Mai jin tsoron fad'a...

Murmushi Mai sauti ya saki tare da juyowa gaba d'aya Yana fuskantar ta "wallahi shine why my heart meyasa zakimin haka" tace ba tare da tasan ta fad'a ba....

Kama kafad'unta yai duka biyu tare da kallan idanunta "kalle ni Salamah nine Hammad d'inki kuma mijinki" zab'ura Tai da k'arfi tare da ture hannayensa daga jikinta, baya ta Fara ja tana fad'in "no Ya Hammad no pls ba Haka mukai ba, aa Kai mijin Feenah....." Turo k'ofar da akayi ne ya hanata k'arasawa..

Feenah ce hannunta sark'e Dana Akbil "nikam Kinga mijina a nan" Feenah ta fad'a tana nuna Mata Akbil d'in da yatsarta d'aya...

"Kamar ya? Ta Yaya hakan ta faru, ku Dena wannan drama pls, Hala kun zauce ne?" Murmushi Feenah tayi tare da takowa gabanta ta Kama kafad'arta..

"Kece zance ki nutsu karki zauce Salamah! Kin d'auka ke kad'ai ce keda irin zuciyar Nan? Kin d'auka hallaci mukai Miki danki biyamu a wani gefe? Waya Baki izinin sadaukar da farincinki Dana d'an uwana? Waya gayamiki, bama son ganin farincikin ki? Kin sani kuwa? Kinsan matsayin ki a zuciya, tun bansan akwai alaka Mai k'arfi ta jini tsakanina dake ba?" Sororo tayi tana saurarenta...

"Da ace na auri Ya Muhammad alhalin shine a ranki, shine ya hanaki bud'e zuciyar ki wa kowa shine farincikin ki, kema kece farincikin sa kece burinsa! Da ace na shiga tsakanin wannan k'aunar Salamah wlh wlh bazan tab'a yafe Miki ba, ba Kuma zan yafewa kaina ba, Kuma daga lokacin bani bake" sossai ta tsorata da kalaman Feenah da Kuma yanayin ta, cikin rawar Baki tace.....

"Kiyi hakuri Dan Allah, ban tab'a ganin soyayyar wani a idonki ba face shi, shiyasa na....."

Dakatar da ita tai ta hanyar d'aga Mata hannu....

"Inkin gayamin bazan fahimta bane, menayi Miki da zafi da Baki dauk'eni da muhimmanci kamar yadda na daukeki ba? Saurare Ni Nan kiji....

Tun farkon ganina dake nake hango wani a cikin rufaffiyar zuciyarki, ko sau d'aya Baki yadda kin gayamin sirrin zuciyarki da soyayyar ki ba, meyasa? Meyasa Baki yadda da k'aunar ki nake kamar Nuriyya ba? Ko dai saina bud'e zuciya ne kingani zaki yadda Dani Salamah?"

Cike da rauni ta k'arasa zancen hawaye na biyo idonta, itama Salamar hawayen take sossai, Hammad da Akbil tsaye suke sororo suna kallon girman wannan k'aunar dake tsakanin yan uwan biyu..........




*Sorry for short typing abubuwan ne sai a hankali, keep fallowing pls I love ur comments it makes me feel comfortable👌🏻*

Pls
#Vote#
#Share#
#Comment#





*_Maryam Abdul_*

inda rai ashe da rabo....Where stories live. Discover now