© *_HAKKIN MALLAKAR_* ® *_Maryam Abdul_* _______________________ *_INDA RAI

518 37 4
                                    

© *_HAKKIN MALLAKAR_*

® *_Maryam Abdul_*

_______________________

*_INDA RAI....._*
              *_ASHE DA RABO..._*

Wattpad me on @MaryamAbdul559



{ 23 }



Yalwataccen murmushi ta saki Wanda yayi nasarar bayyanar da farare tas d'in hak'oranta masu d'auke da kyakyyawar wushirya wacce ta karawa murmushin kyau, tare da hugging d'in Fee..

"Am really api twiny who's lucky guy touch the blessing heart of my sis" cikin sanyinta tace maganar wacce ke fita da zallar farincikin da har ranta takejin sa, Allah ya sani tanason ahalin gaba d'aya da zuciya d'aya, to indan ma Bata so su ba ai ta cika babbar butulu wacce batasan alkhairi ba kenan, Amma soyayyar Nafisah ta girmi duk yadda zata kwatantata kota furta ta, Feenah tana da free heart a rayuwar ta ba kyashi ko son Kai a wannan familyn ta sani, tsawon shekarun nan da suka aka kwashe ba Rana d'aya data koka Wai akan tayi rashin wani Abu na rayuwa saidai ta koka akan girman halacci irin na wad'annan bayin Allah....

"Twiny am scared bansani ba ko zai Soni, ban sani ba ko Yana da wacce yakeso, bansan ya zanyi ba Lee" Fee ke fad'a tana fuskantar Salamah, fuskarta kalar tausayi....

Da gaske Feenah na k'aunar wannan Muhammad Dan tana karanto raunin da zuciyarta tayi a cikin kwayar idaniyarta "don't be silly my gal! Ba kind of namijin da ya isa yace bayason my gorgeous and beautiful twiny nah, karfa ki manta Fee ce fa mai haukatar da mazajen campus" dariya suka  gabad'aya tare da kai Mata dukan wasa a cinya....

"U can't understand Lee, shid'in ma nasan Yana gigita chicks din naija and inane ma yayi karatu..?" Dallah can talkative ya akayi kika manta Ni kuma na tuna nida bamma San wannan crush d'in daya zubar min da farashin ki ruwa ruwa a kasa har haka"

"Hhhhhh wlh ke d'innan green snake ce I swear mom da Dad sunki yadda ne kawai Amma kin iya zare zance hankali kwance"

"Leave me surattacciya nayi karatu na, kiji da tunanin crush dinki Nan d'aya hargitsamin ke, mutum na tare dake ma ai Dole ne ya iya surutu" 

Mik'e wa Fee tayi akan baby bed d'in ta, ganin Lee d'in ta koma nata bed, tasan karatu takeso tayi, hannayenta tayi filo dasu tare da yin rigingine tana zuba murmushi, kafin tace.....

"A few day suka rage muje naija zaku had'u, zaki Kuma tabbatar ya cancanta"

"Uhum! Zanzo nagansa Koh, Dan wannan yabon yayi yawa, Koda yake it's love, zai yuyu ma na gansa ni baimin ba" yar dariyar shakiyanci Fee tayi "wlh never twiny duk zafin kannan naki da kikewa maza kikaga Yayana I know u most salute" murmushi Mai sauti ta saki "any way, can't wait to see him, am my sweet country too, I miss naija over 2years fa!"

"Yeah! Buh bafa wani sabon Abu still dai it's naija as u know"

"Hhhmm! My blessing country can't change ( ya Allah ka kawo Mana d'auki da canji Mai albarka a k'asar nan tamu ta Nigeria)...


***********

"Ummi when we going to see her" kyakyyawar farar yarinyar ta fad'a wacce a k'alla zatayi shekaru 12 to 13, itama cike da Taya uwar tasu jimami take maganar duk da cewa har yau d'innan a iya foto kawai suka san wacce ke jikin foto sai labarin ta da suka samu gurin iyayensu, Amma suna jin k'aunarta da Kuma son sanin Ina take da Kuma yaushe zasu had'u...

"I don't know when we meet dear" mamar ta fad'a wacce a kallon fuskarta kawai zaka Karanta matuk'ar damuwarta "very soon sweetheart" suka ji an fad'a a bayan su "ur welcome ABI" yarinyar ta fad'a cikin murnar ganin sa tare da zuwa tayi hugging d'insa, shafa sumar kanta yayi " thanks dear Afiya, Abdul ya dawo? Ina Afrah da Suhail?" Ya bukaci sani....

"Ya Abdul bai dawo ba, Su Afrah ciki Abi Bari na kirasu" wannan kamar wajibi ne a garesa idan ya dawo Dole sai yaga iyalansa gaba d'aya first muddin suna gida kafin wani Abu daban....

"Barka da zuwa Yayanah" murmushi ya saki tare da picking d'inta fore head Yana Mai sakar Mata briefcase d'in, foton hannunta ya Karb'a Wanda ya kasance Zane ne ma na k'aramar yarinya wacce bata zata haura 4years ba tana ta zuba murmushi abinta....

"Inshallah ya kusa k'anwata, inaji a jikina mun kusa had'uwa da DotA nah" murmushi ta sakar masa Wanda ta tabbatar zai samar masa da nutsuwa "Allah ya yarda yayanah, thanks for everything"

Yatsarsa ya saka a bakinsa alamar tayi shiru "u know u deserve more than everything so u don't need to thank okey"

"Yes sir!" Tace tare da Sara masa, 'yar dariya yayi tare da jan karan hancinta "kekoh...." Yaran ne suka katsesu da suka shigo suna Mai sannu da zuwa.....

Cira su sama yayi tare da ansawa Yana musu peck a kumatu, wucewa ciki tayi ta barshi anan da yaran yana biye musu, ita ta sani Allah ya lullub'eta da rahamar sa ta ko'ina Bata da matsala a rayuwa saidai wacce ba'a rasa ba ta yau da kullum, ba zata Kira wannan matsala ba saidai tace itace jarabawarta wato rashin sanin ina 'yarta take tana s Raya ko a mace? Dama ace ta tabbatar Bata raye data dangana tasan mutuwa tayi bata duniya, fatanta da Addu'ar ta a kullum shine idan tana raye Allah ya tsare Mata ita tare da kareta aduk inda take sannan Kuma ya k'addara saduwarsu, idan Kuma Bata duniya Allah ya gafarta Mata ita Kuma ya bata dangana, saidai a ranta tana ji *Inda Rai to tabbas da Rabo*...

********

Fatabarakallahu akhanul khalik'in, shine abinda zan iya fad'a game da wannan bawan Allah, Wanda a zahirance na kasa tantance uniform d'in ne sukayi masa kyau ko shine ya musu kyau, sannu a hankali yake saukowa daga step d'in, sannunsa r'ike da hular uniform d'in na sojan sama wato air Force, fuskarsa a murtuke kamar Wanda baisan ya ake murmushi ko dariya ba, tafe yake cike da takun girma irin na cikakkun maza masu jini a jika, tana zaune akan d'aya daga cikin kujerun falon tana kallon tv maid d'insu na goge goge a cikin falon....

Sossai fuskarta ta kasa b'oye farincikin ta na ganin d'an nata musamman ma tada ganshi cikin shigar uniform sossai ya k'ara yi Mata kyau da kwarjini, sunkuyawa yayi daidai kujerar da take Kai, saida yayi Dan Jim kafin ya iya bud'e baki ya furta "barka da safe Mami" can ciki Wanda ba lallai Wanda ke kusa yaji ba idan ba yasan wanene shi ba ko ya kalli motsawar bakinsa....

"Lafiya qlau Muhammad mun tashi lafia?"

"Alhmdllh" ya fad'a a takaice kafin yadan d'osana akan d'ayar kujerar da ke dubin tata tare da jingina bayansa, shima saida yay jim ya k'ara cewa "Abba ya fita ne?"

"Eh ya fita sassafen Nan shida Sadiq, tafiyar ce na ganka cikin shiri?"

Jinjina Kai yayi kafin ya furta "eh" a labbansa.

"Sai yaushe kuma?"

"Mami bansan exactly time ba saidai kun ganmu"

"To babu damuwa, Allah ya kiyaye ya kuma tsare ya baku nasarar aiki, sannan kuma s r'ike gaskiya da Amana, Allah yayi albarka"

"Ameen Mami, inshallah zamu kiyaye nagode" k'okarin tashi da yayi yasa ta numfasawa tare da cewa...

"Muhammad cika da kimar d'a namiji ko mace shine aure, bakada wani excuse na rashin yinsa, kana kallon ga Sadiq Nan har anyi sadaki, bansan me kake jira ba Kuma, kayi tunani akai, idan Kuma da matsala ne sai kayi bayani"

Murmushin da bai shirya bane ya kwace masa tana nufin kenan idan baida lafia "Mami zanyi inshallah in lokaci yayi, Banda matsalar komai"

"To Kari fa?"

"Nasha cofee zanyi Inna isa" ta sani cin abinci Yana daga cikin abinda ke takura shi Sam bai damu dashi ba, kuma Yana da tsari da ka'idarsa...

"Hakane to Allah ya nuna Mana lokacin, Kuma a saka niyya"

"Ni na tafi Mami, ki gayar min da Abba ki kuma gaya masa..."

"Allah ya kiyaye" bin bayansa tayi da kallon har ya fice sannan ta sauke ajiyar zuciya, muhammad d'inta tun tashin sa wani miskili ya tashi ga tsare gida, saidai na yanzun sunfi k'arfin miskilanci, indai zata masa adalci a matsayin ta na uwa tasan hadda damuwa, damuwar da Bata da hali ko k'arfin yaye masa ita saidai Addu'a kawai.........





*My true follower na sani kuma hakuri Dani da yanayin canji na to pls ku k'ara, yanayin dai ne ya canja, Amma k'aunar ku da Maryam Abdul na Nan daram ba inda taje, mudai kara hakurin Nan nida ku😘🤝🏼*

*#Vote#*
*#Comment#*
*#Share#*



*_Maryam Abdul_*

inda rai ashe da rabo....Where stories live. Discover now