© *_HAKKIN MALLAKAR_*
® *_Maryam Abdul_*
_______________________
*_INDA RAI....._*
*_ASHE DA RABO..._*Wattpad me on @MaryamAbdul559
{ 17 }
A d'aki na wuni na kwana ina kuka, kukan tausayin Kaina, saidai no one care, inajin ta da Dady a falo suna hirar suna nishadinsu da dariyar su alaman basu da wata damuwa.....
Ganin kuka bazai tab'a samar min mafita ba, dole na hak'ura tare da mik'a al'amurana a gun mahaliccina Mai duka, haka naci gaba da rayuwa a gidan mahaifina kamar wacce ke rayuwa a gidan kurkuku ko baiwar da ke rayuwa a hannun iyayen gida azzalumai, duka banfi 12 ba a lokacin Amma abinda nakeyi ba lallai wata Mai 20 ta jure shi ba, abu d'aya zancen aunty tayimin adalci akansa shine barina ina zuwa makaranta, shima kuwa ba tare da ko sisin kobon ta ba, bama zan kawo Dady a wannan gabar ba domin dai Dani dashi duk k'ark'ashin mulkinta muke, ko kallo na idan Bata bashi dama ba bayi yake ba, abinda ma yafi d'auremin Kai baifi duk tsawon rayuwa ta ba, ban tab'ajin wani ko wata yazo gidan mu domin Dady ba, saidai domin aunty kawai, shiyasa na d'auka kila baida kowa ne( an dai rabashi dasu ne Salamah saidai Kuma in da sama ya fad'o ba haifarsa akayi ba)
Nidai bansan meke faruwa ba kawai naga da Rana tsaka anyi parking kayan gidan mu, an kwashemu zuwa wata unguwar wani sabon gidan, Wai mun tashi da wancen, haka aunty tacemin wai batason makirci Dan taga yan unguwar sun fara tsanarta akaina, karsu huremin kunne suce in gudu, haka taje garinsu ta dauko Zaharadden da cewar Wai k'aninta ne, ta kawoshi gidan Wai Dan ya ringa taimaka Mata da wasu abubuwan.....
Uncle Deeni yadda nake kiransa Sam baida halayyar kirki ko d'aya, Dan shaye-shaye ne na mannawa jarida, ga neman mata kamar bunsuru, Sam baida alkibla a rayuwar sa, shiyasa Sam tamu batazo d'aya ba, haka ta haddar tamai mota duk inda takeson zuwa shike kaita, shike zuwa saye-sayen abubuwan bukatun gida, tasa Dady ya buda masa shagon siyar da provision a bakin gidan mu, nanfa harka ta bud'e masa yake iya shegensa son ransa, idan ya cinye kudin kayan ta saka Dady ya k'ara saka masa wasu, a yadda na lura tana matuk'ar k'aunar Uncle Deeni kamar ranta, duk da tasan duk abinda yake aikatawa ko sau d'aya banji ta tab'a yimai fad'an ya dena ba...
Wahala ce jajir ta k'aru gareni komawar mu sabon gidan mu, Dan kuwa zuwa makarantar mu akwai nisa sossai, haka nake takawa da k'afata naje na dawo ba tare da kud'in cin abinci ba bare na hawan abun hawa, tilas na Kama kaina da duk wata k'awa a makarantar Dan gudun wulakanci, karatu kawai ya kaini shi kuma nakeyi, saboda yadda nake k'okari a makarantar yasa daliban da malaman duka ke nuna min so da k'auna, duk yadda nake kaucewa k'awaye dole saida na hak'ura nabar Zakiyya itama ganin batada hayaniya Kuma tasan me tazo yi duk da alamu sun nuna 'yar gata ce, Amma tasan ciwon kanta...
Sossai tamu tazo d'aya da Zakiyya Dan itama Sam Bata da hayaniya Kuma Bata shiga shirgin da bai shafeta, karatu kawai tazo yi shi takeyi kamar yadda Nima nakeyi, Sam Bata bari gata yayi affecting d'inta ba, nakan Kama kaina har a gurinta ban mata shisshigi ko rawar k'afa Wai don tana da wani abu a hannunta, duk yadda take jana a jiki, hakan tasa in naki fita breakfast zatamin take away ta kawomin inna nuna bazan amsa ba tace ban d'auke ta yadda ta d'auke ni ba kenan, haka kawai saita sakamin kud'i a school bag da Dan short note "bawai na Rena Miki bane, take it pls nasan zasu Miki amfani" a takaice dai Zakiyya is my second guardian after Mama Maryam and her family....
Ranar da tamin ziyartar ba zata ne tagan ma idonta want am going through, tayi kuka sossai ranar kamar ranta...
"Salamah dama haka kike rayuwar ki, shiyasa baki yadda da kusanci da kowa ba, har Ni iya zumuncin mu, a makaranta ne, baki d'auke Ni d way I take u ba, so let me tell you d fact, I feel u like my bloody biological sis, if u take me like dis as u said, tell me who u r? In this house are you maid?why are you living here where is ur real family, I feel something is wrong!( Ina jinki a raina kamar 'yar uwar da muka fito ciki d'aya, in har kema haka ne kamar yadda kike cewa gayamin matsayinki a gidannan ke er aikin su ce? Meyasa kike zaune anan, ina ainihin familynki suke?)"
Kuka na fashe dashi Dan kuwa da gaske yanzu Zakiyya ce kawai zan iya Kira da tawa nasan ba abinda zata iya yimin Wanda mahaliccina baimin ba amma at lease zanji sanyi inna gaya Mata, hakan yasa na gaya Mata ainihin abinda na sani game da kaina...
Haka muka kulle cikin d'aki mukayi kukanmu son Rai ba Mai lallashin wani cikin mu, itace ta fara denawa tare da Fara rarrashina "Ni a tunani na yara irinmu bamu Kai musan me rayuwa take ciki ba, bamu Kai mudauki nauyin rikicin duniya ba, wlh Salamah ur suffer more than word can say, bazan iya Hana kaddarar ki tayi aiki a kanki ba, Amma nayi alkawari I will be by ur side at any time inshallah, Allah ne masani shiyasan dalilin sa na turo Ni cikin rayuwar ki a wannan gabar" da gaske Zakiyya k'awa ce wacce ta zama wani garkuwa a gareni sossai duk da Banda damar zuwa gidan su, ban tab'a zuwa ba, Amma ita takanzo time to time, shima da aunty ta saka ido akai sai ta Dena, Dan tamin gargadin lallai na rabu da ita salon ta batani ne ai...
Itace ci na da sauran buk'atu na makaranta Kai har ma wasu na gida, kuma Koda Rana d'aya Bata tab'a nunamin gajiyawar ta ko tamin gori ba har muka kammala secondary School, duk yadda 'yan bani na iya suka so shiga tsakanin mu kuwa bamu bada dama ba, Allah ya kiyaye mu....
Haka muka kammala makaranta cikin sa'a da Rabo muka fito da mafi kyawun results, saidai nikam nasan ba lallai inci gaba da karatu ba duba da Banda Wanda zaiyi seponserin d'ina....
"Forever" haka take kirana "nayi magana da Dady nah, akanki ya amince da buk'ata ta har ma ya samar Mana gurbin karatu a India, thank God kuma medicine suka bamu duka" rungume ta nayi sossai ina kukan farinciki kenan da gaske zanyi karatun da nakeso da gaske burina zai cika na zama medical doctor, forever I don't....
"Shitt forever u mean everything to me, am always by ur side, let prepare okey"
Cikin fargaba da tsoron Mai zai biyo baya na samu Dady da dare bayan ya dawo aiki suna zaune shida aunty suna Hira na gayamai yadda mukayi da Zakiyya...
Kallon aunty yayi Yana jiran wane kalar hukunci zata yanke tunda dama itace Mai ikona dashi gaba d'aya.....
"Ahh! Lallai yarinyar kin gama bushe fitilar ki, wato duk watsewar da kukeyi dake da 'yar iskar yarinyar nan da samarin cikin garinnan bai isheki ba, har sai kun lula kun bar k'asa kenan, da sunan karatu ko karuwanci" jikina har rawa yake wato abun Aunty kullum gaba yake ba baya ba, zan iya cewa iya zamana da Zakiyya bansan tanada saurayi ko tana kula samari ba bale yadda Babanta keda tsaurin nan ko ina zataje da saida driver ta, duk da cewa mahaifiyar ta ta rasu hakan bai Hana ta samu cikakkiyar tarbiya daga mahaifinta ba, Sam bar had'eta da matarshi ba, yabarta gun kakarta ne, sannan ya d'auki Mai kula da ita, Amma Wai yau shine aunty ke fad'ar magana irin wannan akan wannan baiwar Allah data tallafi rayuwata, nidai kawai abinda na fahimta game da Aunty duk abinda ko wani da zai kawowa rayuwa ta haske ko ci gaba sai tasan yadda tayi ta dakushe shi ta Kuma rabani dashi......
Kaina k'asa ina kokawa rayuwata naji tana cewa Dady "my love yanzu kanaji kana gani sai ka Bari wani can da baka sani ba ya d'auki d'iyarka ya kaita wata uwa duniya da sunan karatu, diyarki mace Kai kana nan sake da baki, ita Kuma tana can wata duniyar tana abinda ranta yakeso, kayi tunani akai, Ni abinda kawai naga yafi tunda irin wannan ta fara tasowa muyi Mata aure kawai, tunda dai ta isa auren Dama Deeni ya dad'e Yana sonta a aura mishi ita kawai"
Cikin tsoro da tsananin mamaki na d'ago a matuk'ar razane jin kalamanta na k'arshe, Wai amin aure, auren ma kuma da uncle Deeni, Uncle Deeni fa!....
"Ah to to..To ai shikenan abin ma yazo gidan sauki Deeni dai nawa, kice tuwona maina kawai ai sai a Fara shirye-shiryen biki kawai ayi ma a huta ba wani jinkiri da za'a tsaya" na tsinci muryar mahaifi ubana, Yana fad'in zai aura min yaron da yasan baida hali na kirki ko kwaya d'aya...
Cikin tsoro da firgici nace uncle Deeni fa kake magana Dady shi zaka aura min Dady? Kafasan waye Uncle Deeni, na rok'eka Dady karka auramin Uncle Deeni na yadda kamin aure Amma Dan Allah ba Uncle Deeni ba Dady......
Gau naji saukar Mari Mai zafi a gefen kunci na kafin na k'arasa abinda nakesan cewa.......
_wayyo silly Salamah kiyi hakuri akwai Allah😭😭😢_
*_Maryam Abdul_*
YOU ARE READING
inda rai ashe da rabo....
Ficção GeralIt's all about magic, sacrifice, pity, and true love