© *_HAKKIN MALLAKAR_*
® *_Maryam Abdul_*
_______________________
*_INDA RAI....._*
*_ASHE DA RABO..._*Wattpad me on @MaryamAbdul559
{ 14 }
*After some years....*
Hadarine dund'um yayi k'irin a sararin samaniya yayi Mata kawanya, mutanen cikin garin kowa ka gani tafe yake a gaggauce burinsa bai wuce ya samu inda zai lab'e ba kafin saukar Ruwan Dan da alama hadarin zaiyi ruwa bana wasa ba duk da cewa yanzu ne damunar ta fara....
Matashiya ce wacce a k'alla zatayi 16 zuwa 17, Mai matsakaicin tsayi ce a fata Kuma za'a kirata fara Kai tsaye saidai ba k'al d'innan ba, jikinta ba wata k'iba Dan za'a kirata siririya Kai tsaye saidai tana da diri irin na mata mashaa Allah, a fuska Kuma zamu kirata Mai kyau daidai misali, tana da cikakkiyar gira bak'a sid'ik, tare da gashin ido gazar gazar shima bak'i sossai wad'anda suka k'ara k'awata kyan fuskarta...
Saidai abin mamaki Sam Bata cikin nutsuwarta yanayin yadda take jefa k'afarta duk inda ta samu kad'ai ya isa shedar bata tare da hankalin ta, ko ina yaje? Sai Allah..
Motsi-motsi takansa gefen hijab d'inta ta goge kwallar da ke zuba daga idaniyarta, kasantuwar garin na hadari ba Wanda hankalin sa yakai gunta bare yayi tunanin tambayarta ba'asin kasantuwar ta a hakan....
*********
"Abba kace Ya Saif yayi driving d'innan a hankali mana, dibi fa ga ruwa an Fara sai sharara gudu yake" ta gefen ido ya watsa mata harara, k'ara turo bakin gaba tayi, dariya ma suka bawa iyayen nasu,
"Kema feenah da rigima idan baiyi gudu ba taya zamu samu, mu isa da sauri, tunda kunyi mana tsiyar samun flight, but duk da haka Saif ka rage speed musamman kaga zamu shiga cikin gari"
"To ai ma gudun ne ba wani amfani sannu ai Bata Hana zuwa" murmushi ta saki ganin yau mommy tayi support motion d'inta..
"U see! Mommy ma..."
"Dallah malama rabamu da talar bakin nan haka" saurin katseta yayi dan k'aramin aikinta ne tai ta ma mutane zuba tunda taga anyi supporting d'inta...
"To surutai ai ba danki nayi maganar ba bare ki cikamu da iyayi" Abba ganin za'a Fara ya sakashi yan jaridarsa ya rufe fuskarsa da ita, itama feenah tura baki tayi alaman jin haushi Tare da lafewa jikin seat dake itace a gaba ita da Saif din..
Mommy da Abba suna back seat...
Sai hirar ta koma tsakanin mom da Saif, a haka har bacci ya sureta....
Duk da cewa ya rage gudun kasancewar sun shigo cikin gari ga ruwa duk da cewa sun rage k'arfi goge glass din gaban motar kawai yakeyi saboda ganin hanya....
Kamar wata kamun hauka haka ta afko musu duk yadda yayi k'okarin kauce mata ina bai yuyu ba saida ya bugeta...
"Innalillahi wa'innah ilairrajiun" mom ta fad'a da k'arfi, tare da saurin balle murfin tayi kanta, a tare suka fito duka ukun Daddy, Saif da Feenah wacce faruwar abin yay sanadin farkawarta....
Asibitin ta suka gani mafi kusa suka kaita aiko cikin gaggawa suka k'arbeta ganin babban mutum cikin manyan Kaya ( dat how our 9ja is🤦🏽♀)....
Bayan shasshekar kukanta ba abinda kakeji a d'akin, cike da mamaki suke binta da kallo, to kodai batada lafiyar kwakwalwa ne kamar yadda suke tsammani?...
Mommy ce tayi k'arfin halin matsawa kusa gareta tare da Kama hannunta "is ok 'yata, take heart, sannu kinji" sassauta kukanta tayi tana kallonta k'asa k'asa....
"Ki daure ki gaya muna gidanku koki bamu number babanki ko waninki mu sadaki dasu kinga mu akan hanya muke lokaci na tafiya"
Batajin zata yadda ta koma gidansu a wannan halin dadai tanada address din mahaifiyarta data basu sun taimaka Mata sun sadasu, a take ta samu kanta da fad'ar "Ni bansan kowa ba garin nan bani da kowa, Dan Allah ku taimaka kuje Dani inda zaku"
Kallo kallon suka shiga yiwa juna kafin Abba yayi murmushi irin na manya "to 'yata in baki san kowa ba baki da kowa Kuma meya kawoki nan d'in? Kuma meyasa kika yadda ki bi mu? Halan kin sammu ne?"
Girgiza Kai tayi tana gogo kwallarta da bayan hannunta "wlh zan biku nidai don Allah kuje Dani zan ringa muku shara da wanke wanke, wallahi kuka mayar Dani hannunsu kasheni zasuyi" ganin yadda take a tsorace da maganan kisa data shigo ya darsar da tausayin ta cikin zukatan su, Kiran mommy gefe Abba yayi kuka yi magana kafin yace shikenan ta tashi suje, sudai Saif da feenah nasu ido ne duk da Suma tausayinta ya ratsa su duka iyakarta Feenah in tayi, saidai mutumin yau abin tsoro ne, suna dai fatar kada Allah yasa taimako ya zamo musu wahala...(ameen)
******
"Meyasa Hajia? Meta Miki wai a rayuwa! Tun tana k'aramar ta baki tab'a binta da alkhairi ba, haka nima kika girmar Dani akan muguwar rayuwa da nunamin na musguna Mata, duk bai isheki ba, kika datse Mata burin rayuwar ta, kika had'ata aure da namiji Irina Wanda baisan daidai da rashin daidai ba, duk dai tayi biyayya da tunanin *inda Rai da Rabo* wata Rana ki sota, shine Kuma saida ta fara d'orani hanyar gyara kika rabamu, Kuma kika saka mahaifinta ya koreta meyasa?"
Tsaye ta mik'e tare da binsa da kallon sama da k'asa a wulakance "Kai har ka isa ka tsaya gabana kana gayamin maganar da ranka yakeso? Wanene kai? Nace kaidin waye? Kodai ka manta a k'ark'ashin inuwata kake ci kake Sha ne Deeni? To bari kaji kar kayi tunanin Kai jinina ne muddin kaci gaba da gayamin ba dad'i wallahi sai nayi maganinka! Ka sanni dai kasan iya abinda zan iya toka rufawa kanka asiri inba haka ba hmmm" yatsun ta biyu ta kad'a masa tare da juyawa ta fice tana murmushin nan nata na k'eta....…..
*Tirkashi yanzu aka Fara fa🤔*
_ina barar Addu'a a gareku masoya Dan Allah ku saka Dan Uwana khalifa a Addu'a wadda Allah yayi ma rasuwa, Allah yasa mutuwa ta zamo hutu a garesa ya kyautata tamu bayan tasu🤲🏼😭_
*_Maryam Abdul_*
![](https://img.wattpad.com/cover/198182184-288-k792859.jpg)
YOU ARE READING
inda rai ashe da rabo....
General FictionIt's all about magic, sacrifice, pity, and true love