© *_HAKKIN MALLAKAR_*
® *_Maryam Abdul_*
_______________________
*_INDA RAI....._*
*_ASHE DA RABO..._*Wattpad me on @MaryamAbdul559
{ 31 }
*RAYUWA TANA FARUWA WUCEWA TAKE KAMAR BA'AYI BA....,💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Life is too short for hatred, backbiting, ago, pride, arrogant, and been sad, try 2 be happy as much as possible😊👌🏼*
"Nafisah inaso ki nutsu ki saurareni da kunnenki na basira, inaso ki tsaya s nutse kiyi tunani akan maganar da nakeson na gayamiki" murmushi ta saki, ganin yadda Hajia Inna taci serious kamar ba ita ba, itama gyara zama tayi tare da k'ara kusantar kakar tasu, hannunta tasa tare da Kama Bata ta kalleta cikin yanayin gaskiya da gaskiya...
"Inna nasan me kikeso ki gayamin, nasan kinaso ne ki gayamin nayi hak'uri da Ya Muhammad na barwa Salamah shi, ko ince kinaso ne kice min, nayi shisshigi ne a tsakanin wasu masoya guda biyu, da soyayyar su ta ginu tun kafin Susan meye so da kansa, koba haka bane? inaso na rushe ginin da bansan iya adadin shekarun da aka dasa toshiyarsa ba?"
Kallanta Inna tayi baci sake kafin ta iya cewa "dama kinsan komai kenan?"
"Nice dai har gobe Nafisar ki Inna duk shiga duniyar da nayi bazai canja tarbiya da halina ba da kika sanni akai, bansan soyayyar Ya Muhammad da Salamah ba koda wasa Inna, bansan komai akai ba idan ba'a jiyan ba..."karaf ta amshe zancen..
"Lab'e kika koya nafisa?"
"Kai Inna wane irin lab'e Allah ya kiyaye, Allah ne dai ya k'addara zanji ya dawo dani dai-dai lokacin da kuka Fara zancen, Ni kuma nazo d'aukar Abunda na manta, to kinji dalilin jinda nayi"
"Atou madallah" Inna tace kafin ta k'ara rumtse hannun Feenah a nata a tare tausayi da kuma k'aunar jikar tata ke tsirga jinin jikinta, cikin sassauta murya tace....
"Kiyi hakuri Nafisah, ki k'ara akan wanda na Sanki dashi, ki daure ki Kuma yi hak'uri ki fita daga tsakanin masoyannan, bawai ba zai iya hadaku duka bane, saidai Ina tsoron ki cutu 'yata, nafiso kiyi auren Wanda kikeso yake kuma sonki bawai Wanda kikeso ke babu ke a ranshi ba, na sani Muhammad bazai taba bari wani ya cutar dake ba, bare shi da kansa saidai in akazo magana ta aure Ana nufin tsawon rayuwa ne, tabbas hakuri ke rik'e aure Amma fa idan da k'auna, bazai cutar dake ba, Amma Kuma ba zaki samu soyyarsa ba Dan a idonsa Kaunar Salamatu kawai nake gani babu ke Nafisah, ki hak'ura dashi" saurin shanye hawayen da suka taru a idaniyarta tayi, tana Mai bawa kanta kwarin guiwa....
"Inna tun a jiya na Gama sallama ya Muhammad a gun Salamah bana masa kallon soyayya a yanzu face kallon zumunta, Inna ina k'aunar sa fiye da tunanin Mai tunani kamar yadda nake K'aunar Salamah kamar Ya Nuriyya, bazan iya auren Ismail din Ya Nuriyya ba ya haramta gareni, haka shima Ya Muhammad ya zama haramiyata, son da nake masa da Wanda nakewa Salamah ya rinjayi son rayuwa ta, ya shiga tsakanina da burina Inna, bazan....iyaba..bazan..iya ba Inna, Ya Muhammad na Salamah ne" cikin kuka ta k'arasa zancen tare da k'ank'ame innar tana ci gaba kuka... tana kiyastawa a ranta yadda Salamah tayi going through ba tare da wani mataimaki ba, tabbas ba zata kasance Azzaluma ba Dan rabasu kamar zalunci ne....
Bubbuga bayanta Inna taci gaba dayi harta yi Mai isarta,kafin innar ta Fara rarrashi ta ganin ta Fara sauke ajiyar zuciya"kiyi hakuri 'yata, komai zaizo ya wuce kuma inshallah ladar ki na a wajen Allah inshallahu, d'agowa tayi tana Mai goge fuskarta, tana sauke ajiyar zuciya a hankali...
Hannun Inna ta k'ara kamawa "Inna inaso kumin wata alfarma d'aya?"
"Kallonta innar tayi tare da cewa "wace irin alfarma 'yar Nan?"
![](https://img.wattpad.com/cover/198182184-288-k792859.jpg)
YOU ARE READING
inda rai ashe da rabo....
General FictionIt's all about magic, sacrifice, pity, and true love