© *_HAKKIN MALLAKAR_*
® *_Maryam Abdul_*
_______________________
*_INDA RAI....._*
*_ASHE DA RABO..._*Wattpad me on @MaryamAbdul559
{ 22 }
"Yayana Ni ban ganku da wasu yara ba, Kuma Hajia ai ta riga ta tafi bayan ta tilastaka ka saketa, basan wata matar da 'ya'yan da kake maganar akai ba, kodai ka samu dimauta ne?" Sani ya fad'a a sanyaye Dan shikam ya sakashi a cikin duhu....
Dafe kansa yayi da duka hannayensa tuni wasu zafafan hawaye suka fara kwaranya daga kwayoyin idanuwansa, kenan da gaske ba mafarki yake ba, da gaske ne ya saki umm Ruman da kansa?ya rabu da 'yan uwansa saboda Sofie, towai ma ya akayi ya yadda ya aureta ma? Ya wulakanta mak'otansa da suke tsakanin nuna damuwarsu akansa da iyalinsa? Da gaske yana kallo masoyiyar 'yarsa ta zama baiwa mara 'yanci a cikin gidan ubanta Kuma Yana kallo harma da gudummuwar nuna rashin damuwarsa akan ta kuma ya katse Mata duka burikanta ya aura Mata Wanda Koda wasa bazai iya a bawa wani Wanda ya sani ba ma bare 'yarsa Salamah, daga karshe ya koreta da kanshi, da kanshi fa yace ta fice daga rayuwar sa.....
"Ya ilahi wannan wace iri k'addara ce Mai tarwatsa rayuwa ta fad'o min, bazan iya d'auka ba, bazan iya ba...!!" Ya fad'a a zahirance tare da fashewa da wani irin matsancin kuka kamar wani k'aramin yaron da yayi rashin uwa da uba a lokaci d'aya...
Sani da ya gama rikicewa saboda ganin yadda babban mutum kamar wannan ke kuka irin haka, da sauri yayo kansa don ya bashi baki...
"Dakata!" Yace a tsawace.
"Zaka iya dawomin da Umm Ruman da yarana ne?"
Girgiza Kai yayi saurin yi alamar aa, ya dad'e zaune gurin shiru sai hawaye kebin kumatunsa wani nabin wani, ba abinda yake ambato sai sunayen Allah domin neman sassauci a rayuwar sa, haka ya k'arasa wunin ranar a d'aki sallah kawai ke d'aga shi, warkewar k'arfi da yaji yayi don kuwa da kansa yakeyin komai, hatta ruwa yinin ranar basu ga bakinsa ba, haka darema ba canji yadda yaga Rana haka yaga Daren....
Safiyya ta cutar dashi mafi munin duk wata cutarwa da za'ayiwa wani Dan Adam, me yayi Mata a rayuwa da zafi haka data zafi ta tarwatsa shi ta tarwatsa masa rayuwa da iyalinsa, meyasa Bata kasheshi ba akan wannan abun datayi masa, gara ace mutuwa yayi iyalansa suka rayu a guri d'aya cikin dad'i da wuya, meyasa ta raba 'ya da uwarta, meyasa? Ina zaikai wannan girman zunubin data doramai, yayi kuka har ya gode Allah har hawayen suka Kai matakin basa fitowa, bayajin sai k'ara moruwa kuma a rayuwa to me ya ragewa rayuwar sa a yanzu, komai ya kare masa bayan numfashi, Wanda yake fatan yayi amfani dashi ya je ga Umm Ruman, duk da yasan baida kalmar da zata wadacesa ya nemi afuwarta Amma Dole zaije, dolensa ya nemo gudan jinin sa duk duniyar da ta shiga da yardar Allah indai tana raye inshaa Allah *inda Rai da Rabo* zasu gana wata Rana.....
Sani dake zaune farfajiyar gidan, bisa benci jin Yana tunanin wannan al'amarin Mai cike da abin mamaki na wannan mutumin shikan duk da baisan ainihin abinda ya damesa ba ya bashi tausayi, jin yayi an dafa shi, da sauri ya d'ago, murmushin yake Harun ya sakar masa tare da zama gefensa...
"Baka cancanci na d'aga maka murya ba sani, u don't enough to me, sorry am out of my control"
Shima martanin murmushin ya mayar masa "karka damu Yayana na fahimceka ba laifinka bane"
"Sani ka shigo rayuwa ta, ka taimaka min duk da kana da tabbacin bani da sisin biyanka, ka cika cikakken Dan Adam musulmin kwarai, nagode maka sossai"
"Rayuwa ce bamusan inda Rana zata fadar Mana ba, bamusan wacce k'addara ce a gabanmu ba, baka da buk'atar godemin kaina nai mawa" jin yayi sossai yaron ya kwanta masa kwarai...
YOU ARE READING
inda rai ashe da rabo....
General FictionIt's all about magic, sacrifice, pity, and true love