© *_HAKKIN MALLAKAR_* ® *_Maryam Abdul_* _______________________ *_INDA RAI

497 39 1
                                    

© *_HAKKIN MALLAKAR_*

® *_Maryam Abdul_*

_______________________

*_INDA RAI....._*
              *_ASHE DA RABO..._*

Wattpad me on @MaryamAbdul559





{ 15 }


Ana kiraye- kirayen sallar isha suka iso kaduna, anan suka tsaya sukayi sallah, tare da cin abinci, dar dar take tayi har tana ganin wautar ta na biyosu da tayi, to idan sudin mugaye ne fa? Kai tsaye wata zuciyar ke gaya Mata biyosun shine daidai Dan batasan ina ta dosa ba, kuma da alama suna da alaman mutanen kirki koda Yake sanin ainihin mutum sai sallah....

"Sis kici abincin Mana" taji muryar 'yar budurwa da suke Kira da feenah tace "feel free dota tunda har kika Amince damu kika biyomu inshallah ba zamu cutar dake ba okey" kanta ta jinjina tare da ci gaba da cin abincin a hankali wanda a zahiri cusa wa kawai tajeyi bayan Dan tanajin dad'in sa ba...

Zuwa 9:30 suka shiga birnin tarayya duk da cewa dare ne bai hanata baje idanuwanta tana kallon irin haduwar garin ba, lallai garin dad'i na nesa, gari tar da fitillu Kai kace safiya ce, ga kyau iya kyau Kuma Wai cikin Nigeria ne lallai, gaba d'aya hankalin ta na gun kallon garin sanda taji horn din da matukin su ke dokawa gaban wani kerarren mention cikin wata tsadaddiyar unguwa ta gane sun iso kenan, ita fa iya wayonta batasan ta tab'a fita cikin sokoto ba, iyarka sokoton dai cikin sokoton ma ba ko'ina ta sani ba, tana nan gida kullum zaune kifin rijiya....

Cikin 'yan dak'ik'u gate man ya wangale musu wakeken gate d'in gidan suka kutsa ciki, da fara'a ma'aikatan gidan suka iso suna musu sannu da zuwa tare da kwasar logging d'insu suka shiga dasu, ganin yadda iyayen gidan nasu ke amsa musu a mutunce ya k'ara Bata nutsuwa alaman sun San darajar d'an Adam kenan...

"Ash! Home sweet home! Wlh am really tired" feenah ta fad'a, harara Saif ya watsa Mata "raguwa kawai "yace tare dayi gaba Dady ma yayi gaba abinsa "Ya Saif niko! Irin wannan tafiyar haka Mai nisa har kake cemin nayi ragwanta Dan na nuna na gaji zamu had'u" tace da d'an k'arfi yadda zai jiyota..

"Kwaji dashi dai!" Cewar mom kafin taja hannun bak'uwar tasu "mu shiga daga ciki baby nasan kin gaji ai"

Tsakani da Allah gidan ba k'arya ya had'u over duk da cewa bawai ta tashi gidan talauci bane amma tasan da different is clear, aiko Baba da Babansa.

"Baby kije da ita d'akin ki kuyi wanka nasan ur all tired inda zaku k'ara cin abinci ne nasan su ladidi sun tanadar"

"Ok mom as u wish" ta Kama hannunta tana Mata smile itama murmushin ta mayar mata tare binta kamar yadda ta buk'ata...

Mashaa Allah kawai take maimaitawa a ranta d'akin ya had'u gaskiya komai arrange and neat, toilet feenah ta nuna mata ba, musu ta shiga sanda ta fito ta samu ta fitar Mata da night gown Mai irin hawa biyun nan da alama ma sabuwa ce sai k'amshi take zubawa Bata tayi "thanks" ta fad'a a hankali bayan ta Karba...

Murmushi tayi Mata tare da buga gefen kafad'arta a hankali, ta wuce toilet, sauke numfashi tayi a hankali "ya ilahi ka zama jagorana a duk inda na samu kaina" ta fad'a a fili...

*********

"Salamah! Kamar yadda kika gayamana sunanki, to munaso muji cikakken tarihinki dan musan taya zamu iya taimaka miki, Amma kafin nan zan Fara gabatar maki da namu tarihin a takaice....

Sunana Alhaji Aliyu Mai Dala, ni Dan asalin jihar kebbi ne( daga can suke fito Wanda shine sanadin haduwar su) Amma ina zaune anan Abuja saboda yanayin aikina da kuma sana'o'ina sannan kuma muna zama a malesia saboda karatun yarana" Mai d'akinsa ya nuna mata...

"Wannan itace Hajia Aisha Kuma ita kad'ai ce matata, sai babban d'ana Saif ga akwai twins k'anninsa Nuriyya da Nuren suna can malesia mun baro su ne acan saboda exam da sukeyi, sai Nafeesa gatanan wato Feenah, wannan shine tarihina a takaice wasu abubuwan da sauran yan uwana da sannu zaki ganesu" gyara zama yayi...

"Banida niyyar cutarwa ko bari wani ya cutar dake saboda d'a da dukiya ba'a yi musu k'eta Dan bakasan wazai amfaneka ba a cikinsu, saidai banason k'arya ki tabbatar duk abinda zaki gayamana game da rayuwar ki gaskiya ce zaki gayamana, bance duka rayuwar ki ba akwai private life, amma ki gayamana iya abinda kikaga ya kamata mu sayi so dat musan wane irin taimako ya kamata muyi Miki"

Cikin sanyi ta fara magana....

*Mafarin labari...*

Kamar yadda na gayamuku sunana Salamah Harun, Koda nasan wacece ni na ganni ne cikin kangin rayuwar matar uba, wacce batasan komai ba a rayuwar ta face zalinci da cutar da na k'asa da ita, ba na k'asa da ita ba kawai hadda mijinta, Dan babana bashi da power ko kad'an baida saying sai abinda tace, shiyasa na tashi ina rayuwa kamar wacce Bata da kowa saboda bansan dad'in uwa ba bamma San wacece uwata ba, uban ma Dana sani ban San dad'in sa ba, Dan ba kusanci ko shakuwa irin ta d'a da mahaifi a tsakanin mu, Abu d'aya ke hadani dashi fad'a zaimin idan tace nayi abu koya dokeni ko Kuma bani umurni shine kawai...

Guri d'aya nakejin sanyi ake sharemin hawayena duk lokacin da zasu zubu, shine gidan mak'otanmu gidan mama, d'aga ita har 'ya'yan ta gaba d'aya da mijinta roron farinciki na suke, wani lokacin sai naji inama Ni 'yar gidan ce, ko ko inama Dady zai yadda ya basu Ni, tunda shi bai damu Dani ba bai k'aunata, duk da cewa ba irin dukan da ban sha ba akan zuwa gidan nan daga gurin Dady da aunty Amma ban fasa zuwa ba, taje gidan ba taci musu mutunci tayi musu son ranta akan su dena kulani abinda kawai nakejin matar gidan na ce Mata shine "ba Dan ke ko Dan Harun muke kula Salamah ba kinga ko ba zamu dena domin ku ba, kuma ki sani komai nisan jifa k'asa zatayo" haka take hayyako Mata da zagi da cin mutunci itakam ko a jikinta ba zata k'ara tanka ta ba tayi ta gaji ita kad'ai ta sani gaba mu wuce bazai hana Dana ga chance din gujewa ba in gudu, to har karatuna suke daukar nauyinsa daga boko har islamiyya, bawai Dan Daddy baida abin d'aukar nauyin karatun nawa bane aa badai a bashi damar dauka bane, har sutura wannan sai shekara shekara ubana kemin dinki Kuma bazai wuce set biyu ba shikenan, saidai mama kemin tare da yaranta....

Akwai shakuwa Mai girma tsakanina da babban yaron gidan wato ya Hammad, sossai yake kula Dani da karatuna fiye ma Dana kannensa, muddin ina gidan to banida sauran matsala, matsala kawai in ina gidanmu ne inda nake rayuwa kamar yar aikin gidan Kuma kaskantacciyar 'yar aiki mara kima da daraja a idon uwayen gidanta, kafin na samu na fita zuwa makaranta zai nayi shara nayi wanke wanke nayi Karin safe, sannan zan samu ta barni naje makaranta tun shekaruna basu kai 10 ba abinda zan iya tunawa kenan, hakan ya saka nake tashi tun kafin ayi subahin na Fara ayyuka na, Dan duk yadda naso rage wasu da dare bazata taba barina nayi ba zata kirkiromin wani aiki daban, kuma duk wannan wainar da ake toyawa daddy bai tab'a ganin laifinta ba ko da Rana d'aya saidai ma Ni nayi laifi idan na kuskure Mata, ko ina ciwo ne kuwa...

Lokacin da nakai shekara goma sha d'aya lokacin ne Mama ta zaunar Dani Dan ta bani cikakken labari game da rayuwata Dan tanada tabbacin a lokacin na fahimci rayuwa daidai gwargwado duk da k'arancin shekaruna........


*Lafiya ce banda isasshiya shiyasa kuka jini shiru*




*_Maryam Abdul_*

inda rai ashe da rabo....Where stories live. Discover now