© *_HAKKIN MALLAKAR_* ® *_Maryam Abdul_* _______________________ *_INDA RAI

514 31 0
                                    

© *_HAKKIN MALLAKAR_*

® *_Maryam Abdul_*

_______________________

*_INDA RAI....._*
              *_ASHE DA RABO..._*

Wattpad me on @MaryamAbdul559



{ 11 }



"Wait! Madam Dan nayi aure ne laifi? Har kike d'aga min murya haka kina min tsawa? Well Mai kyau ne, buh hala na tab'a gaya Miki bazan k'ara aure bane? Kodai kin manta ni namiji ne mijin mace hudu ok" tsabar rashin abin cewa da imani da yayi Mata lallai matsa bala'i ne maza allurar guba ne, namiji buhun k'aya ne, yau itace gaban Harun yake gaya mata ido cikin ido ya tab'a mata alkawarin bazai Mata kishiya bane? Murmushi Mai ciwo tayi tare da girgiza kanta tabar gurin tare da shigewa dak'inta...

Tana jiyo 'yan kawo amaryar kuma k'awayenta suna ta shewa suna yad'a maganganu....

Bayan share hawayen da ke malala akan kuncinta, kamar an bud'e fanfo ba abinda take, had'e Kai da guiwa tayi tana rera kukan kota samu sassauci a ranta, lallai ta yadda da auren nesa baiyi ba, gata a garin da Bata da kowa, Wanda takeji a matsayin gatanta ya juya mata baya, yau da tana da iyaye a kusa Mai zaisa ta tsaya cikin wannan gidan a warhaka ita kad'ai ba Wanda zai rarrasheta ya Bata shawara, Maman sadiq kawai ta fad'o Mata arai, cikin rashin sanin madafa ta Danna Mata Kira, daga yanayin muryarta ta gane akwai matsala...

"Yadai sister yanaji muryarki haka?"

"Maman sadiq akwai damuwa Dan Allah kizo gida yanzu" shine kawai abinda ta iya fad'a ta yanke Kiran tare da k'ara kifa kanta.....


******


A falon kuwa cikin rashin damuwa da yanayin da Umm Ruman ta shiga ya juya ya wuce Yana d'aga kafad'a alaman kin jikinsa...

"Kai ku tashi ku wuce tunda dai kun riga kun kawo ni a bamu guri mu baje kolin amarcin mu koh" ta jefesu da rafar yan dubu-dubu, wata iriyar shewa suka k'ara yi suna ta d'aga Mata babbar yatsa alamar jinjina "ki dad'e kiyi lasting hatsabibiyar yarinya, tauraruwa Mai witsiya asha amarci lafia, gimbiya Sofie ta Harun" wata daga cikinsu ta fad'a bayan sun mike sun dauki mayafan su da jakukunan su, itama hannun ta d'aga musu kawai tana Mai shigewar ta d'akin ta.....

A farfajiyar gidan sukaci karo da Maryam, wacce tazo da sauri cikin tashin hankali, d'aukarta sukayi suka watsar itama da kallon ku kuma fa watsattsu dake daba son renin wayo....

Sallama ta kwada daga falon shiru ba kowa hakan ya saka ta shigo direct kawai, ihu da shewa da sambatu kawai take jiyowa daga b'angaren Harun, har ta juya zata koma jin al'amarin ba nata bane sai taji an dafata, da sauri ta juyo ganin Umm Ruman ya saka mamaki bayyana a fuskarta to me kenan, k'arara alamomin tambaya suka bayyana akan fuskarta...ga kuma umm Ruman d'in tayi wani biji biji da ita idanuwanta jajir ga damshin hawaye duk sun b'ata fuskar

Ba tare da tace komai ba taja hannunta suka shiga dak'inta tare da zama bakin gado, hannayanta duka biyu Maryam ta rike sossai tare da kafeta da ido tana nazarinta kafin tace....

"Jikina na bani akwai matsala a cikin gidannan, na had'u da wasu Mata da zan shigo ba alamar kirki bare nutsuwa a tare dasu, sudin su waye me yake faruwa ne?"

"Yan kan amarya ne, aure Harun yayi yau"

"Aure kamar ya?" Ta fad'a a zabure cike da sabon mamaki.

"Aure dai Wanda ake Kira aure Maman sadiq?"

"Dama kinsan da auren kenan?" Girgiza Kai tayi cike da jin zafi a ranta..

"Ko d'aya nima shigowata gidannan shine sanina, saidai nasan kafin haihuwar abbana ya gayamin zaiyi aure" nan ta shiga Bata labarin abinda ya faru har ya zamo dalilin yi Mata cs...

Jinjina lamarin kawai take a ranta da canjawar Harun din lokaci daya, tome ya shiga kansa, wace irin amarya ce wannan da za'a kawota gidan miji haka da rana tsaka ba danginta ba kowa sai k'awaye? K'awayen ma na rashin arziki..

"Wane irin aure ne wannan? Wace iriyar amarya ce wannan ya auro miki?"

"Wata shed'aniyar  kanta ce maman Sadiq, a restaurant muka tab'a had'uwa da ita tana aiki a gurin" nan ma labarin haduwar su da sofin ta Bata...

"Ya subhanallah, umm Ruman kina cikin jarabawa, jarabawar ma Mai zafi, Addu'a, Addu'a sossai zaki dage dayi ba a karan kanki ba kawai hadda mijin ki da yaranki, nima inshallah zan tayaki, sai abu na biyu, ki daure ki jure ki kawar da kanki daga garesu, ki kula da Salamah sossai Dan wannan tazo da salon b'ata miki tarbiyar yara,  banda ikon da zan Sanya Harun yayi ko ya bari, haka ma Babansu, Amma inshallah zanyi magana dashi akan lamarin ya bashi shawara ya kuma lurar dashi irin musibar da ya Sanya kansa, ki yi hakuri ki k'ara hakuri ki dogara ka ki mayar da al'amuranki gareshi inshallah zai isar Miki" haka taci gaba da yi mata nasiha tare ba Bata shawarwari da lurar da ita.....

Lokacin da abbansu Sadiq ya tari harun da zancen sai cewa yayi meye damuwarsa a ciki, kuma ai rayuwarsa ce ba tashi ba, meye damuwarsa da gidansa dahar sai tsoma masa baki, hadda cewa ko yan uwansa basu isa suyi Mai shisshigi kamar haka ba, sossai yayi mamakin abokin kuma makocin nasa, hakuri kawai ya bashi ganin tabbas shine ya shiga huruminsa.....

Lokaci d'aya gidan Harun ya koma fiye da prison ga rayuwar Umm Ruman Sam aure da zaman gidan duka sun gama fita kanta, sossai take daurewa tare da jurewa akan abubuwan izgilan ci da renin wayo da Sofie ke mata, gaban Salamah takema Harun abubuwan Sam basu dace ace anyi a gaban yara ba, hakan yasa ta maida zamanta mafi yawa Dana 'yarta gidan 'yar uwa kima makociyar ta Maman sadiq, nan nanne kawai take zuwa tana jin sanyi a ranta, sossai take kewa da son danginta a kusa da ita, lallai kowa yabar gida gida ya barsa...

Gashi ta kasa gaya musu komai na damuwarta gudun ta tayar musu da hankali suzo ayi tashin hankali abinda Bata so Sam...

Tadai bar kawai al'amuranta gurin mahaliccinta tana mika masa kukanta.....

Duniya fa tayi wa Sofie dad'i ta mallaki Harun fiye da yadda take so, sai abinda tace, ya koma k'ark'ashin umurninta, sai mulkinta take zubawa son ranta a gidan, ko kallon inda Umm Ruman take bayayi bare yasan da zamanta a gidan, 'yarsa ma ya manta da ita, tun tana zuwa inda yake Yana hantarar ta da korar ta taje gurin uwar tana kuka, ta rarrasheta har ta fara tsoron zuwa ma, bare yadda Sofie ke tsorata ta take tsoronta kamar ranta itama.....




*Allah ka iyama na abinda bamu iyawa kanmu🤲🏼*





*_Maryam Abdul_*

inda rai ashe da rabo....Where stories live. Discover now