© *_HAKKIN MALLAKAR_*
® *_Maryam Abdul_*
_______________________
*_INDA RAI....._*
*_ASHE DA RABO..._*Wattpad me on @MaryamAbdul559
{ 16 }
"Salamah nasan zuwa yanzu kin fahimci rayuwa daidai gwargwado, shiyasa yanzu na zaunar dake don na k'ara haskaka miki hanyarki na sanar dake wacece ke domin kisan yadda zaki tafiyar da rayuwarki a yadda ta sauya miki, Wanda ba makawa rubutacciyar kaddarar ki ce wacce ke baki isa ki guje Mata ba....
Salamah Harun d'iyar fari gurin Harun da umm Ruman, kintaso cikin cikakkiyar gata da soyayyar iyaye, a yanda mahaifiyarki ta bani labari aure Mai cike da soyayya sukayi ita da mahaifinki Wanda soyayyar ce ta zama sanadin nisanta kanta da yan uwa da danginta ta biyo abbanki har garin Sokoto, Salamah ni kaina sheda ce akan soyayyar da ke tsakanin iyayenki, da irin k'auna da kulawa da suke nuna Miki, musamman mahaifinki yana Miki matuk'ar k'auna, nasan zaki Sha mamaki Dana fad'i hakan Dan kin tashi baki ga k'aunar ba,saidai gaskiyar kenan kin taso cikin soyayyar iyaye matuk'a saidai halin rayuwa da yake Mai sassauyawa ce ta sauya ta zamo haka" Kama hannuna biyu tayi bayan tayi shiru na 'yan mintuna..
"Salamah barakar iyayenki ta fara ne tun kafin haihuwar k'aninki Wanda nasan da wuya in zaki iya tunashi, bayan haihuwar sa komai ya ida lalacewa mahaifinki ya sauya tashi d'aya daga loving and caring husband zuwa stranger wa mahaifiyarki, daga karshe dai ya bijiro da maganar auren Safiyya Wanda babu sanin mamanki har sai ranar da ta tare bayan d'aurin auren kenan, mahaifiyarki tayi dauriya da juriya matuk'a duk saboda ke da d'an uwanki da jure zaman auren duk da mayar da ita bola da akayi a gidan haka ta d'aure ta jure, rabuwar auren iyayenki k'addara ce wacce bata da makawa, Kuma nakasu ne ga rayuwar ki, sossai mahaifiyarki taso tafiya dake kamar yadda ta tafi da k'aninki saidai fau fau mahaifi yak'i barinta taje dake, taje da niyyan zata dawo gareki ta tafi dake saidai Sam hakan bata yuyu ba Dan kuwa iyayenta sun hanata saboda jin zafin abinda mahaifinki yayi mata, zuciya ta ciyo su ta hanasu hango me mamanki ke hango Miki, Dan tafi kowa sanin a wane hannu ta barki, bance Safiyya ce sanadin komai daya faru da rayuwar ki ba, saidai na sani kin sani kowa ya sani Bata kyautata sam a gareki, kiyi hakuri ki k'ara 'yata, kici gaba da Addu'a ga mahaifinki kiyi musu biyayya inshallah *inda Rai da Rabo* zaki ga ribar hakurinki, sannan ki sani mahaifiyarki tana matuk'ar k'aunar ki saidai anfi k'arfin ta ne, shiyasa tayi nisa dake, Amma ni na sani duk inda take tana cike da begenki da tunanin rayuwar ki, kada ki manta kinada uwa da d'an uwa masu k'aunarki, kuma inshallah Allah inda Rai da lafiya zaku had'u watarana....."
Tun daga ranar da Mama tayi min wannan bayanin game dani nasa a raina duk rintsi wata Rana zanje ga mahaifiyata da yardar Allah, a lokacin ne Kuma Babansu ya Hammad ya samar ma ya Hammad da kaninsa gurbin karatu a kasashen waje, gaskiya bazan iya tuna sunan kasar ba, sossai ya Hammad yaso tirjewa akan bazai bar Koda garin Sokoto bane da sunan karatu saboda ni Dan gani yake idan ya tafi bai cika alfarmar da Aunty Rumana ta nema daga gareshi ba..."
Zoben hannunta ta kalla tare da murza shi tana tuna kalaman wanda ya mallaka Mata goben, haka kawai taji ba zata iya gaya musu abinda ke tsakanin ta dashi ba "karki manta Salamah, kada ki manta Dani, duk rintsi ki jirani zanzo, inshallah zanzo gareki na aureki, ina k'aunarki Salamah k'auna Mai cakud'e da tausayinki wacce ban gane ba sai yanzu, ki r'ike zoben nan kada ki rabu dashi, ki rik'esa kiji a ranki kamar nine tare dake, ina Miki fatan alkhairi, zan tafi ne kawai a dole bawai Dan inaso ba, saidai inada tabbacin nida ke zamuyi alfahari da karatun nan wata, rana, nasan cewa kinyi k'ank'anta kuma ba lallai ki fahimci me nake nufi ba, Amma dai alal a k'alla inaso ki sani Ni Mai k'aunarki ne " murmushi Mai gauraye da k'auna Wanda yayi Mata ta tuna "kada ki manta ki zama likitar nan fa, zan dawo kimin allurar nan" duk da cewa bazata tuna lokacin ba saida tayi dariya duk da kuka takeyi a lokacin) wannan shine rabuwar ta da ya Hammad dinta Wanda har yau basu k'ara had'uwa ba, Amma tana sa ran inda Rai da Rabo zasu had'u wata Rana....
Jin shirun ta yayi yawa ne, ga hawaye na zubo Mata yasa momy cewa "kiyi hakuri 'yata kamar yadda Mama Maryam ta gaya Miki Nima shine zan fad'a bawa bazai tab'a tsallake tsinin k'addarar sa ba..."
Gefen mayafinta ta saka ta share hawayen kafin taci gaba...
"Bayan tafiyar su ya Hammad ba dad'ewa Kuma sai akayima abbansu transfer zuwa wani gari duk yadda Babansu yaso Dady ya basu Ni su tafi Dani da sunan zai dawo masa Dani inna kammala karatuna, haka Dady ya murje idonsa yace baisan zancen ba, ya kuma k'ara da ci musu mutunci akan cewa suna masa shisshigi ba dangin iya bare na baba daga mak'otaka, duk ya zuba musu ido Amma shine bai ishesu ba zasu ce ya basu 'yarsa kwaya d'aya dayake kalla yaji sanyi, to su fita idonsu kada ya hadasu da hukuma, haka dai ba dad'i muka rabu ina kukan zafi goma goma, shikenan nikam nasan yanzu kuma sai abinda Allah yayi Dani my last hope na rasashi Nima, kafin su wuce saida abbansu yaje har makaranta da muke ya biyamin duka kud'ad'en makarantar har na kammala secondary Dan dama Dady nah ya dad'e da cire hannunsa akan karatuna...
Mama Maryam ta Kirani gefe "Salamah ungu nan" takardu ne masu d'auke da adireshin mahaifiyata da sunan garin su, da takardun fili Mai d'auke da sunana, sai adireshin ta, da Kuma k'aramar waya da wasu kud'ad'e masu d'an jimillah "wannan adireshin mahaifiyarki ne, ki aje a wurinki nasan inshallah zai miki amfani Koda nan gaba, wannan Kuma fili ne naki ne mallakinki ne, da kud'in kayan mahaifiyarki da aka siyar da sunan in tazo tafiya dake ta wuce da kud'ad'en da Allah bai k'addara ba, shine mukayi maganar a sai Miki fili dasu da ita kafin na Dena samun ta a waya, Wanda bansan dalili ba Amma dai nasan koma meye ba son ranta a ciki inshallah, wannan waya ki r'iketa a hannunki zamu ringa magana dake na saka Miki number ta a ciki, zan rinka kiranki inajin lafiyarki, wannan kud'ad'en ki r'ike saboda k'ananun buk'atu in sun taso Miki, kada kiyi nauyin baki 'yata in kina cikin damuwa ki sanar Dani, inaso ki d'aukeni tamkar Umm Ruman, Nima na d'aukeki ne kamar Ummi da Kausar wlh inajin k'aunarki har raina, Dan dai kawai anfi k'arfin mu ne bamu da iko dake da tabbas bazan tab'a barinki hannun Safiyya ba, ki kula da kanki sossai kinji, ki r'ike mutuncinki Dan Allah, duk rintsi, inshallah bayan an kwana biyu zanzo in k'ara gani in zan iya tafiya dake, Allah ya sani har raina banaso zamanki da Safiyya Dan Sam zuciyarta ba alheri a kanki, kedai ki kula ki Kuma lura sannan ki r'ike Addu'a inshallah komai Mai wucewa ne" da haka mik'a rabu da uwar goyona da uban goyona da Kuma k'awaye na muna kokawa Wanda kuma rabuwar kenan har yau bamu sake had'uwa ba.....
Bayan sun wuce na shigo gida idanuna a kumbure kaina na matuk'ar sarawa saboda tsabar kukan da nasha "ke!" Aunty Safiyya ta Kirani da tsawa, Allah ya sani ina matuk'ar tsoronta har raina Wanda ta girmar Dani dashi, tsabar rawar jiki bansan lokacin da na saki ledar da ke hannuna ba, ganin ledar da ta fad'i gabana yasa ta tako ta sameni gun tare daukar ledar, tana duba abinda ke ciki.....
"Eh lallai, wato salon lalataki kenan da Maryam keyi, to mundai gode Allah yau gayyar tsiyar sun d'aga, dole muma mu d'aga kada ma azo Ana bibiyar rayuwar mu Dan nasan halin nacin nasu, yo in Banda na rashin zuciya meye nasu dake tunda dai ba dangin iya bare na bada da tsoho bare tsohuwa" nasan iyayena take nufi, haka dai ta gama ci musu mutunci Dani da uwata gaba d'aya, k'arshe ta karb'e komai ta kona adireshin mamata Dana Mama Maryam a gabana inaji ina gani.......
*Ash!🤦🏽♀Zanci gaba na gaji walle😩😍*
*_Maryam Abdul_*
YOU ARE READING
inda rai ashe da rabo....
Ficção GeralIt's all about magic, sacrifice, pity, and true love