© *_HAKKIN MALLAKAR_* ® *_Maryam Abdul_* _______________________ *_INDA RAI

471 21 0
                                    

© *_HAKKIN MALLAKAR_*

® *_Maryam Abdul_*

_______________________

*_INDA RAI....._*
              *_ASHE DA RABO..._*

Wattpad me on @MaryamAbdul559


{ 46 }






    *_After some years(bayan wasu shekaru)_*





Kunna wutar falon yai bayan yayi amfani da key d'insa ya bud'e falon, dama gate man ya sanar dashi ba kowa, kasancewar ranar aiki kuma Bai sanar da ita zai dawo ba a ranar..

Lumshe ido yai tare da bud'esu a hankali Yana baza hanci Yana shakar dadd'adan k'amshin da ke tashi a falon d'aya Fara chakud'a da sanyin masuburburdar sanyin da ya kunna, komai na nan very neat and clean, Sossai murmushin fuskarsa ya k'ara fad'ad'a "always she's different" ya fad'a a hankali, tare da wucewa upstairs Kai tsaye....

Cikin kaftai jamfa da wando hadda hularsa yadin maroon ne daya fitar da ainihin kalarsa da al'adar ta bahaushe, rufe falon yai, tare da ficewa daga gidan gaba d'aya bayan ya gayawa Mai gadi zaije ya dawo......

************

K'aramar yarinya ce wacce ba zata haura shekaru uku ba, zagaye falon take da motar wasan yara...

"Islaha keda nace ki kwanta daga Shan maganin sai wasa?" Mami tace da yarinyar tana k'arasawa shigowa falon duka, bayanta goye da jaririn da bazai wuce months ba Yana baccinsa....

"Assalamualaikum" sallamarsa ta cika falon, ai ko da gudu warce Mami ta Kira islahar ta fita a motar da tsantsar murnar ta, ta isa garesa tare da rungume k'afarsa "oyoyo papi" tace tana k'ara k'ank'ame k'afar tasa, dagata yai sama Yana sumbatar goshinta, tare da rungume ta a hannunsa "Isi baby, bakije school ba ne?" Ya ce Yana kallan ta tare da shafa sumar kanta...

"Banda lfia ne papi, shine momma tace bazanje ba ta kawo Ni gun Mami nida Anil Kuma tab'a Mami magani da yawa ta bani, Mami ta bani duka maganin bayan ta bani chip and egg naci Kuma...." Sanin surutu irin na islaha yasan idan ya biyeta duk abinda ya faru da baya Nan saita gaya mishi gaba d'ayan sa anan gun...

"Is ok isi hope dai kin samu sauki da Kika Sha maganin ko?" Da Kai ta amsa mishi "bravo my cute gal, get well soon!" Murmushi Tai sauke ta yayi tare da r'ike Mata hannu suka k'arasa shiga cikin falon, Mami tuni tayi gurin Zama tana kallan su tana murmushi, Zama yai a cikin kujera tare da gayar da Mami....

Amsawa Tai tace "Muhammad ka dai riga ka mayar da dirar bazata takenka ko? Yanzu da tasan zakazo ai bama zata fita ba" shafo kansa yai Yana kallon Anil dake bacci a bayanta kafin yace "Mami yanayin aikin ne a haka, damar lokaci guda take zuwa shiyasa"

"Tau Allah ya taimaka yai jagora"

"Ameen Mami, yau kinada bak'in ki har biyu kenan?" Dariya Tai...

"Aishi wannan tasa Mai sauk'i ce indai za'a goyesa to baida matsala, kadai ga wannan zubaidar" ta nuna islaha dake kif kif da ido tana kallanta "Wai Nan ciwo take, amma bakina bai huta ba, gaskiya ka k'arawa malamanta kud'in makaranta dan nasan ba k'aramin ciwon Baki take sakasu ba" dariya yai ita Kuma ta cunno Baki gaba, abinci Mami ta gabatar Masa yaci sannan yace zai je ya dawo, nan kusa Islaha tace sai ta bishi....

"Haba Aunty isi Baki ga, ga Anil Nan baice zaije ba saike da kike auntynsa, yi zamanki yanzu zan dawo ai" bubbuga k'afa ta fara tana kukan shagwab'a, Mami tace...

"Dan Allah d'auki kayarka kui ta tafiya Ni ai na d'an samu na sarara da wannan parrot"

"Parrot?" Tace tana zaro ido "eh parrot kimma fi parrot ai" Mami tace tana zaro Mata nata idon itama, dariyar tare da Jan hannunta Yana gayawa Mami sai ya dawo, ita Kuma tace Mata ba zata k'ara dawowa gidanta ba tunda tace Mata parrot...

inda rai ashe da rabo....Where stories live. Discover now