© *_HAKKIN MALLAKAR_*
® *_Maryam Abdul_*
_______________________
*_INDA RAI....._*
*_ASHE DA RABO..._*Wattpad me on @MaryamAbdul559
{ 9 }
Tamkar wanda aka tsakara da allura haka yay firgigit ya tashi zaune Yana dube-duben d'akin, gefen zuciyarsa ya dafe da hannunsa d'aya tare da mik'a d'ayan bedside ya d'auki tissue yana goge gumin da ya jik'ashi a dalilin gumun mafarkin da yayi, a maimakon yayi Addu'a sai k'okarin sauraren zuciyarsa yake dake azalzalarsa da zafin wutar soyayyar Sofie fiye da wacce yay Mata a baya, ji yake inhar baije ya ganta ba a daidai wannan gabar, ko mutuwa zai iyayi.....
Sauri-sauri kamar Wanda ake jansa yayi wanka tare da shiryawa cikin kayansa na alfarma kamar kullum, sai k'amshi yake zubawa....
"Lafia dai prince irin wannan saurin haka?" Umm Ruman dake zaune a falon tana feeding little Abdul ta tambayesa ganin yadda yake sauri kamar ya tashi sama....
"Am urgent!" Kawai yace tare da ficewa Dan San nutsuwarsa Bata tare dashi...
"Allah ya kiyaye hanya a dawo lafia" ta fad'a Wanda ba lallai yaji ba..
*******
"Kiyi ma Allah sofie ki yarda da aurena, wlh idan kika gujeni my life is useless, kece rayuwata, farinciki na, jin dad'i, I swear ko yau kikeso a daura mana aure to nikam na yadda kuma a shirye nike, pls sweetheart accept me!" Durk'ushe akan gwuiwowinsa yake Yana faman begging d'in ta, bayan ta gama ciyar dashi kayan zafinta na daga abinci da abinsha, abinda ya k'ara rikitar masa da kwakwalwa ya jujutawa shine had'uwar kwayoyin idanuwansu Wanda ta shafawa wani hatsabibin kwalli da bokan nata ya bata Wanda ake Kira idonka idona....
Sarauniyar taku tana hakimce a saman kujera ta d'aura k'afa d'aya kan d'aya tana girgizawa tare da ci gaba da cin chewing gum d'inta daya zame Mata na gado....
"Shit!!!" Tace tare da d'ora yatsanta d'aya akan labb'anta..
"Naji na hakura zan aureka amma da sharad'i.."
"Wlh na amince meye sharad'in?"
"Why ur too eager? Well sharad'in shine auren nan za'a d'aura shine Rana wata yau, kuma cikin gida d'aya zamu zauna nida matarka, sannan zaka kauracewa matarka babu kai babu ita ka yadda?"
"Wannan duka Mai sauki ne muddin kin amince min zaki rufamin asiri ki aureni" wata iriyar muguwar dariyace ke cinta yadda ya dawo wani soko a gabanta kamar bashine wannan matashin Mai ji da girman Kai da takama da isa ba, lallai dole ne ta bud'ewa Gigi gogi bakin jakarta ya dibi iya son ransa Dan aikin sa na matuk'ar yin kyau yadda ya kamata....
K'ara shan mur tayi "kuma baka buk'atar ka sanarwa matarka sai taga amarya kawai fatar ka fahimceni" cikin sauri ya girgiza mata kansa alaman gamsuwa ..
"Yawwa angona kokai fa, yanzu dai zauna dakyau musha firar mu ta soyayya ko ya ka gani" washe baki yayi kamar wani soko tare da komawa kan kujerar ya zauna.....(ya ilahi ka tsaremu ka tsare mana masoyan mu da yan uwanmu da sharrin mutum da aljan ameen)
"Ya Hammad nifa Doctor naceso na zama, kasan meyaca?? Don in taimaka an uwa muculmi sannan na rinda yi Mata allura" ta k'arasa fad'a kanta tsaye tana dariya, Suma sauran yaran da iyayen su mata dariyar suka Kama Mata saboda yadda Hammad d'in ya d'aure fuska tare da tashi ya fice fuu, sun San daba Salamah ce Mai wannan zancen ba, da ko waye yaga ta kansa dashi, saboda yadda yake tsoron allurar sossai ko sunanta bayason ji, k'anninsa saurin toshe bakin sukayi ganin yadda yake binsu da muguwar harara...
"Amma yarinyar nan bakyaji yanzu tsabar rashin M ya Hammad d'in naki kika gayawa haka, ai gashi kinja yayi fushi mudai ba ruwan mu keda shine"
"Hhhhh ai kinyi min dai-dai dota ace mutum gud'ai gud'ai dashi ga son girman tsiya Amma wai tsoron Allura yake, aiko dai Allah ya cika maki niyyarki kizo kita yi masa allurar muga ya zaiyi."
"Amma wlh aunty kin ma yi mana wulakanci, shiko sai ya zauna yay ta tsoron allurar har wannan lab'ub'uwar taje tayi karatun medicine tazo tana masa allura, aiko ta iya allurar yarona yafi k'arfin tayi masa saidai ko Ya Sadiq" dake tana wasa dashi kasancewar sa yaron Maryam na biyu.....
"Aa aunty ai bani take ba, saidai ko k'awarta ta Ummitar da kausaririn Mama"
"Aa nidai ya Sadiq banaso" cewar Kausar dake itama tsoron allurar take, itakam Ummitar dariya kawai tayi Dan duk shiririta tabar abin irin nasu na yara....
"Wai Dady wannan gyare-gyaren gidan duka na menene, yau a gyara can gobe a gyara can sai kace sabuwar amarya za'a kawo"
"Da gaske Dady sabuwar aunty amarya zaka kawo mana?" Sanda kirjin uwar ya buga duk da dai baice komai ba, haka kawai takejin zuciyarta nason karaya da lamarin...
"No angle gidan ne kawai nake k'ara gyara mana ko bakyaso ne?"
"Inaso mana Dady inaso gidanmu yayi cyau nayi cyau yafi na kowa cyau"
"Gud dat my angle, oya jeki gun Mommy kiyiwa Mai sunan baba wasa ni fita zanyi"
"Fita kuma at dis time Dady"
Oh! Princess nikam kin canja wlh kodai kulle zaki koma sani ne, halan kam ba uziri ne a rayuwa?"
"Yi hakuri a dawo lafia"
"Ameen abinda ya kamata kice kenan tun farko kika tsaya jinini" bin bayansa da kallo bayan ya fice tana ta kissama abubuwa da dama data Fara fahimta a tattare dashi a yan kwanakin nan "oh Allah kayi mana maganin abinda duk yafi k'arfin mu ameen.........
*My dear friends, pls kuci gaba da hakuri dani, lafiyar ce Bata gama isata ba, ga kuma abubuwa da suka sakoni a gaba, kunsan ba haka na Saba typing ba wannan dai ne yazo a hakan, to kuyi hakuri muyi ta lallabawa a hakan har in samu kaina, one love all, sannan ku kanku baku bani k'arfin guiwa ba comment ba vote ku gyara pls, sune karsashen duk marubuci🥰👌🏼*
_something big try 2 happen inshallah Allah pls put me on ur prayers pls_
*_Maryam Abdul_*
YOU ARE READING
inda rai ashe da rabo....
General FictionIt's all about magic, sacrifice, pity, and true love