© *_HAKKIN MALLAKAR_* ® *_Maryam Abdul_* _______________________ *_INDA RAI

541 29 0
                                    

© *_HAKKIN MALLAKAR_*

® *_Maryam Abdul_*

_______________________

*_INDA RAI....._*
              *_ASHE DA RABO..._*

Wattpad me on @MaryamAbdul559





{ 13 }



Kukan ma kasa zuwa mata yayi, da ido kawai take binsa da kallo kamar yau ta fara ganinsa a rayuwar ta, yayin da gefe d'aya kukan Salamah ya tsananta, gashi ta rasa Mai rarrashinta, cike da kissar da ta zoma Sofie ta sunkuci yarinyar zuwa seat tare da rungumeta tana rarrashinta ranta k'al, yau burinta ya cika ta rabasu, Harun ya dawo nata ita kad'ai, sai yadda tayi dashi (yo dama can ai sai yadda kikayi dashi ko da take nan, ki daibi a sannu duniya ce)

"Nagode, nagode sossai Harun, tabbas a yau ka tabbatar min Kai Dan halak ne, kuma ina Mai baka tabbacin nima zan tabbatar maka cikakkiyar 'yar halak ce wacce jini biyu ke yawo a jikinta, wato barebari da Shuwa, a yau ba gobe ba bazan kwana cikin garin Sokoto ba Dani da yarana kuma inshallah ba zaka k'ara saka Koda yaran nan a idonka bane, kamar yadda baka buk'atar su, to Suma basa buk'atar ka, Ni nan nayi alkawarin zame musu bango kuma jigo zan zame musu uwa da kuma uba da yardar Allah......"

Sossai jikinsa ya saki tare da yin sanyi yanajin yanayin zuciyarsa ba dad'i duk da baijin yayi abinda bai dace bane har yanzu, Yana tsaye a gurin kamar Wanda aka dasa ta isa gaban Sofie tare da janyo hannun 'yarta wacce take a tsure a jikin Sofin tayi shiru a dole saboda rashin sabo da tsoron sofin dake ranta....

"Ke kuma da kikeji a yau kinyi nasara kin raba wasu masoya da bakisan ta Yaya sukayi suka reni soyayyar su har suka ginata ba, ina tayaki murna Amma fa ki sani" murmushi Mai ciwo tayi....

"Duniyar nan Wanda ya taka ta a sannu ma ya ya k'are bare Wanda yazo mata da tsauri, kuma wlh duk iya hatsabibancinki ina tabbatar Miki duniya ta fiki, duk Wanda kika ga ta d'aga masa k'afa Bata zagesa ba to wallahi taje gurin d'ibar bulalar zanar sa ne, ki rubuta ki aje Koda ranar tazo Miki zaki tuna da na gaya Miki" Jan hannun Salamah tayi kawai ta juya abinta....

Dake shi Wanda yayi nisa bayajin Kira Sam kalaman umm Ruman masu Cike da darasi a kaikaice in kayi duba garesu da idon basira, basuyi tasiri gareta, sai ma jin tayi ya kamata ta k'ara k'untata mata da k'ara Sanya zafi a ranta da rashin nutsuwa....

"Dear bai kamata taje da yarannan ba fa, tunda dai yaranka ne ka amsa ni zan rikesu" ta fad'a cikin Kwanciyar hankali, tana wani shu'umin murmushi ranta k'al.....

Cike da mamaki umm Ruman ta maida kallon ta gareta, tabbas wannan babu d'igon imani a tare da ita....

"Dama ko baki fad'a ba sweetheart ai itama tasan badasu ta shigo garin Sokoto ba anan dai garin Sokoton ta samesu kinga ko ai ya zama wajibi ta bar su, mahaifarsu kuma gidan ubansu Dan basuda inda ya fishi...."

"Wannan ne kuma bazan yadda dashi ba, inbar yarana cikin wannan k'azamar rayuwar wlh bazan yadda ba"

"To shikenan tunda har kin rantse bazan bari rantsuwarki taje a banza ba, kije da Abdulsamad( ya fad'a Kai tsaye) kodon k'ankantar sa karya zamema babynah lalura, Amma kam mamata Salamah dole ne kibar min abata ko kin ki ko kinso" ya fad'a Mata ido cikin ido bayan ya tattako ya d'auki data k'ankame jikin uwar ya fizgeta tana kuka tana komai tana m'ikewa uwar hannu, gwanin tausayi tana kiran ta...

Duk iya bore da tirjiya tayi masa akan 'yarta Amma haka k'ememe ya hanata yarinyar, tanaji tana gani ba yadda ta iya haka ta fito cikin gidan tabar mafi soyuwar 'yarta Wanda take da tabbacin tayi bankwana da saura farinciki ko nutsuwa muddin Salamah zataci gaba da zama wannan azababben gidan, ta tashi cikin kazamiyar tarbiya, ta yadda zataje Amma dole ma ta dawo ta d'auki d'iyarta kota ta Kama ta makasu kotu ne...

inda rai ashe da rabo....Where stories live. Discover now