© *_HAKKIN MALLAKAR_*
® *_Maryam Abdul_*
_______________________
*_INDA RAI....._*
*_ASHE DA RABO..._*Wattpad me on @MaryamAbdul559
{ 44 }
Suna sauka a Abuja ba wani hutu ko hutawa Hajia iya tace "to Aisha sai ku tattara sauran d'iyanku ku mik'a su gidan nasu mazajen sa huta a can" a razane Salamah ta kalleta da luhu luhun idanunta da suka kunbura tsabar kukan da Tasha, tab'e Baki tai tare da hararar ta...
"Salamatu saidai fa kallon kawai Amma yau dole ki kwana gidan Muhammadu, Ina dai muhammadun ne yaudai gaki Nan gashi tace tana dariya, Nuren tashi yai da zummar ficewa waje dama shi kad'ai ne ya shigo ciki Hammad da Sadiq tuni suka d'auki hanya da Ummi, domin tarbar amarya fauziya da za'a kawo yau dake ita abban ta yaje ya dawo da ita tun zuwansu Mami tunda dai da kunya gata ga surukanta ba tare data tare ba.....
"Oh ni rakiya! Wani mawaki ke cewa jiya nigga gaskiya Amma tayau ta fita, nura yanzu Dan kaji Kausara zata tare ne kake wanga talar baki?" Da sauri ya k'arasa ficewa Yana fad'in "wannan tsohuwar mutane takeson taramin barin bar Mata wuri"
Su Mami Kam sai k'unshe dariya suke, kamar wasa Hajia Inna tayi maganar sai kuwa gashi zuwa azahar Dady Harun da Gwaggo sun diro abujar, dasu akayi rakiyar Kausar har gidanta dake Nan Abuja unguwar su d'aya dasu Ya Saif, nasiha da Jan kunne ba Wanda bai Kara nashi akai ba...
Har suka sauka Salamah Bata kokaba k'arfin hali kawai take kallo irin na Hajia Inna, gata ta rik'e ta Gam kamar goro, Haka suka shiga cikin gidan Mami, anan suka huta aka k'arayi Mata kwaskwarima tare da kwalliya nandanan ta fito fes da ita, sossai tayi kyau cikin super England d'inta d'inkin Riga da Zane plain sannan aka nad'eta da lafaya, k'amshi kamar kamar itace tunkun turaren gaba d'aya...
Bayan Isha motocin angaye suka jiwa gidan mami tsinke.
Gurin Daddy Harun Inna Hajia ta Kai ta, tsugunne gabansa sai lokacin taji wasu hawaye sun silalo mata wad'anda ta kasa tantance dalilin fitar su, hannu ya saka tare da dafa kanta cike da madaukakin farincikin da ya dad'e bai tsinci kansa a ciki tun bayan farincikin bayyanar su a rayuwarsa, a da ya mata aure ba tare da Yana cikin hayyacinsa ba, tuna hakan na tanke Masa zuciya, ranar yau Rana ce babba a rayuwarsa, dak'yar ya bud'i Baki yace..."Salamah mamana, my cute little girl.." cike da tunawa da begen lokatan kuruciyarta yaci gaba....
"Banyi Miki komai ba a rayuwar ki da ya kamata uba yawa 'yarsa Salamah ban...." Da sauri ta d'ago dubanta zuwa gareshi tana jin yadda zuciyarta ke dokawa da k'aunar sa, hawaye shima yake tare da shimfid'add'en murmushi akan fuskarsa "aa Dady ba Haka mukayi dakai ba, mu Duka mun yadda komai ya wuce to meyasa? Dady duk duniya Banda kamarka kaida Ummi Dan Allah ka Dena fad'ar hakan"
"Hakane 'yata keda d'an uwanki ku kad'ai ne sanyin idaniyata, Allah yai muku albarka kinji, kije kiyi aure Salamah, kiyi hakuri, kiyi hakuri da aure, ki rungume shi a matsayin ibada kuma bauta, ki tuna Allah a duk motsinki cikin gidan auren ki, ki ringa wa yace ayi aure bawa kike aure ba kinji?" A sanyaye ta girgiza Masa kanta alaman gamsuwa...
"Yawwa Allah yai Miki albarka ya Baku zaman lafiya da zuria managarciya" a ranta ta amsa Addu'ar tasa...
Mik'e wa yayi tare da mik'ar da ita "tashi muje mamana da kaina zan rakaki d'akin ki inshallah" cike da farinciki da k'aunar mahaifin nata suka fito, Hajia Inna sai tsiya take musu Wai babu k'ara a cikin abun haka ko Harun ya murza wa idanuwansa toka ya tasa tilon masoyiyar 'yarsa zuwa gidan sahibin nata, su Gwaggo da yafindo yan kallo suka dawo.......
**************
Masu iya magana kance komai nisan jifa kasa tayyo, yaudai kanwa takar tsami k'warnafi ya kwanta, ga Hammad da Salamah a cikin rufin kwano d'aya a cikin gida d'aya, cikin d'aki d'aya a matsayin mata da miji abunda suka Gama cire Rai da yuyuwarsa wato dai *Ashe inda Rai da Rabo?* Tabbas *inda Rai ba'a cire tsammanin Rabo*
Tunda yai ma Dady Harun rakiya bayan ya kawo Masa amaryar sa har k'uryar d'aki, tare da k'ara yi musu tak'aitacciyar nasiha da jaddada amanar ta a hannunsa...
Yayi kusan five minutes a bakin k'ofar, kamar mafarki yake kallon duka abubuwan jaddada yake Yana maimaita tawa, Salamah fa na cikin d'akin Nan a kuma matsayin matarsa halaliyarsa fa? Lallai girma da buwayar Allah sun yawaita, gani yake kamar inya shiga zaiga batanan ya samu komai a matsayin mafarki, shahada yai tare da daidaita nutsuwarsa, handle d'in ya murd'a a hankali tare da Yi Mata sallama da bud'add'iyar muryarsa irin ta isassun mazan Nan.....
Dukan k'irjinta ne ya tsananta fiye da ko yaushe da suke samun kusancin juna, duk soyayyar ta da amsa sallama yau Kam sai a zuciya ta amsa ta bakin ta kuf kamar an rufeshi da makuli...
Ta kasa tantance yanayin da take ciki a yanzu, dama wannan shi ake Kira first night, duk soyayyar ka da mutum komai saiya kunce ma? Ko aurenta da Uncle Deeni bataji irin haka ba shi da ma za'a Kira ba soyayya a ciki...
Sautin murmushin sa ne ya katse Mata sakar zuci kafin tayi wani tunanin ta sake tsinkayo muryarsa tana fad'in "amincin Allah ya tabbata ga amintacciya wacce gabanta da bayanta yake lullub'e da aminci, Salamaaaaah aminciii ked'in aminci ce kinci sunanki" sanda taji wani irin 'yar har cikin 'yan yatsunta, cikin bazata taji ya yaye mayafin da rufo har kanta dashi, idaniyarta ta sark'e cikin tasa....
Da sauri ta sauke kwayoyin idanuwanta cike da tsananin kunya da k'aunarsa, kyau, kwarjininsa ne suka cika Mata idanu...
Da duk yadda yake takowa zuwa gareta da yadda bugun k'irjinta ke ninkuwa,
Yatsu biyu ya saka tare d'ago da hab'arta Yana kallon cikin idanunanta, idanuwanda tun yarinta har zuwa yau baiga wad'anda suka fisu kyau ba duk kuwa da yaga kwayoyin idaniya sunfi dubu......"Har cikin Raina Salamah, cikin tsokata nake jinki! *Inda Rai Ashe da Rabo?* Salamah? Kece a gabana a matsayin matata, Allah na gode ma, Salamah tashi ki gani" ya fad'a tare da mik'ar da ita tsaye...
Hannunta ya ja haka ta bishi kamar wata sokuwa, toilet ya kaisu, yai Alwala tare da cewa itama tayi, yi tayi kamar yadda ya buk'ata, suka fito ya shimfid'a musu carpet tare da shigewa gaba ya jasu raka'o'in Nan biyu, Addu'ar sossai yayi musu sannan ya dafa kanta yayi Addu'ar Nan da annabin Allah ya umurci ma'aurata suyi domin neman alkhairan da ke tattare dasu wato "allahumma inni as'aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha, wa'auzu bika min sharri ha wa sharri ma janaltahu bihii(ya Allah ina rokon ka duka alhairinta da duk alkhairin da take tafe dashi, Ina kuma neman tsarinka da sharrinta da Kuma sharrin da tazo dashi) allahu a'alam..
Itama umurtarta yayi ta dafa kansa ta Karanta iriyar Addu'ar.....
Bayan cin kazar amarci da ya tilastata ci, suka ci suka sha, kwashe kwanukan yayi ya fitar dasu, zaune take zuru tana jinjina aure da abubuwan da ya k'unsa, Bata Ankara ba sai jinta jikinsa tai gaba d'aya, kukan da batasan dalilin ba ta saki, da mamaki ya d'ago ta Dan tun da ta shigo gidan ba fa um ba um'um....
"Tsoro nakeji ya Hammad, Ina tsoron rayuwa, Ina tsoron kar wani Abu yazo ya sake rabamu Ina k'aunar ka Ya Hammad k'aunar da Ni kaima bansan iyakarta ba....."
Sauke numfashi yayi ya d'auka wani abun daban ne "shitt! Salamah! Ya isa kinji, karki manta bafa mu muka kawo kanmu a wannan lokacin da wannan matsayin ba, Allah ne ya kawo mu shi, bamu muka tsara jiya da yau d'inmu ba, Dan haka bamu isa muyi hasashen gobe ba, bance zan daidaita komai ya Zama normal har k'arshen rayuwar mu saidai tabbas nayi Miki alkawarin tsaya Miki da duka k'arfina inshallah"
Wani sanyi ne ya mamaye ranta, sossai kalamansa suka kwantar Mata da zuciya, hugging d'insa tayi tight cike da farinciki mara adadi.......
Abubuwan da suka biyo baya, sirrinsu ne, muna fatar alkhairi gareku Mr & Mrs Muhammad......
Pls
#vote#
#share#
#comment#*_Maryam Abdul_*
YOU ARE READING
inda rai ashe da rabo....
Tiểu Thuyết ChungIt's all about magic, sacrifice, pity, and true love