© *_HAKKIN MALLAKAR_* ® *_Maryam Abdul_* _______________________ *_INDA RAI

1.1K 73 2
                                    

© *_HAKKIN MALLAKAR_*

® *_Maryam Abdul_*

_______________________

*_INDA RAI....._*
*_ASHE DA RABO......_*



*DAGA MARUBUCIYAR*
____________________

1. *HADUWATA DAKE*
2. *ABDULMAJID*
3. *A DALILIN PRE-WEEDING PICS*
4. *ZURI'A D'AYA*
5. *MEYE LAIFINTA?*


Wattpad me on @MaryamAbdul559




{ 2 }

Tun daga suka shigo unguwar ta hango diyan mak'otansu suna wasa fad'i take "Ni Daddy gurinsu Ummiter danje" rage speed yay tare da kallon mamanta yace "wai meyasa take mayatar son zuwa gidannan?"

"Saboda tana jin d'ad'in wurin ne, kuma ga k'ananun yara tana samun abokan wasa" jinjina kai kawai yayi alaman gamsuwa sannan ya taka burgi, aiko da saurinta ta fita, musamman data hango Ya Hammad suna ball da sauran yaran ga kuma Ummiter zaune akan dandamalin gidansu tare da kausar suna wasan su saita k'osa ta isa itama ayi da ita...

Itama Ummiter tana hangota ta fara washe baki tana dariya tare da nunawa kausar, itama cikin sassarfa ta isa garesu suka sarke hannun juna suna dariya, nan take wasar ta koma ta teddy ta data iso da ita wannan ya runguma wannan ya runguma suna wasan an haifi jaririya (dama wasan yara mata kenan)..

"Umm Ruman!" Dady Harun ya Kira sunan ta, bayan ya rike mata hannenta, cikin yanayinta na rashin walwalar da yake hangowa tattare da ita ta d'ago ta kallesa..

"Meke damunki ne? Tun da muka shiga Hamdala restaurant kika rasa walwalarki meke faruwa? Kinsan dai damuwa ba taki bace a wannan gabar, musamman kodon lafiyarki data baby" ya k'ara fad'a yana tsareta da idanu..

Marmar da idanu tayi wad'anda suke k'yallin hawaye tana k'okarin shanyesu "ina jin tsoro! Ina jin tsoro Harun Ina tsoron kaidin matan yanzu" sai a lokacin ya fahimci ainihin damuwar ta..

"Kina tunanin zan so wancen matar ta eatery ne, ko kin manta na sha gaya miki ked'in kinnan kin isheni? Koko kina shakkar zan juya miki baya ne bayan duka dunbin hallacin da kikamin Umm Ruman??"

Hawayen da take tarewa ne suka tsiyayo a kan kumatun ta, cikin sauri ta rungumesa tare da k'ank'amesa kamar wani zai kwace mata shi..

"Harun bana kokonto a kanka saidai ina tsoron mummunar kaddara da kuma sharrin matan yanzu! Harun muyita Addu'a nida kai mu roki tsari daga sharrin masheranta, Harun Allah abin tsoro haka ma Dan Adam abun tsoro"

"Is ok My princess, inshaa Allah ba abinda zai faru kinji ni naki ne ke kadai kinji" yace yana bubbuga mata bayanta, saida ya tabbatar ta samu nutsuwa sannan ya d'ago ta.

"Oya smile for me!" Bata San time din da murmushin ya sub'uce mata ba, shima murmushin ya mayar mata da martani, tare da m'ikewa "zanje nad'an kwanta kafin time din sallah yayi...

Agogon falon ta kallah ganin it almost time "dear ai lokacin ya kusa da ka bari kayi sallar inaga da sai kayi baccin zai fi"

"Nop kidai tasheni kawai" jinjina kai tayi tabbas wannan itace matsalar Harun wasa da ibada bai kuma damu da Addu'a ba, lallai dole ta sake zage damtse da yi musu Addu'a tare da lurar dashi illar wasa da ibada da kuma rashin Addu'a....

"Salamah to waye baba, baban baby" bud'ar bakinta kenan tace....

"Ya Hammad" cikin rashin damuwa ko a jikinta, zaro ido kausar da Ummiter sukayi "Kai Salamah, kinsan Ya Hammad bulala yake koh, kike cewa shine baba yaji bulala zai mana"

Tashi tayi da d'an gudunta sai cikin filin da suke kwallo shida abokansa tare da teddyn ta jin kawai yay an kama hannunsa..

"Ya Hammad dan Allah ba kaine Baba ba?"

Cikin mamaki yace "baban wah?" Murmushi tayi wadda ya K'ara fitar da cute face d'inta tare da nuna masa teddyn "nice mama Kai kuma babanta"

Allah ya so shi ya matsa da gurin abokansa aida wannan ta karta masa no mercy, Amma ya rasa me yasa yake kasa mata hukunci kamar k'anninsa idan tana sakoshi cikin shirmen su, muguwar harara ya watsawa su Ummiter aiko tuni suka tsorata sukayi cikin gidansu, itako gogar taku koma kula batayi ba bare tasan abinda yayi saima k'okarin samun amsarta take...

"Hakane ko Ya Hammad?" Ta sake fad'a cikin son jin amsar a kuma shagwab'e "eh haka ne jeki!" Yace Dan ta shafamai lafia Dan yafi kowa sanin rashin amsawar kamar ya bata katin gayyatar taci gaba da damunsa ne, shifa yama fahimci ko tsoronsa batayi sam kamar sauran yaran...

Gudun ta sake kwasa jelar gashinta da aka tukke mata a tsakar ka, na reto, tana fad'in "bana gaya muku ba Ya Hammad ne Baba.." ganin wayan a gurin yasa ta fara Kiran sunayensu tare da kutsa Kai cikin gidan....

"Irin wannan Murmushin haka Sofie Mai kike shiryawa ne Dan nasan murmushin ki bai cika zama alkhairi ba yau kuma wa aka cafka?"

"Ido yayi gamo rai kuma ya biya, saidai wannan karon aure ne....."







*Tirkashi!! Tabdijam🙄🤔😯*




*Yawan comments and vote yawan k'okarin typing dina, innaga bakwaso kuma tunkan aje ko'ina na tattara na aje🤷🏽‍♀*






*_Maryam Abdul_*

inda rai ashe da rabo....Where stories live. Discover now