© *_HAKKIN MALLAKAR_* ® *_Maryam Abdul_* _______________________ *_INDA RAI

458 22 7
                                    

© *_HAKKIN MALLAKAR_*

® *_Maryam Abdul_*

_______________________

*_INDA RAI....._*
              *_ASHE DA RABO..._*

Wattpad me on @MaryamAbdul559


{ 33 }



*TUSHEN LABARI.......*




*Iyalan Alhaji Yaro Majidadi* asalin shuwa ne dake zaune a garin barno, kamar yadda ya bud'i ido ya tarar da al'adar familyn su, na auratayya irin ta zumunci shima sai ya kasance cikin masu d'affaka sunnar tasu Wanda ya d'auki abin kamar wajibi ne yayi rik'o da al'adar matuk'a....

Allah yayi wa Alhaji Yaro Majidadi nasibi a cikin kasuwancinsa Yana samu sossai hakan yasa daya tashi yin gininsa sai yayi tafkeken estate guda, shida 'ya'yansa duka maza da Mata, kamar yadda suka Saba had'a auren zumunci shima shi yayi da matarsa Khadija wacce yaranta ke Kira da (Inna) khadija, 'yar kanin mahaifinsa ce aka had'asu, Kuma suna samun sa'ar auren da suke had'awa yaran nayin biyayya ko baka so dole ka zauna ba yaji bare saki, Dole a k'irk'iri k'aunar a cikin gidan auren......

Allah ya azurtasu da yara shida maza uku Mata uku, Abdulsamad shine babba wacce ake Kira da Baba gana, sai Abubakar da Umar a Mata Kuma akwai Zainab wacce suke Kira yagana, sai Fatima(yakura) sai autar su Aisha(Ayssa).

Rayuwa suke ta jindad'i a gidan Dan ba abinda suka nema suka rasa, na buk'atun rayuwa yau da kullum suna cikin wadata sossai, kamar yadda aka saba auren zumunci aka yima Baba gana da matarsa ta farko, Rukayya duk da ba itace zabinsa ba haka yayi biyayya, daga baya ya auro 'yar kawunsa Asiya tunda ba damar ya fita daga cikin gida, haka Suma sauran k'annensa duka irin auren da akayi musu kenan....

Lokacin da akazo auren Aisha(Ayssa) labari yasha banbam domin kuwa Ayssa ta fad'a soyayya da wani saurayi Wanda ke zaune Nan kusa dasu gidan wasu mak'otansu, karatu ne ya kawo shi maid, inda yake zaune gidansu abokinsa , kamar wasa soyayyar tasu ta Fara ta dalilin shigar da takeyi gidan gurin k'awarta, haka suka fara soyayya ba tare da sanin iyayenta ba, ko mutanen gidan da yake inka cire abokin nasa da k'awar tata da suka San da soyayyar tasu, wacce su suka d'auka sunayi ne kawai in ya tafiyarsa ko ta tashi aure shikenan tunda dukansu sunsan al'adar familyn su, a haka suke tafiya...

Saida maganar aurenta ya tashi ta fahimci tabbas soyayyar Ali tayi rinjaye a rayuwar ta, har takejin mutuwa zatayi muddin aka aura Mata wani ba Aliyu, kasancewar shima Wanda za'a had'asu aure akwai wacce yakeso daban a dangin ba ita ba, lokacin da taje Mai da zancen bai wani damu ba saima yaga damace tazo masa ta mallakar wacce yakeso cikin sauk'i, hakan yasa maganar ta fito daga gareshi akan Ayssa tace batason sa....

Duk yadda Ayssa ta d'auki lamarin ya girmi yadda take tunani, wuta sossai takeji cikin gidannan duk wani Wanda ya isa da ita bamai supporting d'inta, Dan wannan sabon al'amari ne tazo musu dashi a dangi, Wanda Alhaji Yaro yafi kowa d'aukar zafi da ita Dan a ganin shi abin tur ne da kunya ace daga cikin gidansa irin wannan ya fito, duk iya wutar gashin da Ayssa Tasha sossai ta tsaya Kai da fata sai zabinta Ali, halin 'ya da uwa, Sossai Inna ke tausaya Mata yadda aka mayar da ita wata saniyar ware a gidan ko yaran gidan an hanasu zuwa Inda take aka kulluta a d'aki kamar wata Mara gata, lokacin da labari ya isa ga kawun su Alhaji Yaro, shine yace tunda har lamarin yakai haka tabbas Alhaji Yaro ya Bata Wanda takeso...

Kiranta yayi akan zai Bata Wanda takeso kamar yadda ta buk'ata saidai ta sani daga Rana Mai kamar ta yau babu shi Babu ita bare ahalinsa, taje can ta samu wasu dangin da iyaye Dan ya cireta a cikin su, kuka Sossai tai ta rera masa akan ta hak'ura da Ali Dan Allah kar ya rabata da danginta da shi kansa, Amma Ina ya Riga ya k'are nashi magana....

inda rai ashe da rabo....Where stories live. Discover now