© *_HAKKIN MALLAKAR_*
® *_Maryam Abdul_*
_______________________
*_INDA RAI....._*
*_ASHE DA RABO..._*Wattpad me on @MaryamAbdul559
{ 39 }
__Feenah na ankare da duk wani movement d'inta, tana jinjina k'aunar da Salamah ke Mata, yanzu da ace Bata sani ba, haka zatai ta juriya duk saboda ita, sometimes dariya take Bata, musamman tashin sallar Daren da take tana jiyota tana rokon Allah ya yaye Mata soyayyar Hammad ya maye Mata gurbin da son Akbil, itakam tasan taso Hammad akansa tasan ma meye so, saidai soyyarsa da take hangowa tattare da Salamar ta girmi tata ko kusa bama za'a gwada ba....
Yau dake da tsokana ta tashi cema tai "beb Amma dai da munyi aure, koma tun yanzu kawai ki Fara cema ya muhammad Dady, Kinga aiya koma abbanki tunda mijin momynki ne ko?"
Duka takai Mata tayi saurin kauce wa tana dariya, yamutsa fuska tai "Allah Fee ki kiyaye Ni, kema ca Miki akai nayi accept naki a matsayin uwa ne bare mijinki ya zama Babana? Wai ma ba Mom take ke Dena ba? Ni ai 'yar Mom ce, Umm Ruman antina ce" tace tana Mata gwalo, gwalalo ido a fili tai...
"Auntyn kike Kira auntynki? Zakiyi bayanine yarinyar barin gaya Mata" daga hannuwa sama tai "ki gayamata Mana kiji ma a bakinta, ke ma in Banda kin reneni ko Ya Nuriyya ban Kira da Mom ba, saike 'yar k'anwata"
"Lallai yarinyar Nan kin girma nice k'anwar Taki to ai ko a haife nice gaba kin sani dai" harara ta zuba Mata zatayi magana wayarta tayi ring, d'agowa wa tai ganin Sadiq ne tayi saurin d'agawa, sun kwana 2 basuyi magana ba tunda ita ba kirkin Kira gareta ba...
"Idonki Kenan Salamah, ba waya ko? Ko chat d'in sai can za'a ganki, to inaga idan balaraben Nan ya d'auke ki shikenan Kuma mantawa zakiyi damu" murmushi ta saki....
"Kai Ya Sadiq ko gaisawa bamu yi ba, sai k'orafi, to yi hak'uri school ne yay zafi kasan ya munzo hardest years, akwai caja Kai, kayi hak'uri kaji zan gyara"
"Kinfa iya wannan, to ya school? yasu Mom? Ina twins din taki da balaraben naki?" Murmushi ta k'ara yi tare da amsawa da suna lfy..
"Gama Fee kusa"
Bata shi tai suka gaisa duk da takan kirashi ita shima Yana kiranta, ta mayar wa Salamah cemai tai "Ya Sadiq Ina pretty Zak's din taka tana lafia ko? Ko pic d'inta baka nuna Mana ba bare kayi joining namu ko bakaso mu santa ne sai anyi auren?"
Dariya yai "rigimarki na Nan Salamah ba inda taje, ganinki silent kawai ake, Ni na isa in b'oye muku Zakiyya ce kece dai Baki nemi ki Santa ba, ai suna magana da Nuriyya ma taje Mata, bayan kun dawo, kece dai da Feenah Baku Santa ba, barin tura Miki fotonta ta WhatsApp sai na turo contact d'inta ko?"
"Eh turamin barin duba, dama Wai Zakiyya ne sunanta kake wani Zak's Kai ya Sadiq ka Bata Mata suna, wlh Kama tunamin da k'awata Zakiyya, gani har sokoto ban nemeta ba, koda yake bansan gidansu bane"
"Hey wait! Zakiyya itama 'yar asalin sokoto ce, if bazan manta ta tab'a bani labarin wata school friend d'inta kuma fa kamar Salamah tace sunanta"
"Can't wait ya Sadiq, pls yi sauri turamin pics d'inta, jikina na bani same Zakiyya ne" tura Mata yay, hannu na vibration ta bud'e pics d'in...
"O.m.g wlh itace" tace cikin kuwwa da tsananin farinciki, Feenah dake toilet da sauri ta fito jiyo ihunta ta zata wani abun ne.....
"Meya faru sis?" Tace a forgice "hold on Ya sadiq" ta fad'a tare da kallon Feenah fuskar taf murna..
YOU ARE READING
inda rai ashe da rabo....
General FictionIt's all about magic, sacrifice, pity, and true love