© *_HAKKIN MALLAKAR_*
® *_Maryam Abdul_*
_______________________
*_INDA RAI....._*
*_ASHE DA RABO..._*Wattpad me on @MaryamAbdul559
{ 47 }
Cak ta tsaya tare da Fara ja baya jikinta a matuk'ar mace, emotions ne mabanbanta brain d'in ta, past memories ne ke dawo Mata kamar yanzu suke faruwa....
Da sauri nurses biyu sukayi kan Sofie da batasan a duniyar da take ba, saurin tare da sukayi tare da mayar da ita Kan gadon, allurar rage rad'adi hade data bacci sukayi mata, tunda dama Dr Salamah tazo dasu da niyyan tayi Mata...
D'ayar nurse d'in, da sauri ta isa gaban Salamah tare da d'an russunawa "madam are you okey?"
Girgiza Mata Kai kawai tayi tare da ficewa daga ward d'in gaba d'aya, ta kallon mamaki hade da tuhuma nurse d'in ta bita, tasan badai ganin halin da matar ke ciki ne ya rikita madam d'in tasu ba, tunda Tasha handling cases da sukafi wannan munin ba tare data rik'e ce ba, su sheda ne akan k'arfin zuciyarta, akwai question mark Akan wannan matar but Bata da Mai warware Mata d'aurin kanta so dole ta jira taga Mai zai faru......
Ba zatace ga yadda akai ta isa ga motar ta, kanta ta kifa akan sitiyarin sai lokacin kuka ya samu damar zuwar Mata, kuka take Mai cike da emotions mabanbanta da iya gaskiyar ta take kukan
Tsawon shekaru bakwai d'innan da auren ta, abubuwa da dama sun faru na farinciki da sab'anin sa, na farko dai ta kammala karatun da successfully bayan dawowarsu gida naija, Allah ya azurta ta da haihuwar 'yarta ta fari, Maryam wacce taci sunan Mami suna kiranta Iman wacce ke shekara ta 6 a yanzu, a shekarar ne Kuma suka rasa Hajia Inna, ta koma ga mahaliccinta, sukayi alhinin rashinta daga baya suka dangana tunda hanya CE ta koma komai tsawon zamani kuwa, sukayi yawon kasashe da yawa a tare na tsawon shekara biyu, k'arfi ta dawo ta zauna domin tabbatar field d'inta, Inda ta Fara aiki asibitin kaduna state, daga baya abokinsa Kuma amininsa Abdulmajid ya roki ta dawo hospital d'insa da aiki saboda ganin kwazo da kuma ba tare da wata damuwa ba ta aminta saboda yadda ake taimaka talaka da Mara gata a asibitin shiya janyo ra'ayin ta, still Bata daina zuwa d'ayar hospital d'in ba dama sauran asibitoci in buk'atar hakan ya taso, hakan yai sanadin dakatar yawon da ita saidai lokaci zuwa lokaci...
A shekara ta biyar da aurensu bayan tayi haihuwa ta biyu ta haifi Aisha Mai sunan mom suna kiranta Ishala suka samun wannan tajigidin daya girgiza hankulansu, na rasuwar Dagash mahaifin Umm Ruman, ba wata uku tsakani sai ga kwatsam rasuwar Harun bayan k'ank'anuwar jinyar da yayi, rashin da ya tayar da hankalinsu Musamman Salamah da Abdul, lokacin da akazo maganar gado sukace sun yafe tunda ba wani abune sossai ba, aka barwa matar da ya aura mace Mai kirki Mai kula dasu da fararan gidan kuwa a barwa Gwaggo da kawu Bala, hakan ne ya tilasta Abdul yin aure tunda dama Yana Shirin yi ne...
Zuwa lokacin anyi auren Afrah, meenal d'in saif nada yara biyu, Haidar Mai sunan Abba, sai Fannah Mai sunan mamanta, Nuriyya ma nada biyu, Asad Wanda yaci sunan baban mijinta, sai esha Mai sunan Mom, Kausar nada d'aya suhail, Zak ma nada Hisham, Feenah mutanen Kuwait kuwa twins tayi alhassan da alhussain, Ummitar kuwa ta k'ara mace ilham bayan Mai sunan abbansu, Allah ya bud'ewa mijinta ya samu aiki navy suka koma ibadan...
A shekara ta bakwai ne ta k'ara haihuwa namiji yaci sunan marigayi Harun suna kiran sa da Anil, matar Abdul namiji ne, shima Harun suna ce mishi Ahkam, Afrah kuwa tayiwa Umm Ruman takwara tunda Anki musu k'ara a cewarta, tanayi da Salamah tana kiranta ihsan, zumuncin su sai abinda yai gaba kowa na zuwa ma kowa, sannan Suna had'a yaransu ta waya Dan a saba da juna.....
Ganin Sofie a wannan lokacin ba k'aramin famin mutuwar Harun yai Mata ba, mutumin da kammala rayuwar sa kuntace da kuncin da Sofie ta sakashi ta rugaza tare da tarwatse Masa duniyarsa ba tare daya moreta ba, haka ya koma ga mahaliccinta da tambarin Sofie a zuciyarsa....
*********
Hammad jin shirun yayi yawa ne, dama daya d'auki Iman gidan Mami yakai su ita da islaha tuni sukaci abinci hadda wasansu kafin ya saukesu madrasa, kukan Anil ne yak'i k'arewa gashi bai Fara cin komai ba, damma yaron baida rigima indai za'a goyesa tofa yunwa ce kawai ke tayar dashi, karb'ar sa yayi tunda anata Kiran wayarta Bata d'agawa, kila aikin ne ba k'arami ba dama silence ko switch up d'in wayarta take indai ba office take ba....
Nurses ne suka tabbatar Masa ta dad'e da fita, har yazo sai shiga motar sa ya hango motarta can gefe, cikin sassarfa ya isa ga motar, tare da kwankwasa Mata, Salamah da d'aga kuka abinka da warce bacci ke nema Nan take ya d'auke ta, Mai cike da mafarkin mahaifinta cikin kyakkyawan yanayi Yana Mata murmushi, knocking d'in da akayi Mata ne ya farkar da ita...
"Subhanallah!" Tace tana dubin Inda take, ba tare da Bata lokaci ba ta sauke glass d'in, Hammad ta gani rungume da Anil daya gaji da kuka yay bacci, kallon tuhuma ya bita dashi tare da zagayowa gefen Mai zaman banza, hannu ta saka ta Karb'i Anil ba musu ya mik'a Mata shi, shayar dashi ta farayi....
"Meya faru?" Ya jeho Mata tambaya Yana kallon idaniyarta...
"Aunty Sofie" ta fad'a a hankali, da bayyanannen mamaki a fuskarsa yace "aunty Sofie Kuma, a Ina kika ganta? Meta Miki?"
"Itace wannan patient d'in ta emergency, she's in critical condition, Bata masan waye akanta ba, idan bakayi Mata farin sani ba, ba zaka tab'a ganeta ba, she's totally change" shiru yai Yana nazarinta kafin yace...
"Kin taimaka Mata?" Da sauri ta d'ago idanunta tayi Masa wani kallo "taimako fa? Tsakanina da ita Sofie, Sofie fa! Kadai manta ne ko?" Gajeren murmushi ya saki "let go home u have to relax" Anil ta Mik'a Masa tare da tada motar suka fice, ba Mai magana a tsakanin su har suka Isa.....
Can zuwa Isha saiga Kiran Dr Abdul yace "Dr nazo na samu patient in such condition ance a hannunki tazo but bakiyi Mata komai ba, duk da she rilly need ur help, why what happening?"
"Sorry sir! But to be sincerely I can't help her" cike da mamakinta yace "why? Do you have financial issue wit her?"
"It personal issue Sir, sorry pls" is okay" kawai ya fad'a tare da datse Kiran....
Hammad dake tsaye bakin k'ofar d'akin Yana sauraren ta, shigowa ciki yai tare da janta suka zauna bakin gado, Kama hannunta yay cikin nashi ya runtse, sannan ya kalli cikin idonta "kinsan meke driving crazy d one who hate or jelous on you?" Girgiza Kai tayi...
"Seen you living happly and successfully, ke ai yanzu kin Riga kin Gama da Sofie, ko taimaka Mata kikai da gida da mota Baki fad'i ba, tunda abinda tace ba Zaki Zama ba gashinan kin Zama, so help her as well as u can, not as she's aunt Sofie just she's human, and u doctors are savious to human u know, help her as she's Muslim, may Allah will reward u"
Rungume shi Tai sossai hawaye na zubu Mata "thank you Ya Hammad, ur always by side in happiness and sorrow, u make my world complete, thanks for ur good advices and corrections always am proudly having u in my life"
Murmushi ya saki tare da mayar Mata martanin hugging d'in "am who i'm just b'cos ur behind me, ur my success in every stage"
Da kansa ya Kira Dr Abdul yai mishi bayanin komai tare da Bashi hakuri, yace aiba komai tunda yaji tace ba zatayi bada yasan tana da hujjarta, Kuma dole xataji abinda taji game da Sofie so ba wata damuwa, Nan ya gayamasa zata shigo gobe suyi Mata abinda ya kamata inshaa Allah sannan sukayi sallama...
*******
Dr Abdul da Salamah da Dr Humaira ne suka had'u akan Sofie kariya a hannu da kafafu takai shida, ga muguwar buguwa datayi aka, gashi tana d'auke da HIV har ya Zama AIDS, ga diabetes ga heart failure, Dr Humaira gwanar kuka tuni ta Fara koka Mata.......
😜😂😂 *So how market sofie people, so sorry fa, abunne yazo a hakan, heart you all my guys🥰😍*
Pls
#vote#
#Share#
#Comment#*_Maryam Abdul_*
![](https://img.wattpad.com/cover/198182184-288-k792859.jpg)
YOU ARE READING
inda rai ashe da rabo....
General FictionIt's all about magic, sacrifice, pity, and true love