© *_HAKKIN MALLAKAR_*
® *_Maryam Abdul_*
_______________________
*_INDA RAI....._*
*_ASHE DA RABO..._*Wattpad me on @MaryamAbdul559
{ 42 }
__da sauri ta had'e gap d'in da ke tsakanin su ta hanye rungume ta k'amk'am a haka sukaci gaba da rera kukan su gwanin tausayi gun Mai sauraro "is okey" Hammad ya fad'a cikin serious tone Dan yaga kukan bana k'are bane gasu da alot things a gabansu, shikam Akbil mamakin soyayyar dake a tsakanin su har yau yake, tabbas wata k'aunar daga Allah ce badai aikin mutum ba....
Hannu tasa ta share hawayen ta tare da d'ago fuskar Feenah itama ta share Mata hawayen hannayenta biyu tasa ta d'ago hab'arta tare da kallon cikin idonta na d'an mintuna, itama cikin nata idon take kallo, sauke numfashi Tai..
"Gaskiya ta nakeso ki Fara hangowa Feenah! Am sorry first! Ban tab'a jin zan Dena k'aunar ki ba tunda na Fara, Bansan dalilin da yasa na b'oye Miki soyayya ta da ya Hammad ba Feenah, nadai San kawai ban fad'awa kowa soyayyar mu ba na barta a matsayin sirri ne kamar yadda ban da tabbacin sake ganin sa bayan k'addara ta rabamu, tabbas na kulle zuciya dashi kad'ai ne, bana tunanin k'ara bud'e ta Kuma, saidai bayan bayyanar sa na fahimci watakil dalilin zaki k'aunace sa yasa ban bayyana Miki soyayya ta dashi ba, pls forgive me?" Ta k'arasa fad'a da yanayin tausayi a fuskarta.......
Murmushi Mai sauti Feenah ta saki tare da dangwale Mata hanci "see her innocent face, Dama kin saba yaudara ta da ita, but karfa kima d'auka na yafe akwai punishment d'inki ai"
"Oh oh Mom pls forgive me" ta sake fad'a tana dak'una fuska kamar wata baby, sossai yanayinta ya tsunduma Hammad cikin nishadi har sanda ya murmusa...
"Kofa ta yafe nikam bazan yafe ba I will going to punish you!" Yace Yana tamke fuskar irin da gaske d'innan, harara ta watsa masa tare da alaman zanzo kanka, shima Akbil matsowa yai yana fad'in...
"Nifa fa i will punish you by showing fake love to me?"
Dan sakin Feenah Tai tare da yi Mata kallon tuhuma "nasan kece Amma as how?"
"Taya ko ba zamu samar da farincinki ba my DotA a duk inda yake?" Ta jiyo muryar Abban su Salamah Yana fad'a, k'ofar ta kalla tare da zazzare ido, ganin yadda suke shigowa, Abba, abbansu Hammad, Dady Harun, Abban su Afrah, hajia Inna, mom, Mami, Ummi, ya Saif, Sadiq, Nuren, Nuriyya, Ummitar, Kausar, Abdul.....
"Me kenan? Wai meke fa..faruwa ne, duk kunsani kenan?" Dariya Hajia Inna tai...
"Yo ke kad'ai CE me wayo kenan, ai kifi na ganinka Mai jar koma, duk wani motsin ki muna sane mun tsaya muga gudun ruwanki ne, waike Mai 'yar uwa ko?"
"Ummi kema?" Dariya kawai Tai, kallon Mami tayi, harara Mamin Tai mata "karma kice min komai, Ashe ma nice kawai ke haukar sonki da damuwa dake tunda Baki dauk'eni a uwa ba"
Maraice fuska tayi tare da kallon Mom "aa kar ma ki Fara lokacin da kike kukan darenki da wuni ciwon Kai cikin gida bakizo guna ai" Dama fuska tai ba sauki kenan ko Ina? Ashe duk suna ankare da ita to ma ya akai ta kasa ganewa ne...
"Kai Ashe haka Dan nawa yake da farinjini, har ake son nasa hadda su kukan dare?" Ta jiyo muryar Harun na fad'a, b'ara Baki Tai tare da sakin kukan tabara, dariya duk suka kwashe da ita, Feenah tace cikin dariyar da take "ai hadda su tsayuwar dare fa tana rokon Allah ya rabata da son Yaya"
"Ke taho abinki jikalle kyalesu, Naga dai ai shima kasa hak'uri yai saida ya yazo Yana min 'yar murya shima ai hadda k'wallarsa" dariya aka k'arayi Dady Aliyu yace "Ashe dai ba d'iyar tawa kad'ai bace hadda d'an nawa to ai anyi 1+1"
Haka akai ta nishadi da annushawa ran kowa k'al Musamman ma'auratan da suke Jin sun cika burinsu.....
Nasiha iyayen suka bisu da ita tare da sanar dasu muhimmancin aure da jajarcewa tare da hak'uri a cikin zaman aure....
Wannan ranar ta so wa Salamah a bazata, ranar da take tunanin duka burinta ya ruguje akan Muhammad, take tunanin ta rasashi Rashi na har abada, sai gata ta rikid'e ta dawo Mata madaukakiyar Rana a Duka ranakun rayuwarta, ta mallaka Mata kyauta mafi tsada data tab'a samu a rayuwar wato Ya Hammad d'inta, itakam me zata cewa Akbil da Feenah, mezatai musu ta sanyasu farinciki kamar yadda suka sakata, tasan badata abinda zata musu daya wuce tayi musu Addu'ar dawwamammen farinciki a zaman aurensu tare da zuria dayyaba, had'e da gamawa duniya lafia, tabbas sunyi Mata cikakkiyar sadaukarwar da batada tabbacin ko Abdul dasu Afrah zasu iya Mata ita.....
**************
Cikin kwanciyar hankali akaci gaba da gudanar da shagalin bikin, Wanda aka tsara dama sai bayan d'aurin aure za'a Fara gabatar dasu, cultural day aka fara had'awa, inda amaren sukasha kwalliya irin ta shuwa aka nannad'esu da lifaya, turaren wuta Kam abun ba'a magana Hall ya amsheshi kamar barin sa akai ya Kama ram, duk Wanda ya shiga tofa dole ya fito da kamshin sa, angayen ma irin tasu shigar sukayi ta bahaushe sak, hadda rawannai Kai kace sarakai ne, mashaa Allah taron ya matuk'ar k'ayatarwa fiye da yadda Baki zai furta, duk yadda Hammad ke kwakwar keb'ewa da Salamah itakam wasar buya take dashi Bata shirya ma magana dashi ba, Dan shi yai ikirarin punishment kuma gashi dai da alama akansa zai k'are, dango mutuniyar taku ta d'auke wuta fa🤭
"Washe gari aka gabatar da kamu Wanda Ummitar da Nuriyya da Minal din Saif suka shirya, sossai Hall din yasha decorations na black nd pink tare da sky blue da akai light up dashi, hakanne yasa amaren sukaci arniyar gowns black tare da head pink, angayen Kuma kaftan d'in dakakkun shaddodi sky colour, shima dai taro yayi mashaa Allah, an gabatar da hide and seek inda aka b'oye angayen akace kowacce amarya ta Nemo nata angon, Ummitar ce Taiwa Salamah nunin inda aka b'oye Hammad sannu a hankali ta shiga takawa harta isa lungun lekawa tai Bata gansa ba, bama alamar mutum, juyowa tai da niyyan zuwa ta saukewa Ummitar masifar wasan da tai Mata.....
Rungume ta taji anyi tight ta Baya ga k'amshin turarensa daya tabbatar Masa shid'in ne, sassanyan numfashi ta sauke, tare da lumshe idanu, tana jin yadda gudun zuciyarta ya karu tana harba mata cikin sauri, Allah ne shaidar ta shikadai yasan irin k'aunar da take wa bawan Nan nasa....
Turning d'in ta yai tare da zuba Mata Lulu eyes d'in shin Nan masu k'ara tsumata "why hidden baby....." Ya fad'a can kasan mak'oshi, har cikin zuciyar ta kalamansa suka ratsa, tabbas so daban ne, ba kuma wanda zai fahimci hakan face Mai yinsa.....
*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Love! Love!! Love!!! Allah ya Raya soyayya da masoyan gaskiya, aci gaba da barar da love till eternity💞*
_friend u have to ready for going out side d country fa, it's time fa, zamu yi flighting fa🛬🛫😂😂 umm annur, nasan ana gaba ai, sis shamcy yane? Zaki kuwa? Nafeesa aysher yane? Kishiyas basma, ta Baban Nana, DotA, my Aunt duk nasan ba'a barku ba, ko ba komai an Lula a gajimare a Kuma bawa eyes food😜_
Pls
#Vote#
#Share#
#Comment#*_Maryam abdul_*
![](https://img.wattpad.com/cover/198182184-288-k792859.jpg)
YOU ARE READING
inda rai ashe da rabo....
General FictionIt's all about magic, sacrifice, pity, and true love