© *_HAKKIN MALLAKAR_* ® *_Maryam Abdul_* _______________________ *_INDA RAI

544 34 1
                                    

© *_HAKKIN MALLAKAR_*

® *_Maryam Abdul_*

_______________________

*_INDA RAI....._*
              *_ASHE DA RABO..._*

Wattpad me on @MaryamAbdul559






{ 7 }



Kicibas sukayi da Maman Sadiq data shigo don dubata ganin yadda suka rabu, duk da tasan ba lokacin shigowa bane kawai dai yanda zuciyarta ta kasa na nutsuwa ne ya tilasta ta shigowan...

Ganin yadda yake kid'ema mutum babba haka na rusar kuka, yasa zuciyarta tsinkewa ta tabbatar ta mutu kawai, ganin yadda kafafu da hannaye ke lilo, cikin jarumta ta isa garesa tare da k'okarin kab'arta..

"Aa Maryam ba zaki iya ba, taimaka bud'e mana motar dai na sakata" cikin sauri ta bud'e motar ya shimfid'ar da ita, sannan ya zagaya ya shiga mazaunin driver, ita kuma bayan ta shiga tare da runguma Umm Ruman d'in a jikinta, tana tofa mata Addu'a....

Saida suka d'auki baban su Hammad suka wuce bayan an dauki Salamah an mayar gidansu suka kulle gidan,

Saukin ma kanwar ita Maman su Sadiq tazo musu sai aka barta da yaran....

Tun kan su isa asibitin sun Kira to ansan da zuwan nasu, a gaggauce suka shiga da ita, ganin yanayinta, likitoci ne kusan uku akanta...

Cikin su ukun ba Wanda ke cewa uffan kowa jiran tsammani kawai yakeyi, baban Sadiq da Maman sadiq sune a zaune suna ta Addu'ar samun sauki, yayin da gogan naku ya kasa samun muntar zama bayan Kai ka komo ba abinda yakeyi, don jikinsa ya matuk'ar sanyi, yasan ko mutuwa tayi to shine sila, meyasa yayi irin wannan gangancin kawai yake tambayar kansa...

"Waye mijin nata?" likitan da ya fito daga d'akin da handcer a hannunsa Yana goge gumi ya fad'a...

"Eh..eh nine" k'are masa kallo yayi kafin yace "biyoni" yafi 1mnt da wucewa Harun na tsaye gurin kamar Wanda aka dasa, jin an dafasa ne yay firgigi "take heart baban Salamah, je kaji condition d'inta.."cewar Babansu Hammad daya dafasa, itadai Maman sadiq na gefe tana ta mata Addu'ar d'agawar kafad'u...

Jiki a sanyaye ya tura k'ofar, gurin zama likitan ya nuna masa, zama yayi, saida ya kwashe some minutes Yana rubuce-rubuce kafin ya d'ago ya kallesa tare da cire eye glasses nasa....

"Ka kuwa San darajar d'an adam?" Tambayar da ya jefesa da ita kenan, wacce tai sanadin kad'awan 'ya'yan hanjinsa, kenan ta gaya musu abinda yayi mata.....

"Matar ta na cikin matsancin halin da batasan inda kanta yake ba har zuwa yanzu, Wanda numfashi ma saida taimakon oxygen takeyin sa, kuma kaine k'ololuwar Wanda yafi dacewa ya bata dukkan kariya a wannan matakin da take, bansan kaine ba ko ba Kaine ba, sanadin tashin hankalin ta, koma dai waye sakacin nakane, Wanda ya janyo dole yanzu za'ayi mata aiki ko don ceton yaron cikinta Wanda shima rayuwar sa take cikin barazana, so sign here" Dr yace ba tare daya jira amsarsa ba....

Saka hannun yayi  tare da neman alfarmar ko zai iya ganinta....

"Saidai ku hangeta ta taga kawai, cool down my man, Addu'ar ka kawai take nema" cikin sauri yace "Allah yasa ayi cikin nasara, Allah ya sauketa lafia...

"Ameen"

Bayani yadda sukayi da Dr din ya musu, ba tare daya gaya musu ainihin musabbabin dalilin shigarta halin ba, Suma dai basu buk'aci sani ba saboda tsakanin ma'aurata sai Allah...

Tana kwance sharkaf cikin uniform din asibitin tana shak'ar numfashi ta hanyar oxygen gwanin tausayi, lallai Dan Adam ba'a bakin komai yake ba, Kaine mutum yanzu anjima sai ka zama gawa, kana da lafia yanzu kamar kiftawar ido ka ganka a gadon ciwo, Allah yasa mudace....

Baban Sadiq ne kawai Wanda yayi jarumtar rike, hawayensa, shima zuciyarsa cike da tausayin matar yake wadda yake kallo a mazaunin k'anwarsa, haka aka gungurata zuwa d'akin theater, Harun sossai zuciyarsa ta k'ara karyewa ya kud'ere a ransa ko son Sofie zai zama ajalinsa ya barta bazai ma k'ara kusantar inda take ba(to Allah yasa zaka iya)...

Bayan wasu awanni aka fito musu da sabon jinjiri dal, k'ato dashi mashaa Allah, Mai matuk'ar Kama da mahaifinsa Dan har yafi Salamah biyosa, saidai farin fatar uwar da yayo sabanin Salamah da haskenta baikai na uwar ba, duk da itama tayo hasken....

Cikin farinciki da k'auna Harun ya k'arbi yaron ya rungumesa a jikinsa Yana sumbatarsa ta ko'ina tare da yin godia ga mahaliccinsa sarkin kyauta...

Suma su baban Sadiq da matarsa cikin farinciki suka k'arbi yaron suna Sanya masa albarka tare da yaba kyawun halittarsa, dama jarirai are unique🥰

Kafin safe sanarwar haihuwar ta gama karad'e yan uwa da abokan arziki, mutanen wamakko dangin Harun har sun Fara isowa, yayin da mutanen Mai duguri suke kan hanya, su Salamah har an iso anyi kani tana nanik'e dashi bataso kowa ya d'aukesa...

Kakkaninta sai tsokanar ta suke, cikin hikimar ubangiji Umm Ruman ta farko cikin masu nasarar ci gaba da numfashi a doron duniya saidai abinda ba'a rasa ba, bayan ita da Harun sai su Maman sadiq ba Wanda yasan dalilin yi mata CS har yan uwanta da suka k'araso da nashi duk dai an bar abin a ta Sha wahalar haihuwar ne ta kasa shiyasa aka yankata tun da kowacce haihuwa ai da yanayinta,

Shirun ta ya mugun k'ara sanyayawa harun jiki, hakan ne yasa dole ya cire layinsa ya yar ya sayi sabo tare da gayawa mutane wayar ce ta fad'i....

Saida sukayi 2weeks a hospital d'in kafin a sallamesu tare da Bata bed rest, sossai harun yayi hidima kamar bashi ba, abinda ya k'ara kwantarwa da yan uwanta da ita kanta hankali har ma da Maman sadiq kanta a nasu tunanin komai ya wuce....

Ba wani taron suna akayi ba andai yi yanka anci ansha Mai jego da yaranta sun fito fes har ma da yan uwa da abokan arziki yaro yaci sunan baban mamarsa Abdus samad zasu kirasa Abdul.....

**********

"Gigi gogi! Akwai damuwa, ban tab'a samun aikinka daya ke Shirin kwabewa ba sai akan wannan, yau fa tsawon kwanan wata d'aya ya k'aurace min hasalima ko samunsa banayi ta waya banayi, nama fi tunanin canja layin yayi fa me haka ke nufi kenan?"

"Huhu haha hihihihihi!" Ya sheke da waka kafurar dariyar da ta k'ara tunzura ta tsuk'e fuska tayi tamau tana ganin lokaci yayi da zata sauya shek'a inhar shi bazai iya ba, Dan batajin zata iya hakuri da Harun koda hakan na nufin tayi yawo tsirara ne...

"Ke baki da hakuri ne ko kad'an sobina, ko kin manta aikinki bai kammalu ba, karki manta baki binne laya d'aya ba ta gidansa, kuma na gaya Miki Yana matuk'ar k'aunar matarsa kamar rayuwar sa, duba nan!" Allon ta kalla gasu zaune tare da iyalansa cikin farinciki kamar wancen karon daya nuna mata su, saidai yanzu taga hadda karin jariri wato haihuwa ta k'ara kenan.....

"K'arfin sihiri kawai ya isa ya janyo mana da hankalin sa kamar yadda kikeso Amma fa sai kinyi aiki sossai kamar haka."

Allon ya k'ara nuna mata Yana ci gaba da Bata tips dinda zatabi su cimma burinsu, cikin kuwa hadda kasantuwar umm Ruman cikin jinin biki zai taimaka ka musu(wlh Mata mu kula da yanayin jini mukanyi sakaki sossai Wanda tanan shaidanu da aljannu da yan tsibbace tsibbace kecin galaba akan mu, Allah ya taimaka mana ya karemu da sharrin masu sharri)......








*_Maryam Abdul_*

inda rai ashe da rabo....Where stories live. Discover now