© *_HAKKIN MALLAKAR_* ® *_Maryam Abdul_* _______________________ *_INDA RAI

881 53 0
                                    

© *_HAKKIN MALLAKAR_*

® *_Maryam Abdul_*

_______________________

*_INDA RAI....._*
              *_ASHE DA RABO......_*



        *DAGA MARUBUCIYAR*
____________________

1. *HADUWATA DAKE*
2. *ABDULMAJID*
3. *A DALILIN PRE-WEEDING PICS*
4. *ZURI'A D'AYA*
5. *MEYE LAIFINTA?*


Wattpad me on @MaryamAbdul559




{ 3 }


"Aure fa kikace? Are you serious?" Saida ta zageta kafin ta d'ora hannunta a kafad'arta suka fuskanci juna, tana ci gaba da makirin murmushinta "kin tab'a jin maganar aure a bakina tsawon *had'uwata dake* ? ( I swear really love dis novel)

Tasan shu'umancin Sofie yafi haka, maza kuma tamkar takalmi sakawa ta mayar dasu zata taka ne iya son ranta data gama morarka ta yar...

"Wannan mai zafi ne, kuma da alama ba Dan hannu bane so inaga kawai ta aure ne kawai zan cimma me nakeso fatar kin gane" tana gama fad'a ta wuce ba tare da jiran amsar kawai tata ba data bari sake da baki......

"Assalamu alakum.."

"Aah! Maman Salamah har kin biyota kinji shiru shiru ko" murmushi ta saki tare da samun gurin zama itadai haka kawai mutanen na burgeta kowa nasu ne haka Salamah zatazo ta shige cikin yaran suyita wasan su ba tsamgwama ko kyara, duk da basu dad'e da zuwa unguwar a Dan watannin nan da sukayi ta fahimci suna da kirki ga yaranta duka masu tarbiya itakam tana son mu'alama dasu kodon kasantuwar ba yar gari ba....

"Aah Maman Sadiq ba ita na biyo ba, Babanta ne ya fita shine nace bari nad'an shigo muyi fira ni kad'ai a gidan duk ba dad'i.."

Murmushin fuskarta ne ya k'ara fad'ad'a "aah to madallah sannu da zuwa mu shiga daga ciki mana"

"Aah! Sai kace bak'uwa ai daga Nan ma ya isa, bare naji hayaniyar yaran, kin barsu sun shige miki d'aki aiko Zaki Sha b'anna kamma Salamah taji"

Dariya tayi tana wanke hannunta bakin fanfo tare da jan d'ayar kujerar robar ta zauna "Salamah ai yarinyar badai wayo ba da rashin tsoro, duk d'in yaran nan tsoron mai sunan Malam suke sossai dan yawan dukan su da yake ga zafin zuciyar tsiya, amma ita kam ko a jikinta"

Itama dariyar tayi "kinji koh, aiko ta mishi rashin kunya ya doketa wlh"

"Duka haka kawai? ai kuma cikin sa'a sai nake ga kamar tasu tazo d'aya dan inata Allah Allah kar ya doketan Amma kinga har yau hakan bata faru ba, saima kamar shakuwa da naga sun fara yi" haka sukaci gaba da tattaunawa game da yaran sai gashi duka kason hirar sun cinye shi akan yaran ba tare da sun san lokaci ya ja ba saida dawowar Babansu ya ank'arar dasu ta mata sallama ta wuce...

Sannu sannu tsakuwa da sabo ya fara shiga tsakanin gidajen biyu Wanda har ya janyo zumuncin ya had'u na iyayen maza, yaran kan ba dama yaro da saurin sabo tuni sun dinke guri d'aya kamar yan gida d'aya....

Iyayen ma mata sun koma kamar yaya da k'anwa idan wannan bata zo wannan zataje, suka koma abokan shawaran juna, musamman da suka fahimci halayyar juna tasu tazo d'aya...

"K'awata yau fa sati biyu ina ta tsumayen gayen nan shiru ne fa, inaga fa zuwa Kogi ya kamani karfa na tsaya eh..." Ta kashe mata ido d'aya...

"Naji a shalansha fa" dariyar k'awar tata tayi "wlh k'awata baki da dama sam baki barin maza su huta, kina lokaci fa tawan to wai kodai binki zanyi nima na samu na faso gari"

"Ato kidai tsaya kallon ruwa mana har kwado ya Miki kafa, waike jikar liman" tace tana sakin wata shak'iyiyar dariya, itama dariyar tayi suka tafa "wane liman kuma wanda ya dad'e da tamkad'e bukuti" itama cikin shak'iyancin ta bata amsa, suka k'ara bushewa da dariyar alaman duniya da shed'an sunayi dasu( Allah kayi mana tsari da sharrin shed'an da sharrin zuciya ka tsare mana imanin mu da mutuncin mu)...

"Princess gaskiya mutanen nan sunada kirki ada har ina d'ari-d'ari da zuwan Angel ashe basu da matsala baki yadda mukeyi da Alh, Aliyu ba ke kyace yayana ne, kuma wani abin burgewa in yaga kayi ba dai dai ba, zai fito ne ya gayama Kai tsaye kinga ko ai wannan shine gaskiyar zama"

"To kaima kenan Dady, nikam ai sai nace Yaya na samu wacce muke ciki d'aya yadda Maman Sadiq kemin wlh kosu Yaya Falmata sai haka, kaga nayi nisa dasu cikin ikon Allah kuma na samu masu mayen gurbinsu"

"Hakane gaskiya to bale angle ai itakam ta koma 'yar gidan shiyasa nake tunanin sakata makarantar da ya saka yaransa shikenan kinga suci gaba da zuwa tare."

"Gaskiya hakan yayi Dady, Allah dai ya mana jagora...."

"Ameen princess umm Ruman uwar gidan Harun kuma amaryarsa ta har abada"

Cikin murmushi jindad'i tace "Allah ya yarda my dear Harun"

Tafiyace Mai tsawo tsakanin Sokoto zuwa Kogi state, Amma k'awayen biyu masu mummunar niyyah a zuciyar su, haka suka yanki hanyar da b'akar niyyar tasu a zuciya, dare ne kawai yay muku cikas din isa inda suka nufa, suka yada zango ainihin gidan iyayen ita sofie..

Washe gari da sassafe wani ma ko tashi baiyi ba, suka lula ainihin k'auyen da magician d'in nata yake, ba k'ananun tsaunika suka haye ba Wanda idan ba Wanda ya sani ba, bakace akwai halittar da ke rayuwa a gurin ba, Amma da yake ita d'in hatsabibiyar kanta ce, ba alamar tsoro ko d'ar tattare da ita saidai k'awarta dake Fara shiga tuni tsoro ya rufeta take ganin kila ta kawo kanta makasa ne......



*Ya Allah dan girman ikonka da buwayarka ka tsare mu da tsarewarka ka kare mu da sharrin mutum da aljan🤲🏼🤲🏼*







*_Maryam Abdul_*

inda rai ashe da rabo....Where stories live. Discover now